← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 168

Sashe 144

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Cikin mintuna ƙalilan suka iso station ɗin bisa taimakon Sadiq, sai dai kuma securitys sun hanasu shigowa musamman ganin yanayin baba ƙauran, sun musu roƙon duniya amma sun hanasu, Sadiq ya kira wayar Jay amma bai ɗagaba, hakan yasa suka koma gefe cike da damuwa, musamman ma baba ƙaura dake matuƙar matse da son ganin Jay.
      Suna a wajen tsaye su biyu Sadiq na cigaba da kiran Number Jay sai ga motar su Aliyu, harma an buɗe musu gate zasu shige Aliyun ya hango baba ƙaura ta mirror. Sauke gilashin motar yay ya saka ɗaya daga cikin securitys ɗin yay masa magana da baba ƙaura. Ganin shi ɗinne dai kamar yanda yay hasashe sai ya bada umarnin barinsu su shigo. Bayan ya shige da motar ya samu waje yay fakin ya fito shi da waɗanda sukabi masu ƙwamushe Alhaji babba, gaisuwa kawai yay da baba ƙauran ya shiga ya sanarma Jay.

          Duk da Aliyu ya sanar masa baba ƙaura ne hakan nbai hanashi yin mamakin ganinsa har station ɗinsu ba, ya ƙarasa fuskarsa babu walwala, dan duk yanda yaso aro fara'a ya azama fuskar tasa kamar yanda ya saba idan yaje wajen baba ƙaura hakan ya gagara. Cike da girmamawa suka gaishesa har Sir Ahmad.
          Kallonsu baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana faɗin, “Kagani har a wajen aikinka ko?”.
         Ɗan murmushi Jay yayi da cewa, “Babu komai baba, ai nasan zuwan naka mai muhimmanci ne”. “Hakane” baban ya faɗa yana sake maido hankalinsa garesu sosai. Yace, “Tun da safe na saka a nemomin kai amma hakan ya gagara, ba'a samunka da farko, daga baya kuma ta shiga ba'a ɗagawa”. Kai Jawaad ya dafe, “Dan ALLAH kayi haƙuri baba, wlhy na tsinci kainane a yanayin da komaima bazan iyaba”. “Gudun faruwar hakanne ya sakani yimaka neman gaggawa ai daman,  tun bayan wucewarka na tafi jeji ne, acan ma na kwana, dan sai gabannin asubahi na shigo gari, sanda na iso nan har an shiga salla. Na saka a nema min kaine domin isar maka da saƙon abinda idona ya ganomin jiya a cikin jajin nan. Muhammad Jawaad lallai akwai matsala babba dake tunkaroku, da idona na gani, na kumaji da kunnena, gashi rashin samunka akan lokaci ya nunamin alamomin fara faruwar matsalar dana guda ma a yanzun”.
         Hankalin Jawaad a tashe yace, “Baba hasashenka duk haka yake, yanzu haka zancen da nake maka anje har gida an ɗauke kakana, akan binciken inda zamu samesa muke”.
             “Wannan shine shirinsu na farko dama. Na zauna nayi ƙyaƙyƙyawan nazari mutanen nan ba haka nan suke bibiyarka ba, akwai wani abu aƙasa wanda akwai jininka a ciki, ina nufin cikin zuri'arku akwai wanda ke tare da mutanen nan.....” cike da mamaki Sir Ahmad da Jay suke kallon baba ƙaura. Ya jinjina kansa yana cigaba da faɗin, “Kar kuyi mamaki, neman duniya babu wanda baya ɓatarwa, lallai kamar yanda na faɗa akwai wani abu a ƙasa, dan babu rami miya kawo rami? Bayan abubuwan dana sani ke a hannunku akwai wani abu da kuka ɗakko a wani gida ne?”. Sir Ahmad ya kalli Jay, shima ya kalleshi, sai kuma ya maida dubansa ga baban yana jinjina masa kai. “Akwai wani tukunya baba, wanda.........” ya labartama baba ƙaura da Sir Ahmad komai.
        Baba ƙaura da keta faman jinjina kai cike da nazarin maganganun Jawaad ya sauke nannauyan numfashi. “UBANGIJI ya baku kariya sosai to akan wannan aikin, dan suna cikin ruɗani mai girma akan son gano wanda ya ɗauki tukunyarnan, amma sun gaza gano komai, inuwar wadda ta ɗauka ɗin kawai suke iya gani, sannan har yanzu tsafin nasu kuma bai iya nuna musu mahaifiyarka ta shigo ƙasarnan ba. Wannan hikima ce da rahama daga UBANGIJI, inaga iyakar suce tazo shiyyasa komai

ya keta ƙwace musu. A taron da sukai daren jiya sun tattauna abubuwa da dama wanda zarge-zarge da yawa sun sami rinjaye a kai kanka, sai dai a yanda na fahimta na yau sai sun fisu muhimmanci. Dan haka nakeso ku kasance a wajen kai da matarka idan zai yuwu, sannan lallai matsayinku na jami'an tsaro wannan shaiɗancin ya kamata ma ace ku kawo iyakarsa ma baki ɗaya. Dan tabbas kakanka yana tare da su, acanne kawai zaku iya samosa a halin yanzun dama wasu mutanen da aka kai a wajen bisa zalunci da son zuciya”.
        Boss ya cika bakinsa da iska ya furzar yana taunar lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi. Kallon Sir Ahmad dake fahimtar dukan maganganun nasu a baibai yayi. sai kuma ya maida ga baba ƙaura yana faɗin “Babu damuwa baba, amma kana ganin ita zuwa da ita bazai zama haɗari ba?”. Ƴar dariya baba ƙaura yay yana kallon Bilkisu data fito da waya a hannu ta doso su, “Babu wani haɗari insha ALLAHU, matar nan taka akwai sirrika tattare da ita waɗanda ALLAH kaɗai yasan tushensu, amma haka kawai nakeji a raina kamar sunada nasaba da taka ƙaddarar. Amma ita ɗin ba jami'ar tsaro bace?”. “Eh jami'ar tsaroce, irin aikinsu ɗaya”. Sir Ahmad ya bama Baba ƙaura amsarsa. Baba ƙaura ya sake faɗaɗa murmushinsa “Ka barta itama ta nuna bajintarta a aikinta da ƙwazon da ALLAH ya bata, ALLAH yana tare daku a dukkan al'amuranku insha ALLAHU. kudai kuci gaba da gayama ALLAH”. A tare suka jinjina masa kawunansu da faɗin insha ALLAHU baba. “Karkuji komai, wannan tafiyar tafi ta farko sauƙi insha ALLAHU, ta wani ɓangaren kuma tafi waccan haɗari, dan haka runduna zaku haɗa mata da tafi ta farko indai aikin zakuyi da gaske” ya ƙare maganar dai-dai da isowar Bilkisu wajen.
       Rissinawa nai na gaida baba ƙaura da banyi tunanin ganiba anan, ya amsamin cike da fara'a da kulawa. Cikin girmamawa na miƙama Sir Ahmad takardar hannuna da aka aikoni na kawo masa. Amsa yay yana dubawa, ni kuma na maida dubana ga boss da yanayinsa ya bani tsoro. Da ido nai masa alamar ‘Lafiya?’. Kansa yaɗan girgizamin kaɗan yana lumshe idanunsa dake jajur.......
     Sir Ahmad ne ya katse mu da faɗin, “Jay inaga yanzu haɗa rundunar da zamu tunkaru jejin ne ya dace, bara na nema mana jirage masu saukar angulu yanzun nan, sai ku haɗa kayan operation ko”. “Okay Sir” Jay ya faɗa cike da karsashi na jami'i mai cikakkiyar lafiya da zafin nama..
     Tare muka koma da baba ƙaura office ɗinsa inda su Jabeer keta aiki cike da zafin nama da ƙwarewa. Boss ya ɗan bigi tebir da zafi-zafi yana faɗin, “Ayi shirin fita operation mun gano inda suke insha ALLAHU”. Duk juyowa sukai suna kallonsa da mamaki, harni kaina kallon nasa nake, amma sai ya ɗauke kai yana nufar telephone ɗin dake saman table ɗinsa yana jero sunayen waɗanda za'a kira yanzun nan”.
        Cike da bin umarni Aliyu ya fice zuwa office ɗinsa domin aiwatar da komai, shima bayan yayi waya da wani da bansan ko wanene ba ya ajiye yana kallona da nufar ƙofa yace na biyosa ni da Dawood da suka dawo da Oga Aliyu yanzun.
        Store ɗin station ɗin muka nufa, inda acan muka iske Sir Ahmad da wani ogan mu shima suna haɗa bindugu. Muma aikin haɗa wasu makaman aka sakamuyi. Mamaki ya kuma cika zuciyata, duk yanda nake hasashen al'amarin da alama ya wuce nan, nasan Boss mutum ne mai muhimmanci a hukumarnan tamu, ya cancanci a nuna masa kowanne irin halacci akan taɓa ahalinsa, amma yanda ake shirin fita operation ɗin sai nakeji a raina kamar ya zarce na maido kakansa kawai. Cikin mintunan da bazasu gaza talatin ba duk wani shiri an kammalashi, duk jami'in da aka buƙaci gani ya amsa kira, a mamakina harda su Ummie su dukansu, Rose harma dasu Ada, sai sauran jami'ai na departments ɗin da ba namuba ma. Dukanmu mun kasance cikin Uniform ɗin aiki, dan boss ma da yake sanye da kayan gida a da sai gashi ya fito cikin Uniform harsu oga Jabeer da Sir Ahmad ɗin kansa. An bamu bullet proof jacket duk mun sassaka, kafin oga Hafiz ya rarraba mana bindugu harda kibiya ga waɗanda suka samu horo na musamman a kanta, wasu kuma wuƙaƙe naga an basu manyan takubba, sosai mamaki abin yayta bamu mu baƙin shigowa hukumar, dan zan iya cewa wannan shine operation na

farko gagarumi da za'a fita damu..............✍

Da ace zan iya sai nabi wasunku da bulala goma-goma a ɗuwawu aradu🙄, wlhy nafiku son naga na kammala buk ɗin nan🤦🏻. Uzirin daya riskeni ya wuce dukan tunanin mai hasashe, yanzunma dauriyace kawai dason ganin na faranta muku, saɓanin wasunku da Umar o bakunansu ke furta abinda bai daceba a gareni😢🚶🏻.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
[2/6, 11:41 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: ƘWAI CIKIN ƘAYA

BILYN ABDULL

*_FARIN WATA SHA KALLO🤓🤗_*

ZAFAFANKU SUN DAWO GAREKU A 2021😋😋😋😋🚴🏼🚴🏼

*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥🔥🔥
*_SABUWAR SHEKARA_*
*_TAREDA SABON SALO_*👍

✔️ *_A DUNIYAR RUBUTUN HAUSA SU NA DABAN NE,_*
✔️ *_A DUNIYAR NISHADANTUWA DA KARATUN HAUSA SU DIN NA MUSAMMAN NE,_*
✔️ *_A DUNIYAR FADAKARWA DA QAYATARWA NA KARATU SU DIN NA FARKO NE,_*
✔️ *_A 'BANGAREN NISHADANTUWA DA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA MAI SHIGA RAI DA SANYA SHAUQI DA NUTSUWA TO SU DIN ZA'BABBINE,_*
✔️ *_A 'BANGAREN SANYA NISHADI DA BARKWANCI TO SU DIN QWARARRINE,_*

*_Shin ko kunsan su ake kira da zafafa biyar masu tashe?_*
_*Idan kin/ka san kai maabocin karatun littafan HAUSA ne to tabbas karku Bari ayi Babu ku*_
*_domin kuwa wannan karon sun dawo muku da wani sabon salon Wanda babusa a DUNIYAR karatu,_*
*_cikinsu Babu wadda bataga jiyaba bataga yauba a fagen nishadantarwa._*

*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*YANKAN BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Chapter 144 · 0% Book details