← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 168

Sashe 11

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“Mom kinga abinda Bb ya kemin kuwa? Bayan ya kamata ace ya nuna zalamarsa da kewata na shekarun da muka kwashe bama tare”.
“Huhm” Mom ta faɗa tana shafa kan Shahudah dake saman cinyarta, dan kuwa suna cikin bedroom ɗin Mama Atika ne ita da Shahudahn kawai, dan ta fahimci ɗiyar tata na tare da damuwa, yau tunda sukazo gidan ta shigo ɗakin Mama Atika bata sake fitaba, shiyyasa ta biyota, sai ta isketa cikin damuwa, hakanne ya sakata zama ta dora kan Shahudah a cinyarta tana shafawa, itakuma take bata labarin ruɗanin data shiga akan tarbar data samu daga wanda batai tsammaniba daga Bb ɗinta (Jawaad).
Mom ta haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi tana sake yamutsa sumar Shahudah'n, “Kar taurin kan yaron nan ya ɗaga hankalinki fiye da haka Shahudah, ki barsa, ni da kaina zan sauke masa wutar dake ci a kansa, bara dai a gama hidimar rasuwarnan kinji”.
Kai Shahudah ta ɗaga mata cike da shagwaɓa, har ƙwalla na sakko mata a kan kumatu tace, “Amma Mom wane mataki zaki ɗauka to?”..
Mom ta share mata hawaye tana murmushi, “Karki damu Shahudah zaki gani, kedai sonake kicigaba da kwantarmin da hankalinki, nan kusa kaɗan zaki dawo ɗakin mijinki”.
Kai Shahudah ta ɗaga mata tana murmushi da rungume mom. Murmushi mom tayi taci gaba da lallashinta cikin so da ƙauna.
Nikam nace, “Mai uwa a gindin murhu baya cin tuwonsa gaya ai Shahudah😋😜🤸🏼.
..::..★__________★..::..
BILKEESU
____★..::..★__________★..::..★____
Kwanaki huɗu cir bana zuwa Office ina gida ina jiyyar hannuna, yayinda kullum Ummie ke tare dani, ƴan gidanmu kuwa basa yini suna gidan rasuwa, barci kawai ke kawosu gidan. A kwana na biyar nai shirin komawa aiki, dan naji sauƙi sosai, a kuma daren ranarne Yah Qaseem ya dawo, nayi farin cikin dawowar tasa, dan nikaina nasan idan nace banason Yah Qaseem na yaudari kaina, a ƴan kwanakinan da bayanan sosai nayi kewarsa.
Tun a daren yake jeramin tambayoyi akan hannuna, bai samu amsa ko ɗaya ba daga gareni sai murmushi kawai.
Koda muka tashi da safe ma dai bai fasa sonjin musabbabin ciwonba, da naga ya damu sai kawai nace masa tsautsayine ya gitta mani a wajen aiki, badan ya yardaba ya ƙyaleni kawai, kasancewar yau zan koma aiki nima sai na bisa muka tafi tare kamar yanda muka saba kafin yay tafiyar.
Yah Qaseem na gama daidaita fakin motarsa wani jami'inmu na isowa wajen, ya isarmin da saƙon kira daga office ɗin B.G, maganar da jami'in yazo da itane ya sakamu kallon juna ni da yah Qaseem ɗin.
Idanuna na janye daga cikin na Yah Qaseem daya tsatstsareni da kallon tuhuma, da ƙyar na haɗiye yawun da ya tarumin a baki, dan girman office ɗin mai kiran nawa na kalla da kuma tunanin minene dalilin kiran?.
Yah Qaseem da har yanzu idanusa ke kaina da alamar tambaya na kuma kallo, ya gyara tsaiwarsa yana mai jehomin tambaya,
“Bilkisu mikike ɓoyemin ne?”.
Da sauri na girgiza masa kaina, “Wlhy Yah Qaseem bana ɓoye maka komai, nima bansan minene dalilin kiranba, amma bara naje najiyo”.
Ban jira amsarsaba na bar wajen cikin tafiyar sassarfa, zuciyata sai bugu take da sauri-sauri, dan inaji a raina wannan kiran bana lafiya bane ba, musamman idan nai dubi da ƙaramin matsayina a hukumar.
Koda na iso sai da na jira aka bani izinin shiga sannan, wannan shine karon farko da zan shiga office ɗin a rayuwata, ba shi kaɗai bane a cikin office ɗin, jinai wani abu ya tsargamin daga saman kaina har zuwa yatsan ƙafata, na aro jarumtar dole na yafama kaina tunda bansan minene dalilin kiranba. Na miƙa musu gaisuwa cikin girmamawa kafin na zauna inda aka nunamin.
Tambayar farko da aka jefamin ta sakani ɗago idanuna na kallesu badan na shiryama hakanba, ba firgici ne ya sakani kallon nasu ba, nutsuwace ta zomin saɓanin yanda na shigo a rikice, dan kuwa a nawa tunanin inhar akan rikicin daya faru kwanaki biyar da suka wucene banga wani abin kuskure dana aikata a cikiba, zamana na gyara na fara amsa musu tambayarsu da iya gaskiyata dana sani.
Yanda Bilkisu ke amsa musu kowacce tambaya kanta tsaye babu ko ɗigon firgici ko rawar harshe ya sakasu kafeta da idanu, su kansu iya zallar gaskiyarta suke gani a saman fuskarta da furucinta.
Sun mata tambayoyi sosai, domin sake tabbatar da gaskiyar tata suka sake maimaito mata dukkan tambayoyin da sukai matan a farko, abinda ta faɗa daga farko shine ta sake maimaitawa saboda hakan shine gaskiyarta.
Kusan awa ɗaya da wasu mintuna suka sallamoni na fito, a raina sai juya wannan al'amari nakeyi...
_________________________________
JAWAAD
Zaune yake a office yanata aikin duba wasu tulin takardun dake gabansa yaji knocking ƙofa, siririn tsaki yaja dan baya buƙatar kowa a irin wannan lokacin, izinin shigowa ya bada batare daya ɗago ba balle kallon wanene?.
Ƙamshin turarenta kawai ya bashi amsar wacece, harta zauna bayan gaisheshi da tayi bai ɗago ɗinba, a haka ya amsa mata.
“Mi kike buƙata?”
Ya faɗa yana cigaba da aikinsa batare da ya ɗago ɗinba.
Duk da taji haushi sai ta danne, abinda ta gani kuma ta jiyo game da kiran Bilkisu da akayi office ɗin B.G ta zayyane masa, karon farko da ya ɗago ƙyawawan idanunsa ya sauke akan rose, sai dai baice komaiba. Duk da tsawon kwanaki kenan tana buri da buƙatar irin wannan kallon daga garesa saboda kwallin da take sakawa na jawo hankalinsa kanta sai ta kasa jurewa, dan wani irin kwarjininsane ya kuma cika mata idanu da gangar jikinta, tai azamar janye idanun nata ƙirjinta na wata irin harbawa.
Har lokacin idon Jawaad na akanta, ya cigaba da ƙare mata kallon nazari har kusan mintuna biyu kafin ya janye ya maida ga aikinsa.
Ɓoyayyen numfashi rose ta sauke, daga can ƙasan ranta kuma wani daɗi na sake mamayeta, dan kuwa dai tasan ta gama da taurin kan Jay kamar yanda bokanta ya sanar mata, inhar suka haɗa ido wannan kwallin na idonta to lallai tagama da mallakarsa har abada, ba kuma zai sake kallon kowacce maceba bayan itaɗin.
Sakanni kusan ashirin bai tankaba, bai kuma sake kallonta ba. Takaici ya sake mamaye zuciyar rose, ta buɗe baki da nufin yin magana ya miƙe tsaye, bindigarsa da wayoyinsa dake saman tebir ya ɗauka ya tura cikin aljihun Blue jeans ɗinsa, tare da ɗaukar tab... ɗinsa a hannu. “muje” ya faɗa batare da ya kalleta ba.
Binsa tai da kallon mamaki, harya buɗe ƙofar office ɗin ya fice, dole itama ta tashi da hanzari ta bisa, a ranta tana ayyana cewar ‘Yau ƴan wulaƙancinne a kansa kenan?’.
Fitowar Jay daga office yay dai-dai da fitowar Bilkisu daga sashen office's ɗin su B.G, kaɗan ya rage suyi karo, kasancewar hanyar data haɗa shataletalen office's ɗin ɗayace kafin su ƙarasa su hau lifter da zata kaisu kasa.
Da sauri naja baya ƙirjinna na motsawa, cikin dakewar harshe da banyi zaton inada shi ba nace, “Kayi haƙuri dan ALLAH , bansan ka taho bane”.
Ƙyawawan fararen idanunsa ya zubamin kansa tsaye, kusan sakan biyar tamkar zai cinyeni dasu sannan ya janye batare da yace dani komaiba. ya raɓani zai wuce, hakan yasa na matsa baya na bashi hanya, tafiya ya fara tare da faɗin, “Biyoni”..............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻🙏🏿
[11/15, 5:35 AM] Abue Saleh AlQuyraemey: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Bilyn Abdull 📚:
😂🤣😂🤣😆😆😆Kunsan miyasa nake dariyarnan? Akan yanda kuke ganin kamar bily tsoron Jay takeyi, dukfa halin da take shiga shiba fahimta yakeba, hasalima kallon miskila idan kun lura yake mata, akwai masu samun kansu a irin yanayin bily akan wani ko wata, sai daga baya suke fahimtar dalilin shigarsu irin wannan halin, itama bily lokaci zai warware mata komai har muma mu sami amsa, ina muku fatan alkairi aduk inda kuke, sosai Comments naku na sakani nishadi da sani typing kodama ban niyyaba.
I love you wujiga-wujiga irin trillions ɗinnan🤸🏼🤸🏼🤸🏼 😍😘😍😘😍😘🤗.

Page 6
Chapter 11 · 0% Book details