← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 168

Sashe 18

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

buɗe sannan yace, “An taɓa karyaki?”. Cak na tsaya, ni ban fitaba, ni ban komaba, bamma iya sakin mariƙin ƙofarba saboda yanda furucinsa ya daki ƙirjina, sai da na shaƙi iska na fesar sannan na juyo a hankali ina kallonsa, kauda kaina nayi saboda ganin shima niɗin yake kallo, ya wani haɗe fuska tamkar hadarin tsakkiyar ogusta.
        “Idan kika bari na sake miki magana ki kuka da kanki”.
      A yanda yay maganar da tsananin kaushi sai tsoro ya sake tsirgamin, dama dai ƙarfin hali nake kawai, dole na dawo na zauna ina sake haɗe fuska dan nikam gaskiya an sakama rayuwata ido, komawa nai kujerar dana tashi na zauna. Ina zama shikuma yana miƙewa ɗauke da wasu takardu ya fice daga office ɗin abinsa batare da yace dani komaiba. Na sauke nannauyan numfashi ina kallon naman, bani da zaɓinda ya wuce nacin kawai kodan ya barni na tafi, na ɗauki cinya nakai bakina ina ambatar bismilla, ɗanɗanon naman da laushinsa ya sakani lumshe idanuna, ko ba'a faɗaba dama namannan zaiyi ɗankaren daɗi ai, ban ankaraba na laƙume cinyar na sake ɗaukar wata tsoka irin ta haƙarƙarinan, (Damafa inaso shegen gulma ne. Lol) ina gab da cinyeta aka turo ƙofar da azabar ƙarfi aka shigo, a tsananin razane da ganin wanda ya shigo ɗinne ya sakani miƙewa babu shiri ina kallonsa. Shima idanunsa ya zubamin tamkar zai cinyeni da su.
         “Ubanmi kikeyi nan Bilkisu?!!”
Idanuna na lumshe saboda tsawar tashi ta rasha kunnuwana, na buɗe a hankali kansa, cike da dakiya na zubasu a kansa nace, “Yah Qaseem miya faru?”.
       Wata malalaciyar harara ya zubamin kamar zai juye idanunsa ƙasa, ya fara takowa inda nake, taku baifi ukuba tsakaninmu ya rage aka buɗe ƙofar office ɗin aka shigo. Ni da shi duk kallon ƙofar mukai, sai dai shi a take ya janye nasa idon yana jan uban tsaki. Nikam numfashi na sauke a ɓoye dan koba komai na samu kuɓuta daga wannan yunƙurin na yah Qaseem da bansan mi zuciyarsa ke kissima masa yaminba.
         Jay da ya shigo kuwa kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa ya taka zuwa ga kujerarsa ya zauna.
       A mamakina sai naga yama cigaba da daƙilar Keyboard ɗin Computer ɗin hankalinsa kwance kamar baisan damuba. Shima yah Qaseem ɗin bai tanka masaba ya kalleni yace, “Wuce muje”.
     Jawaad daketa danne-dannensa batare daya ɗagoba yace, “Kai ka kawotane?”. Dogon tsaki yah Qaseem yaja yana damƙar hannuna da faɗin, “Miye na azarɓaɓi ƙaramin tsagera, ai zan dawo kanka idan na gama da ita”. Ya ƙare maganar da fisgar hannuna muka nufi ƙofa. Jinake tamkar na kurma ihu, ‘Nikuma wannan wace fitinace na shigo ciki haka?’..........
      “Wlhy kika fita daga office ɗinan saina saɓa miki kamanninki!”
      Muka tsinkayo kakkausan furucin boss yayinda yah Qaseem ya murɗa ƙofar zamu fice. Bani kaɗaiba hatta da yah Qaseem ɗinma tsayawa daga yunƙurin fitar yay, ya juya yana kallonsa, nidai kaina a ƙasa na gaza kallon kowa a cikinsu, addu'ar ALLAH ya kuɓtar dani daga tsakaninsu kawai nakeyi a raina, dan bansan wazan bijiremawaba? Wakuma zanma biyayya ba?. Yarfar da hannuna yah Qaseem yay ya nufesa, zafin da najine ya sakani durƙushewa a wajen ina sakin siririyar ƙarar azaba.
      Qaseem daya ƙarisa gaban Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa har wasu abubuwan na faɗuwa, “A matsayinka na ubanwa zaka saɓa mata kamannin?”. Ko motsi Jawaad baiyiba balle ya kalli Qaseem, aikin gabansa kawai ya cigaba dayi hankalinsa kwance. A kausashe Qaseem ya sake maimaita tambayar tamkar zai mari Jay ɗin. Ɗago idanu Jawaad yay ya zubasu akan Qaseem, cike da gadara yace, “Qaseem fitarmin daga office!!”.
     “Anƙi a fita, kayi duk abinda kaga zaka iyayi” Qaseem ya maida masa amsa a zafafe shima.
     Jawaad bai sake magana ba, ya miƙe ya nufi Bilkisu dake durƙushe tana hawaye saboda hannunta dake zugi.

        Tsayuwar mutum kawai naji a kaina, cikin bada umarni yace, “Tashi”. Miƙewa nai babu musu, na saci kallonsa, ganin shima kallon nawa yakene yasa na janye nawa ina goge fuska, kafin ya sake wata magana yah Qaseem yazo ya shiga tsakkiyarmu, ”Wuce muje” ya faɗa yana nunamin hanya, haushin murɗamin hannu da yayne yasa naƙi motsawa. Ganin naƙi motsawarne ya sake hasalashi ya

ɗaga hannu zai saukemin mari.
         Rufe idona nai da sauri naja baya saboda masifar firgita da nai da ihun da yaymin akai, na ƙanƙame jikina ganin ya ɗaga hannu zai makeni, shirun da naji yasani ɗago kaina kaɗan naga miya hanashi dukan nawa da yay niyya.. Saurin waro idanu nai waje ganin boss riƙe da hannun Yah Qaseem da ya ƙara kumbura sai hura dogon hancinsa yake.
       “kika fita saina karyaki a office ɗinan Miemaa” boss yay magana a dake  kamar yanda na fahimci halittarsace yin magana kai tsaye koda a gaban wa yake. Saurin duƙar da kaina nai saboda tsatstsareni da yay da idanu, nai baya daga kusa dasu cike da tashin hankalin sakani tsakkiya da sukai.
        yah Qaseem ya fisge hannunsa dake cikin na boss ya kai hannu zai damƙoni ina ƙoƙarin matsawa. Cikin matuƙar zafin nama boss ya fisgi yah Qaseem ɗin gefe, hakan sai ya bani damar mannewa a bango na sake musu kuka kawai, dan zuciyata bazata iya ɗauka ba.

          A cikin tsagwaron fushi Qaseem ya damƙi wuyan rigar Jawaad zai shaƙeshi, “Amma kasan zan iya illataka ko?”.
     Murmushi Jawaad yayi yasa hannu ya ture hannun Qaseem dake damƙe da wuyansa, cikin halin ko in kula yace, “Ka illatanin mana Qaseem, kai wai wace irin banzar zuciyane da kai haka? Mace zaka ɗaga hannu ka daka?”. A matuƙar masife Qaseem yace, “ina ruwanka? Miye matsalarka?” baki Jawaad ya taɓe yana watsa hannayensa da ɗage kafaɗa yace, “Banda” ya ƙare maganar da juyawa zai koma kujerarsa. Saurin maidoshi baya Qaseem yay, hakan ya saka Jawaad tsayawa sai dai bai juyo ya kalli Qaseem ɗinba, ƙoƙarin danne zuciyarsa yake dan bayaso su raba hali gaban yarinyarnan kamar yanda ya kula Qaseem yana buƙata. Cikin nunashi da ɗanyatsa Qaseem yace, “Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da zaka sake saka Bilkisu! cikin lamarinka, itaɗin matar dazan aurace, ya rage naka ka kiyayi ko kaci gaba”.
       Rumtse idanu Jawaad yayi saboda jin yanda Qaseem ya ambaci sunan mahaifiyarsa gatsal, ya juyo a hankali yana kallon Qaseem cikin ido, cikin ƙunar zuciya yace, “Ko wacece ita a wajenka baya gabana, sai dai kai kasani baka isa hanani sakata aikin dana gadamaba tunda har tazo station ɗinnan a ƙasana, kasa a ranka yanzu aka fara wasan kuma, ina gargaɗinka Ka kiyayi  kai hannu kan mace da nufin duka”. ya ƙare maganar a wani irin yanayin rainin wayo. Hakan sai yay masifar sake fusata Qaseem, a tsawace yace, “Matsayinka na ubanwa?”..............✍

Qaseem team & Jawaad team banda faɗa kuma 🚴🏼🏋🏼🤼🏼😂😖.

Ina Bil-Qas team nidai😜🤫🤸🏼.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻

Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO
Chapter 18 · 0% Book details