← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 168

Sashe 139

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

mbatonsa da komai a ɓangaren farin cikin rayuwar aurensu da akasinsa, gidan data haifi gudan jininta bayan shafe shekaru tana kuka da fatan samu. kallon Jay tayi hawaye cike da idanunta. A hankali ya kaɗa mata nasa kan yana ɗan murmushi. Ta sake damƙe hannunsa cikin nashi tana haɗiye abubuwa masu yawan gaske dake yunƙuro mata tun daga ƙasan zuciya har saman harshe. A hankali ya fara takawa da ita suka nufi ƙofar da zata sadasu da cikin gidan, suna gab da isa ƙofar falon Bilkisu ta fito cikin matsanancin hanzari.
         Nai saurin ƙarasawa garesu batare dana tuna da wani matsayinta na surukata ba, ni kallon uwa nake mata, uwa ɗinma mai muhimmancin gaske ga ɗa. sakin Jawaad Umm-Anum tai itama da sauri ta buɗema bily hannayenta, aiko tazo ta shige jikinta. A take hawayen da Umm-Anum ke maƙalewa suka gangaro mata saman kumatu. Kauda kai Jay yayi daga kallonsu saboda ƙwallan da suka cika masa idanu, sai ya tura duka hannayensa cikin aljihun farin wandonsa ya ɗaga kansa sama ya maida hawayen. Sai da ya tabbatar hawayen sun koma sannan ya sauke fuskarsa a kansu. Yanzu kam Bilkisu ta ɗago daga jikin Umm-Anum, sai dai su duka hawaye suke tana jeramata sannu da zuwa. Umm-Anum ta shafa fuskar bilyn tana ƙare mata kallo sosai, wani sassanyan murmushi ta sake saki da jawota jikinta ta sake rungumeta, dan ita kaɗai tasan mita gano.
           “Ummuna kumuje ciki, sai ku cigaba da murnan”. Jay ya faɗa a hankali kamar bashine yay maganarba. Kallonsa tai shima ta riƙo hannunsa suka sakata tsakkiya shi da Bilkisu, a haka suka shiga falon inda Nabeelah da Anum ke zaune surutu ya kaure tsakaninsu, Anuwar kuma ya tasasu a gaba yana kallon Nabeelah kamar ya samu wani majigi.
        Cak Umm-Anum ta tsaya tana kallon Nabeelah da itama tai mutuwar tsaye tana kallon mai tsananin kama da Ummahn ta. Kallon Jawaad Umm-Anum tayi cikin wani yanayi na alamar tambaya. Hannunta ya kama ya zaunar da ita yana ɗan murmushi, sai da ya tabbar ta zauna sannan ya kalli Nabeelah da ke ƙoƙarin gaisheta. Hannun Nabeelah ta kamo ta matso da ita jikinta, da ƴar rawar murya Umm-Anum tace, “Da ace mutum baya ƙara shekaru da girma ni dai da nace wannan Mariya ta ce Jawaad, kamar yanda nake kallon takwarata da kamannin Rahma”. duk da ba yaune karan farko da akace Bilkisu na kama da aunty Mah-mah ba a gabansa sai da ya kalli Bilkisun da tasha jinin jikinta, sai kuma ya ɗauke kansa yana zama kusa da Umm-Anum. “Ummuna ki kwantar da hankalinki kinji, dukkan abinda kike buƙatar ji zaki samu fiyema da hakan har sai kin gaji, yanzu dai kitashi a kaiki inda zakiyi wanka, kuci abinci ki kwanta ki huta, sai komai ya biyo bayan hakan kinji”.
      Kansa ta shafa da ja masa hanci tana faɗin, “Rigimammen Mama har yanzu dai ana taɓawa kenan”. Dariya duk su Anuwar sukayi, shi kuma ya zuba musu harara da kama hannun Umm-Anum ɗin ya miƙar da ita. Da kansa yay mata rakkiya har ɗakin bily, itama da tabi bayansu tai saurin shiga bayi domin haɗa mata ruwan wanka.

         Nabeelah na ganin Jay da bily sun shige da Umm-Anum tai saurin ɗaukar wayarta ta turama Ummah babba saƙo.
      Sai da suka tabbatar Umm-Anum ta shiga wanka sannan Jawaad ya fito, kayansu da Sadiq tuni ya gama shigo musu da su ya saka Anum ta ɗauka na Umm-Anum ta kai mata ɗakin Bilkisu, shi kuma ya kai Anuwar ɗakin baƙi inda zai zauna, Anum ma ɗakin baƙin dake cikin falon bily zata zauna. Bilkisu da Nabeelah da keta ALLAH, ALLAH su Ummah su iso sukai hidimar shirya abinci su kuma a tsakkiyar falon, dan yanda Umm-Anum ta gaji bai kamata a sakata zaman Dining ba.
       Tana son tabi Jay ɗakinsa dan ta nuna masa farin cikin data shiga na bazatar da yay mata akan zuwan su Umm-Anum amma haushinsa da takeji ya hanata aikata hakan, sai kawai ta sharesa ta cigaba da harkokin gabanta, dan farin cikin ganin su Umm-Anum ya shafe mata duk wani damuwarta kuma.  
           A ɓangaren Jawaad shima tun shigowarsa ɗakin ya ke zuba idanu ya ga bilkisu ta biyosa amma sai yaji tsit, duk da farin cikin ganin mahaifiyarsa da ƙannensa ya shafe masa duk wani ɓacin ran da ya samo daga Qaseem da gidan Dad hakan bai hana ransa sosuwa ba da ƙ

in shigowar Bilkisun, sai huci yake da jera tsagwayen ƙwafa, ayyanawa yake a ransa sai yayi maganin miskilancin yarinyarnan a yau ɗin nan basai gobe ba, dan ya gama lura gadon barcinsa da ta gama ganine yasa take neman fara kawoma rayuwarsa raini (Ka manta wulaƙancin da kai mata kai ɗazun saraki🙄😜).
          Tashi yay da ga kwancen da yake saboda jin an fara kiraye-kirayen sallar Magriba. Alwala yayi sannan ya fito, a babban balo suka haɗu da Anuwar da shima ya fito daga sashen baƙi da alamar shirin tafiya masallacin. Yayma abincin da aka shirya a tsakkiyar falon kallo ɗaya ya ɗauke kansa batare da yace komaiba suka fice shi da Anuwar dan falon babu kowa cikinsa.
             Da taimakon Bilkisu Umm-Anum ta dawo falon bayan an idar da sallar Magriba, suna zama Ummah babba da Ummah ƙarama da Batool nayin sallama, cikin matsananciyar faɗuwar gaba Umm-Anum ta juya tana kallon ƙofar dan ko'a cikin magagin barci waɗannan muryoyin sunfi gaban mantuwa a gareta balle ma a zahiri.
        Kasancewar akwai hasken Genretor da aka kunna tas suke ganin junansu, da ga Ummah ƙarama har Ummah babba jikinsu rawa yake da tsuma sosai, sun ƙurama Umm-Anum idanu tamkar yanda itama ɗin kallonsu take bata ko ƙyaftawa. Su dai su Bilkisu kallonsu kawai suke da son ganin yaya za'a kwashe. A haka Jawaad da Anuwar suka shigo suka samosu. Jay ya kalli su Ummah da mamaki sai kuma ya kalli Nabeelah da ya tabbatar itace da wannan aikin. Aiko sai tai ƙasa da kai gabanta na faɗuwa dan tsoro ta koma bayan bily ta maƙale.
      Ɗauke kansa yay daga gareta, ya ƙarasa gaban su Ummah ya tsaya a tsakkiyarsu, hannayensu duka ya kama a cikin nasa, a take duk suka ɗago suna kallonsa hawaye na gangaro musu saman fuskokinsu. Yanda laɓɓansu ke rawa zai baka tabbacin magana suke son yi amma sun kasa saboda ruɗani. Jay yaɗan murmusa yana mai lumshe idanunsa ya buɗe alamar tabbatar musu da wadda suke hasashen ce ba mafarki bane ko gizago. Cikin ƙarfin hali Ummah Babba tace, “Yarona da gaske kake Yaya Bilkisu ce a gabanmu ba mafarkin da muka sabayi bane?”. Yanzunma kansa ya jinjina musu, ya kuma ja hannayensu har gaban Umm-Anum da alamu ya nuna suman zaune tayi. Hannayensu ya saka a cikin nata yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi yaja jikinsa baya.
           A gaban Umm-Anum Ummah ƙarama da Ummah babba suka zube suna fashewa da kuka mai tsuma rai da cin zukata. Umm-Anum ta kawo nannauyan numfashi lokacin da suka rungumeta su duka biyun a jikinsu.
       Su Bilkisu dake kallonsu suma hawayen sukeyi, Jawaad kansa sai da ƙwalla ta cika masa idanu, amma jarumta ta saka shi haɗiye kayansa ya koma cikin kujera ya zauna yana jin wani irin matsanancin farin cikin da ƙirjinsa ma ke neman gaza ɗauka. Su Ummah sunkai kusan mintuna huɗu zuwa biyar a jikin Umm-Anum suna raira kuka kafin su saki juna, hannayenta ta ɗaura saman kumatunsu tana shafawa da murmushi saman fuskarta ga kuma hawaye, suma dai murmushin sukeyi hannayensu duka akan nata kumatun suna share mata nata hawayen. “Ashe Mariya ta da Wasila basu girmaba har yanzun? Ashe shagwaɓar nan da akema Yaya tana nan ba'a fasaba”. Dariya ta kwacema su Ummah lokaci guda da kuka, jikinta suka sake faɗawa ta rungumesu tana dariya. Su ma ƴaƴansu dariyar sukeyi da hawaye banda Jay da murmushi ne kawai a saman fuskar tasa.
       Da sauri Umm-Anum ta sake ɗagosu tana faɗin, “Ina Rahmah take ita kuma? Ko ba'a nan take aure ba?”. Duk ƙasa sukai da kawunansu hawaye masu zafi sosai na sake rige-rigen fitowa daga idanunsu, Umm-Anum ta shiga girgiza kanta a hankali tana kallonsu a tsorace, “Karku cemin na rasa Rahmah Mariya, kar kucemin rabuwa ta har abada nayi da Rahmah dan ALLAH” “Sai dai haƙuri Yayah, Rahma ta jima da barinmu gaba ɗaya, ta tafi tafiya mai nisan zango da babu iyakar sake ganin juna sai idan ALLAH ya ƙaddara hakan a can wata rana”. Ummah babba ta faɗa zuciyarta na mata zogi tamkar a yaune Rahmah tabar duniya. Yanzun kam Umm-Anum ce ta fashe da kuka mai tsuma rai da cin zuciya, tana son Rahmah, tana ƙaunar Rahma sosai, dan tafi shaƙuwa da ita a kaf cikin ƴan uwanta.
       Ganin kukan nasu yana neman yin yawa gashi ha
Chapter 139 · 0% Book details