← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 168

Sashe 137

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

iya da numfashina Bilkisu”.
      Kamar wata sakarai haka na bisa da kallo harya fice a ɗakin. Gaba ɗaya ya birkicemin tunanina, kalamansa suna dai-dai da tambayoyin jarabawa masu wahalar gaske da ruɗani ga ɗaliban dake zana jarabawar ƙarshe ta barin makaranta. ‘Mike nan?’ na faɗa a fili batare da tunanin mai bani amsarba........
      Sanin hakan da nai ya sakani bin ɗakin da kallo tamkar baƙona, sai kuma na juya jiki a sanyaye na fice daga cikinsa. Idanuna akan boss da ke zaune bisa kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya suka fara sauka, sai Dad da Mom dake zaune suma kusa da juna, Yah Salman na daga can Dining zaune da waya a hannu, sai Aunty Aamilah dake jikin ƙarfen bene ita kuma a tsaye. Takawa nai a hankali gaban Dad na durƙusa, hawayene ke zarya a kumatuna masu zafi da saka ƙunar zuciya, “Dad ina kwana” ta faɗa muryarta a ɗarare. Murmushi yayi yana gyara zamansa, “Ɗiyata yau da kanki a gidan nan? Ko dai ɓatan kai kikayi?”. Hawayen da suka cikamin ido suka gangaro akan kumatunna, na ɗago kaina ina kallon Mom da girgiza ma Dad kaina. “Kayi haƙuri Dad, nasan ni ɗin mai tarin laifukace a gareku waɗanda a kullum nike cike da damuwa da kunya a kansu, Dad wlhy banci amanarku ba, har yanzu bansan dalilin da yasa kuka auramin shi ba a maimakon Yah Qaseem, Dad  inajinka a rainane tamkar mahaifina, banason nazama silar ɓacin ranka kona minti guda kai da Mom, banason ka ringa kallona matsayin tauraruwa mai wutsiya, dan ALLAH kace ka yafemin, ka samin albarka kuma, ka roƙamin gafara wajen Momy da ƴan uwana suma, ALLAH ne ya ƙaddara komai a nasarata, sai dai ya sanyaka ka zama sila, ka nunamin hanya a lokacin da mafi yawan al'umma suka rufemin tasu, ka haskamin rayuwa a lokacin da duhu ya lulluɓeta, ka zamemin gata, a lokacin da nake ƙasƙantacciya, duk wanda zaiga bilkisu a yanzu harta birgeshi kaine silar komai..........”
        Dad da yaji ƙwalla sun cika masa ido yasa hannu ya ɗaukesu yana ɗan murmushi da saurin dakatar da bilkisu, kafaɗarta ya kai hannu zai kamo sai kuma ya fasa, murya a sanyaye yace, “Haba ɗiyata ni bakimin komaiba wlhy, duk abinda kikaga ya faru a rayuwar ɗan Adam rubutaccene a littafinsa, ke yarinyar kirkice abin alfaharin kowanne uba, inajinki har cikin raina nima Bilkisu, duk kuma abinda ya faru kema ba laifinki bane namune, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci rayuwar aurenku ya baku zaman lafiya kinji, aje aita haƙuri, karki sake yin kuka domin hakan, ina fatan dai babu wata damuwa ko?”. Bilkisu tasa bakin gyalenta ta share hawayen tana gyaɗama Dad kanta, “Ba komai Dad, shiɗin mutumin kirkine, kullum ƙoƙarinsa yaga ya ƙyautatamin, zaɓin da kukaimin ƙyaƙyƙyawan zaɓine da nake alfahari da shi, na kuma tabbata har ƙarshen rayuwata insha ALLAH bazanyi nadama ba, nagode sosai da kulawarku a gareni”.
        Kallon inda Jawaad ke zaune tamkar baya a falon Dad yayi, cikin ƙara sanyaya murya yace, “Nagode sosai Jawaad, dama bana tsamanin saɓanin hakan daga gareka, ALLAH ya ƙara muku zaman lafiya.
         Jay ya ɗan ɗago idanunsa tare da tura wayarsa cikin aljihu. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Dad, irin kallon da kowa shi yasan ma'anar nasa. Jawaad ya janye idanunsa yana wani shegen murmushi da sake ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin yace wani abu Mom taja wani wawan tsaki tana miƙewa tabar falon.
          Duk muka bita da kallo banda boss da ya basa abinsa hankali kwance. sai da ta gama hayewa benen Dad ya sauke nannauyan numfashi yana sake kallon Jay, “Tana cikin fushine sosai akan damuwar ɓatan Mamana, duk inda muke tunanin samun yaron nan an gaza samunsa Jawaad, dama koda bakuzo nanba ni da kaina zanje gidanku akan maganar. Ka taimakemu dan ALLAH ”.
      Kafin Jawaad yay magana Bilkisu dake share hawaye tace, “Dad wani abunne ya faru da aunty Shahudah'n?”. Kansa ya jinjina mata cike da matsananciyar damuwa ya labarta musu komai, shi dai Jay baice ko uffanba, sai Bilkisu da keta sharar ƙwalla ita da Aamilah. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe abinsa yana kallon bilyn, “Tashi mu wuce” ya faɗa a daƙile. Kamar bily zata fasa kuka dan takaicinsa, ta buɗe baki zatai magana ya zuba mata wata uwar harara..... Tsam ta mi

ƙe tana haɗiye sabon kukan dake neman taho mata, “Dad zamu wuce”. Kallon Jay Dad yayi, “Jawaad bazaka bar mana ita ta yini ananba?”. Shiru yay kamar bazaice komaiba, sai kuma ya kalli agogon hannunsa ba tare da ya kalli Dad ɗinba yace, “Zamuje office ne”. “Shike nan to, kuɗan jirani”. Dad ya faɗa yana miƙewa.
       Jakar islamiyyar ya ɗauka yay ficewarsa batare da yacema bily komaiba.
        Da kallo kawai na iya binsa harya gama ficewa, naja numfashi ina danne zafin da zuciyata kemin, bansan miyasa boss yake hakan gasu Dad ba? Yana ƙara sakamin ruɗani da wasiwasine akan abinda naketa ƙoƙarin ƙaryatashi a zuciyata tun randa nai gamo da wallet ɗin nan...... Dawowar Dad ta katsemin tunani na, ya miƙamin leda babba mai ƙyau yana murmushi, “To ɗiyata ga tsarabarki nan, akwai kuɗinki na kayan ɗaki danai niyya sai dai hakan bata faruba, insha ALLAHU kafin kije gida zakiji alert, ALLAH ya ƙara zaman lafiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, na durƙusa har ƙasa ina masa godiya da addu'oin fatan alkairi. “Babu komai Bilkisu. karki damu tashi kuje yana jiranki”. Jinjina masa kai nayi na miƙe, na kalli inda Aunty Aamilah take zanyi magana, wata muguwar harara ta watsomin tana jan tsaki da ɗauke kanta ta nufi ɗakinta. Duk da naji babu daɗi sai nai ɗan murmushi kawai najuya ga Yah Salman. Shima koda nai masa magana bai amsamin ba, haka na baro inda yake jiki a sanyaye naima Dad da duk abinda ke faruwa yana kallonmu sallama na fice.
            Fa kallo Dad yabi Bilkisu harta fice daga falon, ya sauke nannauyan numfashi yana gyara babbar rigarsa, kallon Aamilah da keta cika da batsewa yay ya ɗauke kansa, batare da yace mata komaiba ya haye sama abinsa. Ɗakinsa ya wuce, sai da ya rufe ƙofar sannan ya ciro wayarsa daga aljihu yay kiran Qaseem. Bugu biyu Qaseem ya ɗaga kuwa. Dad ya sauke numfashi yana cire hularsa ya zauna a bakin gadonsa, “Qaseem gasu nan sun fito, dan ALLAH ka danne ranka karka bari rigimar da kuka saba da yaron nan ta shiga tsakaninku, mu lallaɓasa musan inda Mamana take dan nasan wlhy shi kaɗaine keda masaniyar hakan”. “Karka damu Dad, namaka alƙawarin a daren yau sau Shahudah ta kwana gida, yanzun nan zan kirashi a waya nace masa yazo ya sameni muyu magana”. Qaseem ya faɗa yana danne ɓacin ransa da mugun tsanar Jay dake cimasa zuciya. Sallama sukai, Dad ya ajiye wayar yana sauke numfashi da haɗiye tsantsar damuwarsa akan rashin abar ƙaunarsa mafi soyuwa acikin ƴaƴansa. Qaseem kuwa daga can kiran Jay yayi duk da yana tunani da wahala ya ɗauka tunda bayin wayar sukeba, a yanzunma sai da Dad ya turo masa number Jay ɗin dan bashi da ita da.

         A cikin mota na iske boss yana waya, bayan na shiga Sadiq ya rufe ƙofar kamar yanda ya buɗemin na shiga. Har muka kusa isa gida yana waya, koda kuma ya kammala bai kulani ba har muka ƙarasa gidan, a ƙofar gida yace Sadiq yay parking. Batare da ya kalleni ba yace, “Kije ciki”. Kallonsa nai zanyi magana ya sake ɗaure fuska. Haɗiye maganar nai kawai na ɗauki ledar da Dad ya bani zan fita ya riƙe ledan. Sake kallonsa nai, sai kuma na sakar masa ledar batare da nace komaiba na ƙarasa ficewa dan tsagwaron masifa na hango cikin ƙwayoyin idanunsa.
           Duk yanda naso riƙe hawayena a yanzu kasawa nayi, haka na shiga cikin gidan inayinsu duk da nasan Nabeelah tana a gidan kuwa. Kwance na isketa a babban falo tana barci, dan haka na wuce bedroom ɗina kawai na faɗa saman gado ina fashewa da wani kukan. Kusan mintuna biyar ina kukana kafin ƙarar shigowar saƙo ta sakani dakatawa, ɗaukar wayar nayi ina share hawayen dan zatona ko boss ne, zumbur na miƙe cike da firgicin ganin yawan kuɗin da Dad ya turo min. A fili nace, ‘Tashin hankali, kodai Dad bai lura baneba?’. Bani da mai bani amsa dan haka nai saurin yin dialing Number sa. Bugu biyu kuwa ya ɗaga, cikin rawar murya nace, “Dad a......” “Banason kice komai ɗiyata, kin cancanci fiyema da haka daga gareni kinji, ke dai ALLAH yay miki albarka”. “Nagode Dad, ALLAH ya ƙara buɗi na alkairi mai albarka”. Na faɗa cikin kuka. Ina jiyo sautin murmushinsa daga can, ya sake kwantar da murya yana lallashina cike da kulawa har sai da na

yi shiru sannan mukai sallama.
          Jikina duk babu ƙwari na tashi na shiga bayi nai wanka da alwala, na idar da salla ina ƙoƙarin tashi dan naje na tado Nabeelah sai gata tama shigo da sallama. “Ai bansan kin shigoba, Sadiq ne da kulolin abinci inji Yayanmu”. “Abinci kuma?”. Na faɗa ina ajiye sallayar. Tare muka fita, da mamaki nakebin manyan kulolin da kallo, dan abincine na kusan mutane goma sha biyar ma. “Sadiq wannan fa?”. “Oga ne yace na kawosu, amma inagafa baƙi za'ayi dan naji yana waya akan nanda awa biyu da wasu mintuna ma zasu iso”. Bilkisu dake kallonsa kawai tace, “Yana ina shi?”. “Da muka saukeki Barrack mukaje, bayan mun baro can kuma na saukesa a General hospital sannan naje na amso wannan abincin, yanzu can zan koma na ɗakkosa dan yace dubiya zaiyi”. 
          Sallama yay mana ya fita, ni da Nabeelah kuma muka kwashe kulolin muka kaisu kicin inata tunanin baƙi kuma daga ina zasuzo haka to?. Bani da mai bani amsa, dan haka na koma ɗaki danna gyara jikina, Nabeelah kuma tai alwala itama.

JAWAAD
Chapter 137 · 0% Book details