Sashe 38
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ba da aikina”. Yanda yay kicin-kicin da fuska ya tilasta min komawa na kwanta yanda yake buƙata. “Mike miki ciwo?” ya jehomin tambayar a kausashe. Bansan sanda na tura baki gaba ba nace, “Nifa kainane kawai sir”. Bai tanka minba yamiƙe yabar wajen, ban sake sanin mi yakeyiba saboda ciwon ya dawo. Saida ya lafamin ne na buɗe ido naga Ummie durƙushe a gabana tanamin sannu, hannunta na kama na riƙe ina hawaye, “Ummie ki taimakeni kiyi masa dabara mubar office ɗin nan dan ALLAH”. Kanta ta jinjinamin tana gogen hawayen, tace, “Mararki ke ciwo ne?” da sauri na ɗaga mata kaina ina cije baki. Nace, “Koda yaushe zai iya fitowa wlhy Ummie”. Cikin ƙara rage murya ƙasa Ummie tace karki damu bara nai masa magana”.
Jawaad da duk ke saurarensu daga inda yake zaune ya girgiza kai kawai. Mutum ne shi da ALLAH yayma baiwar jii, dukda ahankali suke maganar yana jiyosu batare da sunyi tunanin hakanba. Koda Ummie ta miƙe zuwa inda yake domin ta tsarashi kamar yanda Bilyn ta buƙata sai yace ta tafi. Babu ƙofar yimasa musu, dan haka tabi umarni ta fice tana waigen bilyn. Waya ya ɗauka shikuma ya tura saƙo. Cigaba yay da aikinsa kamar ya manta da Bilkisu a office ɗin, lokaci-lokaci yakan amsa waya koshi ya kira. Kusan mintuna ashirin da tura saƙonsa aka kawo masa abinda ya buƙata, Gimba ne ya shigo ya ajiye ledan hannunsa bayan ya gaishesa.
Sama-sama nake jin muryar gimba a office ɗin, kafin kuma naji alamar fitarsa. Ƙamshin turaren Boss da naji a akaina ya sakani buɗe idanu, yace, “Tashi zaune” babu musu na tashi, a raina ina murna zai barni na tafi, abinda ke cikin ledar ya fiddo sai naga magunguna ne, batare da ya kalleniba yace, “Kinci abinci?”. A hankali nace, “Nasha tea tun a gida”. Baice komaiba ya miƙe. Naɗan bisa da kallo sai kuma na janye idanuna ganin ba fita zaiyi daga office ɗinba, bansan mi yakeyiba saboda ya juyamin baya, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya juyo ɗauke da kofi, ya zauna a table ɗin tamkar ɗazun yana miƙomin tea ɗin daketa turiri, sai cake, yanda yay da fuskane ya tabbatarmin babu wasa, ya miƙe yana faɗin, “minti biyar na baki kuma”. Bance komaiba nidai sai fuska dana kumbura. Dayake yunwar nakeji kuma tea ɗin ya haɗashi dai-dai yanda zan iyasha gashi babu suga sai gashi na shanye naci cake ɗin, ina ajiye kofin yana dawowa wajen hannunsa ɗauke da ruwa, nidai kaina a ƙasa naƙi kallonsa, dan dauriya kawai nakeyi kar yaga na cika raki, sai haɗiye kukan dake tahomin nakeyi da sauri-sauri, da kansa ya ɓalla maganin ya miƙamin. Amsa nai babu musu na zuba a baki, ya miƙamin ruwan shima, na kammala sha ya amsa yana min nuni dana kwanta. Ban musaba dan babuma damar yin musun na koma na kwanta kamar ɗazun, shikuma ya miƙe zaibar wajen. Bansan lokacin da harshena ya suɓuce nace, “Sir dan ALLAH kai min addu'a a ruwa ka bani nasha, sannan ka tofamin, jinake jikina kamar ana kunna garwashin wuta”. Cak ya tsaya, sai kuma ya juyo a hankali tamkar mai ciwon wuya ya zuba min idanu. Lumshe nawa nai hawayen da nake maƙalewa suka silalo.
Wani irin bugu ƙirjin Jawaad yake da sauri-sauri, ga wani irin sanyi na ratsashi daga saman kai har yatsan ƙafa tamkar wanda ake tsundumawa cikin ƙanƙara, mafarkinsane na daren jiya yake rige-rigen dawo masa a kwaƙwalwa. Bayan gushewar kuwwar halittu masu ban tsoro da ya samu damar yin addu'a ta koresu, sai furucin ƙarshe na cikin mafarkin daya fito daga bakin wata murya mai amo da baisan daga ina ta ɓulloba ita kuma, yay masa tsaye cak a zuciya yakuma kasa fashin baƙi a kai harya iso office ɗin nan, {Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini ta tabbata, rashin gaggawa zai tabbatar da zubewar jinane, hhhhhhhhh karku manta! Karku manta!! Karku manta!! Hhhhhhhhhhh!!!!}......... “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” ya shiga ambata lokacin da yaji gilmawar abu shuuu ta bayan kunnensa, da dawowar maganar tamkar a yanzu ake mai ambatonta ke faɗinta, hankalinsa ne ya dawo jikinsa. ya kalli inda bilkisu take kwance har barci ya fara fisgarta, samun kansa yay da tsira mata idanu a zahiri, a baɗini kuma taurarin cikin mafarkinsa ne daya koma barci bayan yayi addu'a da nafila ne suke
masa kaikawo, yay ƙoƙarin tuno furicin mahaifinsa aka taurari huɗu da sukafi kowaɗanne haske acikin taurarin da ya gani, sai guda ɗaya shima mai tsananin haske amma ya matsa nesa dasu sosai, ya kasa tuna komai da Abba ya faɗa masa akan taurarin, kansa ya shiga yamutsawa cikin wani irin yanayi, a fili ya furta, “Jiya wace irin ranace?”. “Ranar da zata zama cikin ranakun tunawa daga nan har ƙarshen numfashi”. Bily da idanunta ke rufe har tana sauke numfashin tabbatuwar barci ta faɗa cikin motsa labɓanta da sauti mai sanyi, badan ALLAH ya yisa mai jii ba da bazai taɓa fahimta ba. Dukda yaji wani abu a ransa game da amsar tata sai ya tureshi da tunanin ai a fili yay magana shima, tajisane shiyyasa ta bashi wannan amsar, to amma abin tambaya anan miyasa ta bashi amsar a haka?. Ƙirjimsa yay wani irin motsawa, kiran sunata ya shigayi amma ko motsi bataiba alamar barcinta yayi ƙarfi. Ƙwaƙwalwarsa ma saita gaza tunanin komai, samun kansa yay da fara mata addu'ar data buƙata kawai ya shiga tofa mata akan fuska, gani yay ta saki wani lallausan murmushi tana motsa laɓɓanta, yay saurin kai kunnensa amma bayajin komai, ɗagowa yay ya kalleta sai kuma yaga ta yamutsa fusaka ta maida fuskarta ta haɗe. Yay shiru yana kallonta kafin ya miƙe yabar wajen.
Cikin ƙanƙanin lokaci barcin Bilkisu yay ƙarfi sosai saboda maganin na saka barci, gashi dama bawani isashen barci ta samu a daren jiyaba, Jawaad kam ya cigaba da ayyukansa har akai kiran sallar zuhur. Tashi yay ya shiga toilet yay alwala ya fito, idanunsa suka sauka akan bily dake takure cikin kujera alamar sanyi takeji. Takawa yay a hankali wajen zamansa, rigar suit ɗinsa dake jikin kujerar a rataye ya cire ya nufeta, lulluɓa mata yay dukda bata rufe har ƙafafuba, cikin barci ta sauke ajiyar zuciya jin ɗumi ya ratsata, ya ɗan lumshe ido ya buɗe yana girgiza kai, sai kuma ya kalli agogo ya nufi hanyar fita da hanzari ganin zai makara salla.
Koda aka fito salla bai dawo office ɗinba ya amsa kiran da Sir Ahmad ke masa a office ɗinsa.
★★-:-:-:-★★★-:-:-:-:-:-★★★-:-:-:-★★
Ƙarfe biyu da wasu mintuna Dad ya isa asibiti, daga airport bai zarce ko gidaba yasa driver ya wuto dashi dan ya matsu yaga jikin mamansa, zuwa lokacin Shahudah ta farfaɗo, sai dai daka ganta kasan tanajin jiki, tayi zuru-zuru, farar fatarta tai jajur musamman fuskarta ma, Dad ya zauna a bakin gadon kusa da ita yana mai shafa gashin kanta fuskarsa a ƙwaɓe tamkar zaiyi kuka dan tausayinta. “Sannu kinji mamana, ALLAH ya baki lafiya”. Hawayene suka ziraro a kumatun Shahudah, ta kama hannun Dad ta riƙe tana magana a hankali saboda nauyin da ƙirjinta yay mata, “Dad bazan samu lafiyaba, mutuwa zanyi, tunda Bb baya buƙatata gara na mutu, Dad cayayfa mun rabu kenan har abada, ya daina sona Dad, Dad mut......” saurin ɗora hannunsa yay akan bakinta yana girgiza kansa, “Mamana bazaki mutuba, ni da kaina zan roƙesa, ko durƙusa masa ta kama zanyi Mamana danki samu farin ciki, indai ina raye a duniya babu ɗayanku da zai nema abu ya rasashi ko menene shi, danku kawai nake neman arziƙi, nai miki alƙawarin saikin koma wajen Jawaad kinji, zaku sake rayuwarku ta jin daɗi fiyema da da har ki haifamin jikoki, nidai abinda nakeso dake ki kwantarmin da hankalinki ki samu lafiya, namiki alƙawarin daga nan ko gida bazaniba office ɗin Jawaad zanje kinji”. Kanta ta ɗaga tana zubda hawaye, tace, “Kaje dan ALLAH Dad, ka faɗa masa ina sonsa, idan ya barni mutuwa zanyi, wlhy namasa alƙawarin ko a daren yau yakeso yamin ciki na haihu gobe, na kuma samin wani jibi, ko ƴaƴa ɗarine zan haifa masa indai zamu kasance tare har abada”. Wata irin kunya ce ta tsargama Doctor jin furucin Shahudah wai ko yau ai mata ciki ta haihu gobe, a ransa yace anya kuwa wannan ƴa da ubane? ‘to irin wannan manya-manyan zance haka babu risinawa’ yaɗan girgiza kansa yana mamakin yanda tarbiyyar yaran hausa fulani keta ƙara ƙuɓucewa a hannun iyayen wannan zamanin, a ganin ko uwa mace ya dace ƴa taji nauyin buɗe wani lafazin a gabanta inba doleba balle uba namiji, gashi ya kula shi Dad ɗinma ko a jikinsa, saima biyema Shahudah da yake sakeyi yana lalla