← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 168

Sashe 147

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da mafarkin mu na watan jiya dangane da ita. Jariri wannan itace dama ta ƙarshe da zamu baka akan wannan yarinya, Bakandamiyar mu na buƙatar jininta tunda budurcinta ya gagara, Jariri, idan ka gaza hakan daga nan zuwa kwanaki biyu zaka fuskanci mummunan hukunci daga Bakandamiya, zakuma mu saukeka daga shugabancin da kake kai. Sannan Jariri a yau ɗinnan ka tabbatar an sake ɗaura igiyar aure tsakanin gudalliyarka da yaron nan, inba hakaba bazamu yafe makaba a wannan karon dolene ka bamu jinin gudalliyarka........” “Tuba nake uwargijiyarmu, tuba nake uwa maba da mama, tuba nake mai share kukanmu, ina sake roƙon alfarmar a barni da gudalliyata dan itace zuciya ta, zan iya yarda na rasa abubuwa da yawa amma banda gudalliyata ya shugata, nayi rantsuwa da shugaban shaiɗanu a yau sai igiyar aure ta ƙullu tsakanin gudalliyata da halattaccen jinin Bakandamiya. Ina mai sake rantsuwa da a gobe saina kawo jinin wannan yarinya wa Bakandamiya shine zai zama abin kalacin mabiya Bakandamiya yake abar bautarmu”. (wa'iyazubillah😭🙏🏻) “Bakandamiya ta amsa maka, ta kuma baka damar ƙarshe ta dawowa da martabarka tare da dukkan muhimman abubuwan ƙungiya dake a hannun yarancan da jininsu ya halatta ga Bakandamiya. Kurakuranka zasu goge a dutsen rubuta laifuka bayan ka cika alƙawuranka da jinin babban ɗanka Jariri kamar yanda yake a rubuce a sharuɗan Bakandamiya”. “Naji na karɓa yake mai biya mana dukan buƙatunmu”. “Hhhhhhhhhhhhhhhhh!!!!!!!!!!!!!!” ta kece da wata mahaukaciyar dariyar da ta saka duk saida muka toshe kunnuwanmu saboda yanda dajin gaba ɗaya yake amsawa bama gidan kawai ba, tanayi tana tsiyaya masa wani abu mai kama da jini a cikin ƙoƙon hannunsa. Da baya baya ya baro gabanta yana wasu surkulle da shi kaɗai yasan abinda yake faɗi, sauran na amsa masa. Mamaki, tsoro, al'ajab da ruɗani duk suka saukarmin lokaci guda ganin Dad a inda tunanina ko tsammani bai taɓa raya minba, saurin ɗaura hannuna nai na rufe bakinna jin kuka na neman kufce min. “D... Da...Daddy!!”. na faɗa cikin rawar murya dana jiki ina mai matsawa jikin boss dake tsaye abinsa yana kallonsu Dad ɗin shi da su Oga Hafiz. Cikin matsanancin furgici Dad ya saki ƙoƙon hannunsa da kai dubansa inda yaji muryar da bai zatoba ta ambaci sunansa. Ido huɗu sukai da bilkisu da jikinta ke wani irin matsanancin tsuma. A take Dad ya zazzaro idanu waje cikin tsananin firgici da ruɗani, jikinsa sai wata iriyar tsuma ya keyi domin ganin wadda bai taɓa zato ko tsammani ba. duk da glashi ya raba tsakaninsu, bai gaza gane bilkisu da Jawaad ba harma da jin furucinta raɗam a kunnuwansa, dan basu da wani shamaki wajen iya jiyo maganar juna duk da akwai hilashin daya rabasu. Bansan sanda wani ƙarfi da zafin nama yazomin cikin jini da jiki ba na bigi gilashin wajen da ƙafa jikina karkarwa saboda wata irin mummunar tsanar sa ce ta saukarmin lokaci guda da ƙyamarsa. Sauran abokan shaiɗancin nasa da tuni suma sun mike suna kallonmu a cikin matsanancin firgici na alamun bazata a fuskokinsu suka shiga ƙoƙarin motsawa cikin rawar jiki dan neman kariya. Kafin suyi wani yunƙuri su Jabeer sun afko suma tare da su Ummie dake jiran umarni a waje. Zagayesu akai da bindugu, hakan ya tabbatar musu basu da wata dama kuma saina miƙa wuya........ “Ƙassaaa!!!!” Boss ya faɗa a iya ƙololuwar hasala jijiyoyin jikinsa na sake mimmiƙewa. Durƙushewa sukai bisa gwiwoyinsu suna aza hannayensu bisa kawunansu alamar yin surrender. Ban samu dawowa hayyacina ba daga kallon al'ajabi da ruɗanin da nakema Dad sai da Wani irin ihu shaiɗaniyar matarnan da tayi ya shiga dodon kunnena. miƙewa tsaye tai da buga sandar hannunta ƙasa, a take ɗakin ya fara turniƙewa da hayaƙi, sake bugawa tayi, sai jikinta ya fara canja launi harda su Dad ɗin suma. ta ɗaga zata buga na uku nai wani wawan tsale na dire a gabanta na riƙe sandar. Bazan iya fassara muku mawuyacin halin dana shiga ba a wannan lokacin, domin tsafi gaskiyar maishi ne, abinda kawai nake iya jiyowa harmutsewar wajen da ƙarar harbe-harbe ta waje alamar musayar wuta ta ɓarke tsakanin wasu a cikin jami'anmu da suke a waje da yaransu masu tsaron gidan.......
Chapter 147 · 0% Book details