← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 168

Sashe 42

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

auna a kujerar dake gaban tebirin ɗin.  Hannu ya miƙa masa sukai musabaha, murɗe hannu  Jay yay har saida Jabeer yay ƴar ƙara, ya fisge yana hararsa da faɗin, “ALLAH kai mugune na bugawa a takarda, ciremin hannun zakayi boss”. Murmushi Jawaad yayi yana miƙa masa key ɗin motarsa da faɗin, “Gobema ka sake yin gulma”,.  Jabeer ya sake hararsa yana juya hannunsa, “Kasan ALLAH Jay, yau da ace ba sunan momine da itaba da akanta zan rama, ALLAH ya ceceta kuwa”. Murmushi Jay yayi yana taɓe baki, yace, “Kaje ka rama mana ina ruwana, Am sorry jiya na maka tsawa, rainane duk a jagule kaikuma kazo zaka sake cazamin kai da naka shiriritan”.
        Murmushi Jabeer yay yana shafa kansa dajin ƙaunar abokin nasa cikin rai, “Ni dama ban ɗaukesa komaiba, nasan wanene Jay ɗinmu idan yay fushi, ina fatandai itama Momin tamu ka bata haƙuri, dan na koma office ɗinka kusan 3:45 na isketa tana kuka”. Haɗe fuska da lumshe idanu Jay yayi yana sauke numfashi, “Ai  yarinyarnan bata da kunya. manta da zancenta, ina fatan su Hafiz sun iso, dan inason muyi magana”. Kamar yanda ya buƙata sai Jabeer ya bar zancen bily, ya amsa masa da, “Okey bara na kirasu to, nasan duk sun iso yanzun”. Gyara zama Jay yay, yayi shiru har Jabeer ya gama kiransu. Babu wani jimawa sai gasu duk sun shigo, saida suka gaggaisa sannan kowa ya nema wajen zama, Aliyu da idonsa ya sauka akan yatsan Jawaad dake naɗe da bandage yace, “Boss miya samu hannun kuma haka?”. Hannun Jawaad ya kalla yana ƙaramin tsaki, “Wlhy Aliy wani ɗan ciwo naji, shinefa Alhaji baba yaymin wannan naɗin”. Dariya duk sukayi, Hafiz yace, “Shi ka kaima fushin jiya kenan?”. Hararsa Jay yayi amma baice komaiba.
          “Kunga ku ajiye shiritarnan taku muyi magana yau inada aiki a office saboda jiya banyi komaiba”. Duk hankalinsu suka maida gareshi, Jabeer ya direma kowa kofin coffee daya haɗo, “Thanks ” Jawaad ya faɗa yana ɗaukar kofin, suma su Hafiz sukai masa godiya, Jawaad yakai kofin bakinsa sanan ya janye idonsa a kansu, sai dai yay matuƙar canja fuska saboda maganar da zaiyi tana zafarsa a cikin rai, “Guys dolene yarinyarnan tabar cikinmu a wannan karon, bazan iya cigaba da zama da itaba ta isheni haka nan”. Kallon juna suka shigayi kowa da tsoro akan fuskarsa, Aliyu yay ƙarfin halin faɗin, “Wa kake nufi a cikinsu boss? Kasan yanzu sun zama su biyu”. Kallon Aliyu yayi tamkar bazaice komaiba, sai kuma cikin takaici yace, “Rose nake nufi”. Shiru sukai duk suna jinjina zancen a ransu, kafin Hafiz yace, “Banƙi ta takaba Boss, sai dai hakan zai iya zama wata matsala daban, duk da bansan ainahin abinda tai makaba na kula tanason takurama rayuwar mami ne, abinda kuma na fahimta itafa gani take son Mami kake gaskiya shiyyasa take duk waɗanan abubuwan”. Tsaki Jawaad yaja yana yamitse fuska cike da takaici amma baice komaiba. Suma shirun sukai basu damu da rashin bada amsarba, dan a ganinsu idan son Bilkisu yake wataran ai dole ta fito fili ko. Jabeer ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Gaskiya boss hakan ba shine mafitaba, na farko Rose tasan sirrikanmu da yawa, yaƙi take akan soyayyarka a yanzu, idan kace ta barmu zaitai amfani da wannan fushin ta koma cin dunduniyarmu, munada muhimman ayyuka a ƙasa waɗanda munyi zurfi sosai na kaiwa ga nasara, sune zata fara harin ɓatawa, karka manta zagaye muke da maƙiya, ƙaramar ƙofar da za'a kutsa cikin mutuncinmu kawai ake nema dama, magana ta ƙarshe kuma Rose zatabi duk hanyar da zuciyarta ta ƙawata mata ta cutar da mai sunan mom batare da munsan tayaya ta shirya hakanba, kaga kuwa tako ina korarta ba mafita zata bamuba, domin iyakar gudunmu dai bai wuce kabi ta ƙasa kasa aimata transfer ba, duk nisan da kake tunanin zatayi damu ALLAH saita dawo koda ta hanyar saka wanine yay mata aiki kuwa”.
      Dukansu sun gamsu da maganar Jabeer. Aliyu yace, “Maganar Jabeer fa gaskiyace Jay, sawa tabar cikinmu ba mafita bace, gara ace muna ganin duk motsinta, sannan ni a ganin idan kanason Mami ɗin miza hana ka fito ka bayyana mata kawai a wuce wajen, da zafi-zafi ake bugun ƙarfefa a wannan zamanin”. Fuska sosai Jawaad ya haɗe, cikin nuna halin ko in kula ya wani taɓe baki yaƙi cewa

komai a karo na biyu kan maganar Bilkisu. Duk idanu suka zuba masa na mamaki, sun rasa miyake ɓoyewa. Sai da ya shaƙi iska dan kansa sannan yay magana, “Kuna ɓatamin rai da shirmennan naku, kunefa dalilin shigowar wannan yarinyar cikin tawagarnan, amma miyasa kuke son maida zancenta wani abu daban, to inagama ba rose bace ta cancanci yin nesa damu, Miemaa zansa aima transfer, ince dai shikenan”.
     Da sauri Hafiz yace, “Ba shikenanba, yarinyarnan yanzune ta fara aiki, ƙwazon data fara nunawa yana buƙatar a cigaba da horar da ita akan gaskiya, munji ba sonta kakeba, kuma insha ALLAH babu mai sake maka wannan maganar, inaga kawai mu zauna dasu ita da Rose kajama Rose dogon gargaɗi akan wannan haukar tata mara tushe, domin munutsu mu fuskanci sauran ayyukan dake gabanmu, yanzu aikinan da muke wlhy yanada matuƙar sarƙaƙiya da haɗari, amma gashi muna wasa dashi, sai dau ku yaya kuka gani?”. Jabeer dake wani shegen murmushi yana satar kallon Jay yace, “Hakan yayi nidai a wajena, gara a bar mana Miemaar mu muyita kwasar albarkacin sunanta”. Hafiz da Aliyu sukai dariya, dan sunsan shaƙiyancin Jabeer ne ya motsa, Jawaad kam uffan baiceba, saima miƙewa da yayi yay musu sallama ya fita.
     Yana fita duk sukayi dariya, Aliyu yace, “ALLAH Jabeer kasama boss ido da yawa, nakula son ƙureshi kake kawai,, ka barshi yasha iskar duniya malam”. Nanma dariyar sukayi, Hafiz yace, “kunga nima bara na koma Office, gayenan addu'armu kawai yafi buƙata”. “Hakane kam” cewar Aliyu dake miƙewa shima.

           Fitowar Jay daga office ɗin Jabeer yay dai-dai da fitowar Bilkisu daga motar Qaseem suna murmushi ma juna, dukda a sama yake kuma ta glass yake ganinsu hakan bai hanashi ganin murmushin yamata ƙyauba, dayake ba yawan ganin murmushin nata yakeba sai yazam idan tayi yakan kasance na musamman, ya taɓe bakinsa yana barin wajen.
       Bilkisu kam da batasan yanayiba rakkiya tayoma Qaseem dake bata labarin maganar da sukai akan aurensu jiya da Dad.
      hakan sai yasani jin daɗi da raguwar nauyin da zuciyarta tayi tun a daren shekaran jiya, a ganina garama nai auren na huta, dan na kula zamanmu a haka haɗarine babba a gareni, maganganun Dad na jiya akan fyaɗen mai aikin su Nazifa ya mugun tsaya mani a rai, inada yaƙinin irin wannan ƙaddarar ta afka tsakanin ni da ƴaƴansa to wlhy nikaɗai zanyi kukana, dan tabbas zai goya musu bayane, a yanda kuwa Yah Qaseem ke kaima jikina hari da halayyar Salman da batai minba komai zai iya faruwan, to maganin ayi kar a fara kawai.
         Saida nai masa rakkiya har office ɗinsa sannan na juya na sauka namu, saida na gaisa da kowa sannan na zauna mazaunina, Computer ɗin gabana na kunna domin duba gajeren video da boss ya bani nai sharhi akan abinda na fahimta ciki, gaba ɗaya hankalina na maida akan aikin har Ummie data makara yau ta shigo, gaisuwa tayi da sauran sannan ta matso inda nake ta bani hannu muka gaisa idonmu akan video mu duka. “Bily jiya wai miyasa kika gudu bayan kinsan magana mai muhimmanci muke tattaunawa a group?”. Murmushi nai mata ina cigaba da control ɗin mouse ɗin Computer a hannuna na haggu, na damar kuma ina riƙe da pen ina rubutu a takarda. “Hankalina ne yay masifar tashi Ummie, al'amarinne akwai ruɗani a ciki, dan na fara zargin mai aikata ɓarnarnan ba mutum ɗaya bane sai dai ƙungiya garesu”. Kujera ta jawo ta zauna saɓanin da da take tsaye ta ranƙwafo jikin tebirina, tace, “Miyasa kikai wannan tunanin bily?”. Kallonta naɗanyi na ɗauke kaina ina cigaba da aikin gabana, nace, “Saboda Amina mana, kinga su su Nazifa a gida ɗaya akai musu ita da marigayiyya, sai kuma na yarinyar jiya, amma ita Amina ai a gidanmu akai mata, yanda ake salon fyaɗen duk iri ɗayane, sai an bugar dasu ake cutar dasu, sannan babu wandda ta taɓa ɗaukar ciki a cikinsu, zuwa yanzu ina buƙatar mu haɗu waje ɗaya mu duka biyar ɗin, dan yadace mushiga binciken neman sauran waɗanda hakan ta faru garesu, inaji a jikina Ummie basu kaɗai bane akwai wasu”. Na ƙare maganar da kallonta idanuna cike da ƙwalla. Kanta ta girgizamin a hankali alamar karnai kuka, na ɗauke kaina ina haɗiye abinda ya tokaremin maƙoshi mai nauyi d
Chapter 42 · 0% Book details