← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 168

Sashe 132

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

       Duk yanda muka tsara hakance ta kasance, bayan sallar la'asar muka isa gidan Alhaji kokino, cikin shiri nake irin na ainahin garorin yaran nan na ƙauye da ko karatu basu taɓa samu ba, ga matarsa kam mun samu tarbar mutuntawa, ƴaƴan gidanne dai sai a hankali, dan gaba ɗaya halayensu baimin ba, sai wani famar min kallon banza suke, musamman mai son boss ɗin nan. Shiru nai na maƙure jikin kuje alamar tsorata ta baƙunta. Baba mai gadi da suka gama gaisawa da hajiya ya juyo ya kalleni, “K Larai! Baki iya gaisuwa bane? nifa banason wannan ɗabi'ar banzar kin sani”. Muryata na rawa nace, “Ina wuni hajiya, mun sameku lahiya?”. Dariya yaran suka bushe da ita duka falon, irin wai ƙauyancina ne ya basu dariyar. Ita dai hajiyar Murmushi tayi tana cigaba da kallona, tace, “Lafiya lau Larai, yasu mamar taku?”. “Lahiya lumi suke aradu hajiya, tace tana gaiheki”. Saboda dariya har ƙasa suke faɗuwa daga saman kujerun. A raina nace, ‘Wawaye kawai’.
      Baba ne da yake ɗan murmushi shima yace, “Hajiya dama tazo daga ƙauye ne can anguwar tudun birji wajen ƴar uwar mahaifiyarta, to saita iske wai sunje suna ko ina, kuma sai jibi zasu dawo, shine nace data koma kuma ai wahala goma da ashirin tazo nan saita kwana idan suka dawo sai taje, ALLAH yasa dai ban wuce gona da iriba?”. “A'a Malam baka wuceba kam, ai kaga anyi zuminci tunda dama kaƙi kawo mana iyalanka shekara da shekaru, ni nagode sosai da wannan ziyara”. “Nima nagode hajiya, bara na koma bakin aiki to ga tanan”.
      Ganin zai fita nai ƙwalƙwal da idanuna alamar kuka, “Kaka anan zaka barni?”. Juyowa yay da ɗan faɗa yana min daƙƙuwa, “Kinci gidanku Larai, nanɗin cin mutane ake bare kice za'a cinyeki? To idan hakan bai mikiba tashi ki kama hanyar ƙauye idan su Rakkiyar sun dawo sai ki dawo”. Baki na tura ina maƙe kafaɗa, “Ni alkur'an a'a”. “Ke kuma kika sani ja'ira kawai” ya faɗa yana ƙarasa ficewarsa. Yana fita suka fara jana da hira wai na basu labarin garinmu, nasan sosuke kawai su ringajin yanda nake magana suna dariya. Abinci aka kawomin, inaci ina basu labari kamar wata sakara, suko sai kwasar dariya sukeyi da zagina a kaikaice.

              Haka na maida kaina ƴar cali-calin ƙarfi da yaji a gidan Alhaji kokino, sannan aiki duk dana gani zan tashi nayi kamar bansan ciwon kaina ba, bansan inajin kewar mijina ba sai da dare yayi nazo zan kwanta a tabarmar ɗakin masu aiki, hakan bai dameni ba, dan wannan ba sabo bane a gareni, kewar tasace dai kawai naji, sai tunani nake yanzu koshi mi yakeyi? Oho.

★★★★

         Yanda Bily ke cikin kewa a gidan Alhaji kokino haka Jawaad yake a gidansa, tun da ya dawo daga wajen aiki duk sai yaga gidan yay masa wani faɗi da baƙi, yay zaune a babban falo yanata kallon sashenta, da ƙyar ya iya tashi yaje yay salla, koda ya dawo yaga zuciyarsa na ƙara ƙuntata sai ya fice daga gidan zuwa gidansu A

mina, baisan yawan zuwa gidan dan kar a fahimci akwai wani abu duk da yasan Dad baya a garin, sannan ma ƴan gidan hankalinsu baya aƙwance saboda rashin ganin Shahudah, shiko akan hakan yamaƙi zuwa ko family house ɗinsu tunda suka dawo, ya kuma kashe wayar da kowa zai iya samunsa.
     A gidan su Amina ya ɗan rage kewa,  maman yara tace ya kwantar da hankalinsa tanaji a ranta insha ALLAH bilkisu zata iya, dan a zuwan da sukayi jiya ta fahimci tana da hankali da wayo. Kai kawai Jawaad shi dai ya ɗaga, zuwa tara ya baro gidan, rasa mizaiyi yayi, haka dai ya koma gidan ransa duk a jagule. Tea kawai yasha yay shirin barci ya kwanta a ɗakinta, jin zuciyarsa ta sake ƙuntata ya ɗauki waya akan bara ya kirata ko muryarta yaji, sai da yaji switch up sannan ya tuna cewar bama ta tafi da waya ba. Tsaki ya buga yana jefar da wayar a kan gadon, waishi mima yasa ya barta taje ne?. haka yayta takaicinsa hardai daga ƙarshe ya sake ɗaukar wayar, Anuwar ya kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka cike da ɗoki. Wannan kiran Anuwar shine ya rage masa kewar Bilkisu a ransa, sunsha hira sosai dai sai kusan ɗaya da rabi na dare sukai sallama, sai kawai yayo alwala ya hau salloli ma. Sai kusan uku ya kwanta sai barci.

WASHE GARI

        Washe gari ma haka na tashi cikin ƴan aikin nan duk abinda sukeyi dani akayisa, babu wanda yace nabari a gidan, saima faɗa suke wai nafi masu aikin iya aiki. Nidai bance komaiba, sai lokacin da hajiya ke faɗa akan mai gyara mata ɗaki batayi da ƙyau ba, idan bazata iyaba a canja da wata. Murmushi nayi domin wata damace ni a gareni hakan, dan haka nai caraf nace ni bara na gyara mata yau. “A'a Larai, daga zuwa sai kita aiki? Aiba haka akeyiba”. “Lah hajiya karki damu, yo mufa mun saba alkur'an, dafa a ƙauyene da yanzu inacan ina sirhe, yo ni ina zan iya da wanga lalaci naku na mutan burni hajiya, ke dai bani aiki kiga aikin mata aradun ALLAH yanzu na ƙalƙale miki ɗaki ko fadar mai garin garinmu bata nuna masa fita ba”. Sunata dariyarsu niko na fuske abuna.
       Zagewa nai naima ɗakin gyara na sosai, sai gashi hajiya na santi ita da yaran nata, aiko ranar na aikatu, dan ɗakunansu sukaita sakani na gyara musu suma yaran, duk da na gaji haka na daure dan fatana nidai a ƙarshe a turani ɗakin mai gidan, amma sai naji tsit. Washe gari babu wanda ya sakani wani aiki, har yamma, abin duk ya dameni inata addu'a da fatan samun hanyar da zan shiga ɗakin, dan a yinin da nai jiya na aiki nazarin gidan naitayi da hanyoyin cikinsa. Kusan ƙarfe huɗu da rabi ina zaune a can baya ni da ɗaya daga masu aikin gidan sai ga hajiya ta fito, sannu duk mukai mata da gaisheta dan duk yau ban gantaba bata yini a gida ba. Tace, “Larai Please zoki min wani ɗan aiki nan na dawo a makare”. “To” nace ina miƙewa, wani irin farin ciki ya kamani ganin mun nufi sama, inda nake da tabbacin turakar mai gidance anan. Fasalta muku yanda tsarin yakema ɓata lokacine, kowa ta ƙiyasta tsaruwarsa kawai. Kallona tai tana ɗan murmushi, “Larai nan zaki gyaramin, babu wata mai aiki dake shigowa ni nake gyarawa, to naje saloon da gyaran jiki sai yanzu na dawo gashi lokaci ya ƙure, kuma Alhaji nanda takwas na dare zai iso yayi tafiyane, na yarda da kene saboda kinada nutsuwa, dan ALLAH ki gyara komai ƙal kinji, ni kuma zanje mu ɗaura masa abinci”.
       Farin cikin da ke cin raina na danne, na amsa mata da “Insha ALLAH hajiya zaki samu fiye da yanda kikeso” “Yauwa ƴar albarka nakuwa gode, bara na turo miki Laila ta tayaki. Ɗaf ɗokina ya gudu, kamar zanyi magana sai kuma nai shiru harta fice. aikin na fara ina tunanin yanda abin zai kasance, dan insha ALLAHU bazan fita daga ɗakin nanba yau sai da abun nan.
     Laila ɗaya daga cikin yaran gidan ta shigo ko sallama babu, bataimin magana ba ta nema waje ta kwanta a cikin kujera tana danna waya, nima bance da ita komaiba na cigaba da aikin, tsaf na kammala falon na saka fresheners dana gani da turaren wuta, sannan na nufi bedroom ɗin. Ƙaton gaske ne shima kuma ya haɗu, sai dai gadon irin gajere ɗin nanne wanda babu yanda za'ai ka iya leƙa ƙarƙashin gado balle harka jawo abu. Wucewa nai toilet ina ƙullawa da kwancewa a raina
Chapter 132 · 0% Book details