← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 168

Sashe 123

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

buɗe da kaina. Na ƙara ɗan wawwaigawa na kalli ko ina, station ɗin tsit kamar babu kowa a ciki.
       Shima kansa kallon ko ina yake da mamaki, amma baice komaiba, ganin bai amsa jikkarsa ba nasan so ya ke saina kai har office ɗinsa kenan? Tare muka jera, baya bari ya tseremin da ko step ɗaya. Shine ya buɗe ƙofar, muna shiga kawai sai mukaji abu kanmu ana mana wanka da shi. Saurin ƙoƙarin fara share fuskkokinmu mukayi, amma abin yaƙi daina zubowa, sai ma ihun ma'aikatanmu da tafi daya karaɗe wajen. A sannan ne abun ya daina zubowa, muka share na fuskarmu sannan muka kalli juna kafin mu maida ga kallansu. A take kunya ta kamani kuma, dan gaba ɗayansu sukayo mana caa a ka da kalmar “Muna tayaku murnar aure!”.
      Murmushi Jawaad ya daure ya saki duk da iya fuskarsa ne, kafin ya maida dubansa ga Bilkisu datai ƙas da kanta, ya kamo hannunta cikin nasa yana faɗin, “Mun gode sosai, ALLAH yabar zuminci”. Ya ƙare maganar da kai hannun Bilkisu saitin bakinsa ya  sumbata. tafi aka sakeyi, sannan kowa ya nufosu da ƙyautar dake hannunsa, tun jay na amsa har hannunsa ya cika bilkisu ma ta fara amsa, jabeer ne ya matso ya taimaka musu aka tarasu waje guda ya sake musu godiya itama bilkisu tai musu ranta fal mamaki.
        Gaban ƙaton cake ɗin da akai da hotonsu aka jasu, daga bilkisu har jawaad ɗin dai murmushine shinfiɗe a fuskarsu, bazaka taɓa gane sunada damuwa ba, bily ta fara ɗaura hannun ta saman wuƙar kafin Jay ya ɗaura nasa saman nata suka yanka. Ita ta fara cirar ɗan guntu ta saka masa a baki, yay mata murmushi mai sanyi ya ciro kaɗan itama ya saka mata yana jawota jikinsa ya rungume, saboda ganin yanda Rose take musu wani irin mugun kallo mai cike da tsana da takaici yay hakan, da farko baiyi niyyar bama Bilkisu cake ɗinba, amma saboda Rose yayi dan yana lure da ita ko kalma ɗaya bata togaba na tayasu murna, hakama wasu daga cikin matan gurin sai baƙin rai suke da bankama bilkisu harara..
     Nanma tafin akayi, kafin Sir Ahmad ya farayin jawabin taya murna a garesu kasancewarsa head of department nasu, daga nan sauranma suka sake tayasu murna da fatan alkairi da bama Jay hannu suna musabaha, matan kuwa Bilkisu suke bama hannu itama suna mata, shikam Jay sai dai su ɗaga masa dan sunsan ƙa'idarsa ce baya hannu da mace ko wacece ita a station ɗin nan ko tana a gaba da shi kuwa sai dai a kuskure. Suma mazan duk da Bilkisu na ƙasansu hakan bai hanasu mata murna ba, tanata amsawa a kunyace dan wasuma ko magana ita bai taɓa haɗata da suba sai yau.
          Sai da aka gama ɗan kace nace sannan suka wuce office ɗinsa, ƙyaututtukan da suka samu kuwa tuni Jabeer ya saka an kaisu ciki dama.
              Jikkarsa na ajiye masa saman table ɗinsa na ɗan kallesa, ganin hankalinsa nakan files ɗin saman table ɗin ya ɗauki ɗaya yana dubawa saina ce “Sai anjima” kawai na juya zan fita. Caraf naji an riƙoni, kafinma na juyo ya maidoni baya ya jingina da table ɗin, kallonsa nai da mamaki, ya ɗan harareni batare da yace komaiba naji saukar laɓɓansa kawai saman nawa babu zato.
       Idanuna na lumshe kawai ban masa wani musuba ko sau ɗaya, dan inhar zai huce ta hakan to Alhmdllh, rabonsa dako kissing ɗina tun randa mukaje Saudia. Ganin da gaske yake sai kawai na shiga bashi gunmawa, nidai fatana ya samu nutsuwa wannan fushin da fusatar dana gani tattare dashi ya gushe. Burrum aka turo ƙofa babu ko neman izini, ƙoƙarin janye kaina nayi amma ya hanani kowacce dama, saima sake turani jikinsa yayi sosai da sake sauya salon sumbatar, ƙamshin turaren rose da naji ya sakani nima canja salo dan ta bani haushi ɗazun, dan batamin magana ba sam, nakuma gaisheta taƙi amsamin. Jin ta fita da gudu tana kuka ya janye kansa da ƙyar yana jan tsaki da harar ƙofar. Kallonsa ya maido gareni yana hararata, hakan ya sakani sakin murmushi dan harga ALLAH dariya ya bani, to ni miye laifina kuma?.
      Kaina ya dunguremin da faɗin, “Idan kika cigaba da wannan noƙe-noƙen da sanyi saita cigaba da raina miki ai, ki kwana da shirin cewar ke matar Jay ce a station ɗin nan yanzun ba budurwarsa ba”. Ya ƙare maganar a hankali cikin kunnene kamar mai raɗa. Lumshe idanun

a nayi ina murmushi, bance komaiba na ɗauka jikkata nasa a kafaɗa sannan na kallesa, shima kallona yake, murmushi na sake sakar masa da ɗaga masa yatsun hannuna biyu alamar bye-bye. Kafin ya samu damar cewa wani abu harna fice abina daga office ɗin.
          A jikin ƙarfen lifter na iske Rose tsaye sai cika take da batsewa, kallo ɗaya nai mata na ɗauke kaina, “K!!” ta faɗa a daƙile, banza nai mata tamkar banjiba na haye lifter ɗin abuna, wani tsalle tayi zata cakumoni naji muryarsa a bazata kanmu, “Koda kuskure karki sake wlhy hannunki ya taɓamin mata”. Ya faɗa a kausashe. Murmushi nayi da ɗage masa gira na ɗauke kaina, banajin amsar da take bashi dan nayi nisa da su, ina sauka kuma na sake ɗaga masa yatsun hannuna, shima ɗagomin yay, nai gaba abina na barsu bansan yaya suka kwashe ba.

        Bily na ɓacema ganinsa ya juya office batare da ya sake ko kallon inda rose take ba, ta cika tayi fam da baƙin ciki tamkar zatai bindiga a wajen. Ganin zai shige sai tabi bayansa a guje. Tana shiga office ɗin yana zama a kujerarsa, tsabar wulaƙanci sai yay kamar baisan ta shigo ba ya fara ƙoƙarin haɗa Computer ɗin saman table ɗinsa.
     Kuka maicin rai Rose ta fashe da shi tana dafe tebirin da hannu biyu, “Boss! Ni zaka wulaƙanta akan yarinyar da tazo station ɗin nan jiya-jiya? Ni zakaci amana ka yaudara saboda waccan ƴar tatsitsiyar yarinyar da bata wuce ɗiyar cikinka ba?, ko kunya bakaji kake iya nuna ƙaramar yarinya matsayin matarka wai?”.
          Jawaad ya ɗan lumshe ido yana buɗewa akan Computer ɗin da ya kunna, jikkarsa da bily ta ajiye masa ya ɗauka ya buɗe batare da yama rose ko kallo ɗaya bama balle tai tunanin samun amsa.
       Rose dake binsa da kallo ta sake fashewa da kuka tana faɗin, “Yanzu nan boss ina maka magana kana sakemin wani wulaƙancin?”. Sake yimata banza yay yama fara aikin gabansa. A wannan yanayin su Jabeer suka shigo office ɗin dan sunyi knocking har kusan uku yanaji ya share, shigowar tasuma baisa ya ɗago ya kallesu ɗin ba, su dai suka zauna a kujerun gaban tebirin suna kallonsa suna kallon Rose dake kuka. Hafiz ya jawo kujerar dake can gefe shima ya zauna yana jan ƙaramin tsaki dan shifa Rose takaici take bashi da halintan nan.
         Ganin yamaƙi kallonsu Jabeer yace, “Boss wai mike faruwa ne?”. Bai tankaba bai kuma kallesun ba yanzuma, dama cikin damuwa yake, ya fito gida da fushi, ita kuma yanzu sake kunna zuciyarsa take tana cikowa saman ƙirji, idan kuma har ta bari takai masa wuya to lallai zatayi nadamar biyosa office ɗinsa tana masa ihu a kai.
       Jabeer zai sake magana Aliyu ya girgiza masa kai alamar kar yayi, Rose ɗin ya kalla da take kallon Jay tamkar zata haɗiyesa, kuma har yanzu kukan take, “Rose miya faru?”. Juyawa tai ta kalli Aliyu hawaye na sake ziraro mata, “Aliy na gaji wlhy, na gaji da wulaƙancin da boss yake min, dan na soshi shine ya zama laifi? Shekara nawa na ɗauka tare da ku, kuma ban gazaba wajen nuna masa ina sonsa tun yana tare da wancan matar tasa, ya cemin shi bashi da ra'ayin yin mace fiye da ɗaya, karka manta har suspension yasa aka bani lokacin da matsalarnan taku ta faru, saboda ina sonshi na haƙura na mance da komai kamar bai faruba, yazo suka rabu da matansa muka tafi U.S ɗin nan, babu roƙon da ban masaba muyi aure a lokacin tunda dai ai baida mata, amma ya dinga shareni da zancen har muka dawo, yanzu duk ƙoƙarin nan da nai masa bai ganiba sai daga ƙarshe ya auri wannan yarinyar da tazo jiya-jiya cikinmu, bakuga yanda ya yarfani a gabanta ba yanzun, mi take da shi da har zai wulaƙantani a kanta?”.
       Kasa magana duk sukai, dan wannan faɗan kam dai yafi ƙarfinsu, duk da sunsan komai, amma ita rose banda haukarta ai ba lallaine ka SO a SOKA ba ko? Su shaida ne boss bai taɓa cewa yana sonta ba, sannan bai taɓa wulaƙantata ba. Hafiz ya taɓe baki cikin takaici yace, “Ikon ALLAH, so kike ya wulaƙanta matarsa a kanki kenan komi? Mtsoww! Lallai aiki ya sameki, kuka kuwa yanzu kika fara s.....” hannunsa Aliyu ya riƙe da sauri yana murmushi, yasan hafiz da iya yaɓowa mutum zafafan magana, yanzu sai ya sake birkitata. Duk da hakan kuwa sai da Rose ta hayayyaƙo ma

Hafiz akan dama ta lura ita tuni ya tsaneta.
       Da sauri Jay ya bugi tebirinsa, cikin tsananin ɓacin rai ya nuna mata ƙofa yana faɗin, “Rose fitarmin a office!!”. Rose ta nuna kanta tana faɗin, “boss ni ka.......” cikin ƙaraji ya katseta ta hanyar sake doka tebir ɗin, “Nace! Ki fitarmin daga Office”. Yanda taga idanunsa sun masifar kaɗawa ya sakata firgita, tasan shi tasan shiɗin wanene idan yay fushi, ta kuma san abinda zai iya aikatawa bayan hakan, ta kalli su Jabeer ta sake kallonsa.
     Tashi Jabeer yay ya kama hannunta ya fitar da ita dan ya tabbata wlhy idan har ta sake wasu mintuna bata fitaba komai yazo masa rai zai aikata mata, sai da ya kaita har waje sannan yace, “Rose miyasa kikai haka? Kinfa san wanene boss?”. Zatai magana yace, “Kinga kije zanzo na sameki muyi magana, amma Please ki daina masa haka babu ƙyau, wlhy na tabbatar yana ɗaga miki ƙafane darajar kina cikinmu, kinsan fa yana gaba dake, sannan boss bayason raini, kije zanzo ni da Aliyu mu sameki”.
     Badan taso ba ta tafi tana sharar hawaye da kissima irin tashin hankalin da zata saka Bilkisu a station ɗin nan.

(🤔Rose mi kike ƙullawa kuma?).

★★★★★★★
Chapter 123 · 0% Book details