Sashe 154
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da kaushin murya Jawaad daya tsare su Nabeelah da rikitattun idanunsa yace, “Miya kawoku nan?”. “Uh...Uhm Yayanmu bamu kaɗai bane, Ummu ce tace a kawota wajen Alhaji babba”. Nabeelah ta bashi amsa tana laɓewa bayan Anum idanunta cike da tsoro.
Da sauri Jay ya hau waige-waige, saiko idanunsa suka sauka akan Batool da su Ummah da suma kallonsu sukeyi. Batare da ya sake cewa komaiba yabar wajen zuwa inda su Batool ɗin suke.
Umm-Anum data rage a mota bata fitoba hango Jay ya nufosu ta fito da ƙyar dan jikinta duk babu daɗi, kallo ɗaya zakaima idanunta kuma kasan tayi kuka sosai, dan su
n kumburi sun kumayi jaa.
Sauri riƙeta Jawaad daya ƙaraso yayi, ya taimaka mata ta tsaya akan ƙafafunta sosai tana sauke ajiyar zuciya, “Ummuna miyasa kuka fito? Kallafa ƙafarki ta kumbura?”. Maimakon ta bashi amsa sai tambaya ta jefa masa, “Ina Bilkisu?”. “Amma Umm......” “Ni dai ina yarinyata nace maka?”. Numfashi ya sauke da ɗan ƙarfi yana lumshe idanu sai kuma ya buɗe lokaci ɗaya, “Tana ciki Ummuna, sun saka mata drip ne saboda ta suma acan, amma inama ganin ƙila ta farka yanzun dan tun ɗazun Dr Bello ya sanarmin ta farfaɗo”. “Alhmdllh, babana fa”. Yanzu kam ɗan murmushi ya mata da sumbatar hannunta, “Shiyyasa naga idanunki sun kumbura ko Ummuna, kinyi kuka?”. Kansa ta dungure tana ƴar hararsa, yay murmushi da kama kunnuwansa alamar na tuba.
★★★★
Sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Bilkisu, kamar yanda Jawaad yay hasashe sun iske ta farka, tana zaune jingine da filo wata Nurse na bata abinci da takeci da ƙyar dan warin asibitin yay masifar addabarta, farkawarta amanta biyu saboda warin asibitin, yanzu ma Dr Bello ne da kansa yasa aka kawo mata abincin dan taci tasha magani kafin Jay yazo ya ɗauketa kamar yanda ya sanar masa.
Gaba ɗaya tayi wani zuru-zuru, idanunta sunyi masifar kumbura da ƙanƙancewa, sannan sunyi jajur a ciki. shigowar su Jay yayi dai-dai da zaburarta ta sakko a gadon saboda tahowar amai, Nurse ɗin ta ajiye tray'n abincin da sauri tana ƙoƙarin kamota amma tuni takai toilet. Duk rufa mata baya sukai cikin tashin hankali, sai dai duk a ƙofar bayin sukaja birki, Jay da Nurse ɗin ce kawai suka sami damar shiga. Sosai hankalin Jay ya tashi ganin yanda bily ke yunƙurin amai tamkar zata amayo hanjin cikinta, Nurse ɗin na riƙe da ita tana jera mata sannu da shafa bayanta. Matsowa yay kusa da ita shima ya ruƙo hannunta. Da ƙyar aman ya tsagaita, ya taimaka mata da kansa ta wanke bakinta, sai numfashi take saukewa a wahale, kwantar da ita yay a ƙirjinsa tausayinta mai tsanani yana ratsashi, a ƙasan ransa kuma tunani yake ‘mi taci haka?’.
“Ka kaini gida, banason warin asibitin nan”. Ta faɗa murya can ƙasan maƙoshi tana sake lafewa a jikinsa da shaƙar ƙamshin turarensa da yake ɗan dawo mata da nutsuwarta. Ɗago kanta yay ya saka fuskarta cikin tafukan hannunsa suna kallon juna, “Mi kikaci haka?”. Ya faɗa cikin tashi daskararriyar muryar yana raba idanu akan fuskarta tamkar zai gano abinda ke damunta anan ɗin. Matsawa tai zata sake kwanciya a jikinta tana faɗin, “Banci komaiba, warin asibitinne banaso nidai”.
“Jawaad yaya dai?”. Ummah ƙarama ta faɗa kafin ya samu damar sake tambayar bily.
Da sauri naja baya daga jikinsa dan na manta bafa mu kaɗai bane, bango na dafe saboda jikina babu ƙarfi. Ban iya fahimtar amsar daya bataba dan hankalina baya a garesu, tadai riƙe hannuna ta kamani muka fita sunata jeramin sannu.
Jay da duk damuwa ta sake lulluɓesa ya fita domin son ganin Doctor dan yazo ya duba Bilkisun ko akwai wata matsala data sakata aman ne.
A ƙofar ɗakin sukaci karo da Dr Bello da Nurse ɗin dake tare da bilyn, da alama itace taje tai kiransa. Fuskar Dr Bello washe da murmushi ya miƙama Jay hannu, “Dadyn baby ai bansan ka shigoba ma”. Duk da Jay bai fahimci sunan da yay kiransa da shiba sai yaɗan saki fuska kaɗan amma ba murmushi yayi ba, yadai sassauta ta daga cinkushen da take. Doctor bai gajiyaba ya sake faɗin, “Dama sister ce ke sanarmin madam na amai, wannan babyn da alama soja ne, dan nakula zai wajiga madam da yawa tun yana ɗan ficit”. Yanzunkam dai sosai Jay ya kallesa da alamar tambaya, sai dai ya gaza cemasa komai. Lura da hakan da Dr Bello yayne ya sakashi yin murmushi suka ƙarasa shiga ɗakin da Bily take, inda su Umm-Anum suka zagayeta sunata jera mata sannu, kanta na'akan cinyar Ummah babba.
Sai da ya gaisa da su sannan yayma bilyn sannu, kanta taɗan ɗaga masa kawai alamar amsawa, ya sake kallonta da murmushi ganin tanata faman rufe hannci, juyawa yay ya sake kallon Jay dake tsaye hannayensa duka a aljihu shima yana kallon bilyn. “Congratulations dear Friend, madam na ɗauke da babien mu ɗan sati shida. Ma'ana tana ɗ
auke da ciki ɗan wata ɗaya da sati biyu”.
Babu shiri Bily ta janye hannunta daga saman hanci tana waro idanu waje, ganin duk yanda suka zuba mata ido suna murmushi yasa taji kunya, saurin juya baya tayi taja gyalen Ummah babba ta rufe fuskarta ƙirjinta na wata irin bugawa da sauri-sauri.
Su Ummah kam fuskokinsu washe da murmushi sunata jerama UBANGIJI godiya da kirari, gaba ɗaya sai damuwar da suka yini da ita ta ɓace ɓat. Ubangayya da tunda aka fara cakwakiyar nan babu mai cewa yaga haƙorinsa a waje a take ya saki wani lallausan murmushi yana mai lumshe idanu, duk wata damuwarsa sai yaji ta gudu, farin ciki ya mamaye gurbinta. Dariyar su Ummah ce ta sakashi buɗe lumsassun idanunsa dake jajur, yay murmushi a karo na biyu yana girgiza kansa ganin iya shegen da Anuwar keyi shi da Anum da Nabeelah. Ya dage sai rawa yake yana waƙar larabawa shi a dole yayi ɗa ko ƴa, yayinda Anum da Nabeelah ke tayashi.
Cikin dariya Ummah ƙarama tace, “Yarona dama haka kake da iya shege ina ganinka wani ustazu?”. Umm-Anum dake murmushi tana kallon Bily da duk abin nan da ake taƙi kallon kowa tace, “Kaɗanma kika gani indai Anuwar ne, dama can Ustaz ɗin da babu Ustazai ne”. Dariya su Ummah da Batool da Dr Bello suka sanya, Jay dai murmushine har yanzu a saman fuskarsa, kunyar iyayensa ta sakashi dakewa abinsa yanata dai kallon bilyn ta ƙasan ido.
Aunty Batool tace, “Lallai ta maganar Doctor babyn nan namu soja ne, inba soja ba wannan gumurzu da akashawo amma ko gezau baiyiba saima nuna kansa da yayi wa duniya”. Sosai nanma suka sanya dariya, Dr Bello yace, “Gaskiyarki Sister kam, ALLAH dai ya inganta, kema saiki daure kiyi aure ki samo mana namu”. Duk kallon Doctor sukai banda Jay da Bilkisu dake ɓoye, Batool ta zuba masa harara. Shiko murmushi yayi abinsa yana sosa ƙeya waishi yaji kunyar su Ummah. Cike da tsokana Anuwar yace, “Su Aunty Batool kodai-kodai gidan Doctor zamu ɓulla ne?”. Duka takai masa ya kauce yana dariya, Doctor Bello ya kama hannun Anuwar yana faɗin, “Yauwa ɗan ƙanina tayani yaɗa manufa”. Yay maganar suna ficewa daga ɗakin.
“A to mukam wannan indai na ƙwaraine ai bashi zamuyi Batool”. Umm-Anum ta faɗa tana kallon Batool ɗin. Ƙasa tai da kanta batace komaiba. Ummah ƙarama tace, “Yayah wlhy bansan ko Dr Bello da wata matsalaba, mutum kirkine ɗan manyan mutane, sai dai babansane ɗan rigima, amma shima bawai ta ashsha ba”. “Ato Alhmdllh, bara nazo na fara shirin aurar da ɗiya kenan”. Murna Nabeelah da Anum suka fara, ita dai Ummah babba batace komaiba, hakama Jay uffan baice ba, yayi kamarma baya a ɗakinne, idonsa gaba ɗaya yana akan motsin matarsa.
★★★★★★★
Koda suka baro ɗakin da bily take da sallama daga Doctor gaba ɗaya sai suka nufi ɗakin da aka kai Alhaji babba, daga shi sai baba maigadi a ɗakin, jikin Umm-Anum har rawa yake, sai da Batool ta riƙeta, cike da sassarfa ta ƙarasa gaban gadon da Alhaji babba ke a ƙwance an saka masa na'urar taimakon numfashi, sosai jikinta ke ɓari, ta durƙushe ƙasa tana kamo hannunta cikin nasa da fashewa da kuka tana kiran sunansa. “Baba kaine haka? ka tashi baba kaga BILKEESUN ka, nadawo gareku baba, baba ka buɗe idanunka ka kalleni dan ALLAH kozanji sassauci babana farin cikina” ta ƙare maganar da ɗaura kanta a gefen hannunsa tana kuka mai tsuma rai. Suma su Ummah hawayen sukeyi har Bily, Batool da Nabeelah da Anum. Anuwar ma hannu ya saka ya ɗauke nasa ƙananun hawayen tare da ƙarasawa ya durƙusa ta ɗayen gefen kakan nasa daya fara gani a yau karan farko na rayuwarsa, Anum tazo kusa dashi ta tsugunna itama tana ɗaura hannunta akan na Anuwar dake riƙe dana Alhaji babba. Jawaad dai yana kallonsu, sai dai bazaka taɓa fahimtar yanayinsa ba, kamilar fuskarsa ta shanye komai.
A hakanli Alhaji babba yaɗan motsa hannunsa dake riƙe a cikin na Umm-Anum, saurin ɗagowa tai tana kallon hannun, ya sake motsashi a karo na biyu tare da kansa. tsitt ɗakin yay duk suka zuba masa ido. Sake motsawa yay fiye dana farko, sai kuma ya buɗe idanunsa a hankali ya sake maidawa ya rufe saboda nauyin da sukai masa, sake buɗewar yayi a karo na biyu, dishi-dishi y