← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 168

Sashe 85

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

              Office Jay ya koma domin cigaba da tarin ayyukan dake gabansa, dama yana tsaka da aikinne Ummu ta kirasa akan yaje can gidan yanada baƙi, dole ya ajiye ya tashi ya tafi. Fatansa ya rage ayyukan sosai, gashi yanason ɗaukar hutu kona sati ɗayane, duk da dai Sir Ahmad yace bai isaba na sati biyu zai ɗauka shima yaje yasha angwanci da ƙyau.
           Zamansa baifi da mintuna talatinba baƙon da yake jira ya iso, sai da akai masa iso sannan ya bada izinin a shigo dashi, ba kowa bane baƙon face Sulaiman yayan Amina, Jay ya ɗago daga abinda yake fuskarsa a sake dukda dai ba murmushi yake ba. hannu ya bashi suka gaisa kafin ya miƙe ya kawo masa abinsha baya. ya nuna masa wajen zama, yah Sule yay godiya. Ɗan murmushi kawai Jay yayi baice komaiba. Sai da ya ɗan sha ruwa sannan Jay yace, “Yaya ake ciki Sulaiman? ka gano ina yake?”. Numfashi yaya sule ya sauke yana gyara zama, “Wato ni abin nasu yanzu ya fara ruɗar dani oga, nama rasa wanene mara gaskiyar tsakanin Alhaji Alin da Hajiya Humairan? A yanda bincikena ya nunafa Qaseem baya ƙasarnan”. “Baya ƙasar kuma?” Jawaad ya faɗa yana tamke fuska cike da ɗunbin mamaki kuma. “Ƙwarai kuwa wannan itace magana ta gaskiya, saura kwana ɗaya a ɗauki azumi ya tafi, kuma abinda na fahimta lafiyarsa ƙalau ba kamar yanda ku anan office yace zaiyi zaman ganin likita a gidaba”. Shiru Jay yayi yana juya al'amarin a ransa, tun randa ya fiddo Qaseem a cell bai sake ganinsa ba, sai ana gobe za'a fara azumi, ya shigo station amma baifi awa uku ba ya tafi, Jawaad bai kawo komai a ransaba sai da aka sake ɗaukar tsahon sati ɗaya baiga yazo aikiba, shinefa yay bincike ya fahimci Qaseem ɗin hutu ya ɗauka akan baida lafiya zaiyi zaman ganin likita a gida. Aranar bai ƙasa a gwiwa ba ya nufi gidan Qaseem, amma sai ya iske bayanan daga bakin maigadinsa, yayi tunanin yana gidansu ne, saiya saka a bincika masa can, nanma an tabbatar masa baya nan, tunda yayma gidan yajin aiki ma bai sake waiwayensa ba. Shinefa yasa yaya Sule ya bincika masa.
         Huci mai zafi Jay ya furzar daga bakinsa yana danna ƙasan pen ɗin hannunsa da ƙarfin gaske, ya ɗan kalli yaya Sule ya ɗauke kansa daɗan duka table ɗin, “Tabbas yanzu na sake fahimtar akwai abinda suke ɓoyewa, in babu rami miya kawo maganar rami? Sun fahimci ina bibiyar Qaseem shiyyasa suka turashi can, ammafa sunyi abanza, sugama zagaye-zagayensu saina gano komai, da izinin ALLAH sai na bankaɗo komai, idan nace ina nufin komaima Sulaiman!!”. Ya ƙare maganar cikin fushi da dukan tebirin da masifar ƙarfi. Shidai Yaya Sule har sai da yaɗan rumtse ido. Jay yace, “Wace ƙasa suka kaisa?”. Yaya Sule da yay ɗan shiru alamar tunani yace, “Idan dai ban mantaba China naji”. Karan farko Jay ya saki murmushi mai ma'anoni da dama, yaɗan ɗage kafaɗarsa da taɓe baki.

★★★★★

             Da daddare bayan Jawaad ya koma gida ya samu kira daga su Uncle Nasir, saida ya kammala shirin barcinsa sannan ya nufi sashen mama Atika inda suke jiransa. Bai wani nuna mamakin ganinsuba gaba ɗaya ya gaishesu cikin girmamawa kamar yanda ya saba.
       Uncle Nasir yace, “Alhaji Ali ya kirani jiya akan ankirashi daga gidan sarki za'a kai lefenka gidansa, Jawaad kana ganin kuwa wannan hanyar daka biyo mai ɓillewace? Karfa ka manta a yanda kasa akai ɗaurin aurannan?”. Shidai Jay baice komaiba kuma bai ɗago ya kallesa ba. Cikin fushi Uncle Uwaisu yace, “Wato ga ƴan iska na magana kayi kunnen uwar shegu damu ko?” Murmushi Jawaad yayi yaɗan girgiza kansa batare daya ɗago ɗinba, yace, “Uncle to nikam mi kukeso nace, idan maganar yanda aure ta kasancene tun a wancan karon na bada amsar da duk ake buƙata, a tunanina yanzun mun wuce wannan wajen, kai lefe kuwa daga can masarauta ne sukai t

unain akai lefen can saboda koba komai ubane shi ga yarinyar shine kuma mariƙinta har a yanzun..........”
       “A wannan ganganne Jawaad, Shine mariƙinta ko kai daka ɗauketa ka maida gidan sarki saboda ka isa, karkuma a taɓa maka ƴar gwal?”. Uncle Bashir ne yay maganar a fusace. Jawaad da har yanzu yaƙi kallon kowa a cikinsu yace, “Nidai duk abinda kuke ganin na mukushi ba daidaiba akan wannan aure kuyi haƙuri ku kuma gafarceni”. Uncle Sulaiman da tun ɗazun baice komaiba yace, “Nima dai a ganina maimaita maganar baida amfani tunda abinda ya faru ya rigada ya faru, haka kuma ALLAH ya tsara dama zata kasance, kunga kenan bamu isa canja wannan ƙaddarar ba. Yanzu Jawaad ina zaka ajiye matarka? Dan bamuga kana ƙoƙarin gyara ɓangaren nakaba”. Karon farko Jay ya ɗago daɗan murmushi ya kalli Uncle Sulaiman, “Uncle ba anan zan ajiyeta ba, A.Y street zata zauna har an kammala gyaran”. Uncle Nasir yace, “A.Y kuma? Saboda karmu cinyeta anan?”. Jay da keta ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Ba haka bane Uncle...........”
              Da sauri Mama Atika ta ƙatseshi da faɗin, “Inma haka ɗinne kaidai ka sani fitsararre mai shegen taurin kai da raini, hakan dakai ni bai dameniba, dan ko kaƙi ko kaso dolene a maida aurenka da Sabira, dama shirin maka tsinannen mijin daka aura mata muke a kotu, sai gashi ya matu kuɗinmu sun huta, to wlhy kama tabbata aure kamar mun maidashi ne kai da Sabira”. Cikin fushi Jay ya kalleta zaiyi magana Uncle Sulaiman ya girgiza masa kai. Shiru yay ya maida kansa ƙasa, har sukaci jarabarsu suka tsire bai sake tankawaba, taron dai ya watse da sharaɗin sai ya maida aurensa da Shahudah.
      Shidai bai tanka musuba tunda yasan ɗan fir'auna bai mutuba.

______________________________

SAUDIA

              Gaba ɗaya wannan yinin na yau Umm-Anum ta yisane cikin yimin nasihohi da haɗamin kayan gyaran jiki da wasu littatafai masu muhimmanci kamar yanda tace, sai faifan cds da tace na kasance cikin kallonsu duk randa nake da lokaci zasumin amfani.
    Gaba ɗaya raina a ɓace yake banason tafiya, basan yanda zan musalta muku yanda nakejinta a rainaba, tunda tafiyarnan ta gabato har kuka nakeyi idan na tuna zan tafi, baƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninmu ba a kwanaki sha biyun nan, kodan ta jani jikintane oho.

       A ɓangaren Umm-Anum ma dai cike take da damuwa, haka kawai takejin batason Bilkisu ta tafi, yinin yau komanta sukuku zaka gansa, da daddare tare suka dawo gida da bilkisu, anan zata kwana yau gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce ita da Aunty Mahfuzah da Anum sai Anuwar daya dage shima zaije, da farko Umm-Anum catai bazaijeba, sai da Abie yasa baki sannan da ƙyar ta amince, dan haka kawai takeji batason suje da ga shi har Anum ɗin.
     Abie bai taɓa ganin bilkisu ba sai yau bayan sun dawo, itama kuma yauɗin ta taɓa ganinsa, amma yanda ya karɓeta abin har mamaki ya bata, shikansa mamakin yanda yarinyar ta shiga ransa yakeyi, sannan badan kar ace yay ƙaryaba wasu abubuwa nata suna ɗan masa kama dana Umm-Anum ɗin, musamman tafiya da dai wasu ƙananun abubuwa da saika nutsu sosai kake fahimtarsu.
      Sai da su Bilkisu suka shige suka kwanta sannan ya fuskanci matarsa, dan yanda take komai rai ɓace ne ya sakashi jinsa shima a damuwa. cike da kulawa yake tambayarta mike damunta?.  Hawayen da taketa riƙewane suka zubo mata. Sake rikicewa yay ya jawota jikinsa, dan yanason wannan baiwar ALLAH shidai a rayuwarsa, dukda ba ita kaɗaice matarsaba kuwa, amma yanda take ƙyautata masa yasa tazama tauraruwa a garesa. Yanda yaketa jero mata tambaya wata kan watane ya sakata sakin murmushin ƙarfin hali, idonta a kansa tace, “Bafa komai baneba, yarinyarnan banason ta tafi wlhy, jinta nake cikin jinina fiye da yanda kake zato, ina mata ƙauna maiban mamaki har a ƙarƙashin zuciya, sannan sunanta duk sanda na ambacesa ko wani ya ambata sai naji matsananciyar faɗuwar gaba, bansan miya saba”. Abie dai kallonta ya keyi cike da nazari, sai da tagama ya sauke ajiyar zuciya tare da sake rungumeta, maganganunta na buƙatar ayi musu zama na musamman domin yin nazari, amma duk da haka bara ya gwadata ya gani, ko lokacin da suke fata

ne yazo. “To kodai zamu shirya muma muje bikin nata ne?”. da sauri Umm-Anum ta tashi daga jikin mijin nata tana girgiza kanta, fuskarta harta nuna ɓacin rai, tace, “Babu inda zani Annur, badanma ka takuraba kosu Anum bazasu jeba”. Da kallo shidai kawai yake binta, amma baice komaiba, baikuma sake cewa uffanba game da tafiyar har gari ya waye su Bilkisu suka tashi da shiri.

★★★★
Chapter 85 · 0% Book details