← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 168

Sashe 13

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sundai cigaba da magana, sai kuma mukaga suna ƙyalƙyata dariya a tare, hanya ya nuna mata alamar suje, babu musu kuwa tabi umarninsa, tana gaba yana biye da ita har wajen wata Blue ɗin mota, shine ya buɗe mata ta shiga ta zauna sannan shima ya buɗe ya shiga sashen mai tuƙi, munata kallonsu har suka bar harabar restaurant ɗin......
Numfashi ya sauke a hankali yana ɗauke idanunsa da ga wajen, hakan ya sakani nima sauke nawa a ɓoye ina gyara zama cikin alamar takura, addu'ata da fatana bai wuce drivern ya dawo cikin motarba kona samu sauƙi, babban fatana kuma yace na koma gaba inda rose ta tashi, sai dai har tsahon mintuna biyar da barin su rose gidan abincin baiko motsaba balle ya kalleni, saima kansa da ya kwantar jikin sit ya lumshe idanu, “Ƙil!-ƙill!!” tab dinsa tai motsi alamar shigowar saƙo, bai motsaba, hakan yasa mamaki ya kamani......
“Ɗauki ki duba mi tace?” ya faɗa ba tare da ya motsaba. Gabana ya faɗi, dan nadai fahimci dani yake, kuma yana nufin tab.. Ɗin tasa zan ɗauka, ganin bai sake maganaba ne ya sakani kallonsa, a ɗarare nace, “Dani kake sir?”.
“A'a da kaina nake” ya faɗa a daƙile......
Kafinma ya rufe baki na kai hannu na ɗauki tab ɗin da ya ajiye a tsakkiyarmu, gabana sai wata irin faɗuwa yake tamkar zan haɗiye zuciyata a cikin bakina, madannin na danna ta kawo haske, wani haɗaɗɗen hotonsa ya bayyana, duk da son kallon hoton da naji ya tsargamin hakan baisa na tsayaba, saima mamakin ganin babu lock a jikin tab din ne ya kamani, naja hoton yay sama kawai, a take apps da yawa suka bayyana, baza ido na shigayi wajen neman messeges app, da ƙyar na tsaida hankalina na ganosa, ina buɗewa kuwa da sunan rose na fara cin karo, na buɗe saƙon nata, abinda ta turo bai shige kalmomi hamsin ba. “boss ya buƙaci nabisa, duk abinda ake ciki zakaji daga gareni”.
Cikin ɗan rawar baki nakaranto masa kamar yanda ta rubuto da harshen turanci, bai motsaba, bai kuma tanka mani ba, hakan yasani ajiye tab ɗin ina mai satar kallonsa, sai da ya ɓata lokaci kafin ya jehomin tambaya.
“Ya sunanki?”.
‘Ikon ALLAH’ na faɗa a raina kafin na bashi amsa da, “Bilkisu Adam makaho”.
Yanda ya buɗe idanu da sauri a kaina ba ƙaramin firgitani yay ba, mayun idanunsa masu saka tsigar jikina tashi ya dasamin, bansan miya bashi mamakiba, sunan nawane? Kokuwa na babana? Kokuwa makahon dana ambata a ƙarshe?. bansan amsarba, bani da ƙwarin gwiwar tambayarsa kuma. Tsahon minti ɗaya da sakanni yana kallona kafin ya janye idanunsa yana motsa baki tamkar mai son cewa wani abu,ni dai ta wutsiyar ido nake kallonsa shi da jin kansa.
Baice dani komaiba ya buɗe motar ya fita, ajiyar zuciya na sauke, dan fitar tasa sai naji kamar ya bani wani ƙaton filin cin karena babu babbaka ne.......
“Ko sai an fiddoki?”. Furucinsa ya daki kunnena, da azama na buɗe murfin na fice nima, gani nai ya wani zubomin idanu, bansan mi yake nazartaba daga gareni, sai jefani a ruɗanin zuciya dana takurar kaifin idanunsa da yayi, hakan yaja nai ƙasa da kaina dan bazan jura kallonba.
Takunsa kawai naji alamar ya matsa daga kusa dani, na saci kallonsa, sai naga yana ƙokarin ciro abu daga cikin but ɗin motar da ya buɗe, nufonin da yayne ya sani saurin ɗauke idona, ya miƙomin farar coat ta mata da tsayinta zai iya kaiwa gwiwa, ban musaba na amsa, sai dai ina buƙatar ƙarin bayani, “Saka” ya faɗa yana wuceni.
Sosai naketa mamaki, na warware rigar na saka a jikina saman Uniform ɗin dana sanya, sai ya zam rigar ta ɓoye bayyanar ni wacece, baƙin wandon kawai ake iya gani ta ƙasa, daga sama kuwa farin baby hijjab ɗinane ya bayyana, sai rigar ta fiddamin da wani tsari daban daya bayyanar da sirrintaccen kwarjinina da wasu ke iya ambata da ƙyawu. Bai cemin komaiba yay gaba na bisa a baya, dan zuwa yanzu kam na fara fahimtar hallayarsa da hanyoyin maganin zama da shi.
Sai da muka gabato shiga ƙofar wajen sannan ya tsaya muka daidaita tafiya, ƙasa-ƙasa na tsinkayi muryarsa yana magana.
“Ki kula sosai, sannan ki tabbatar da yanayinki ya canja tamkar munada dangantaka, idan kikamin shirmen da aikina ya buɗe

lallai sai kinyi nadamar hakan”.
Sosai maganganunsa suka tsirgamin zuciya, dan kuwa ban gama fahimtar ma'anarsu ba balle manufarsu har muka ƙarasa shiga wajen.
Wajen yay bala'in haɗuwa, daga gani kasan masu abokan magana a aljihune kawai keda hurumin shigarsa, dan danan akai mana tarba ta mutuntawa, yanda ya ƙawata fuskarsa da murmushi ne ya ɗauren kai, hakan yasani nima aro irin basajar tasa na yafama kaina ina murmushin, ɗaya daga cikin yaran wajenne ya nuna mana wajen zama, bayan mun zauna yake tambayarmu komi muke buƙata.
Boss ya juyo yana kallona fuskarsa shinfiɗe da wani murmushin da ya kusa zautani, “My princess! Mi kike buƙata?”.
Wata masifar harbawa zuciyata tayi, kaɗan ya rage ban fallasamu ba, nai azamar haɗiye zuciyata dake niyyar fitowa ta baki saboda salon da yay amfani wajen kiran sunana da yanayin fitar sautin, da ƙyar na iya dai-daita kaina nai wani farin da bansan na iyaba da idanu, ina wani narke murya nace, “Duk abinda ka zaɓa mana yayi my king”.
Ɗauke idanunsa yay daga kaina, har zuwa yanzun fuskarsa ɗauke da murmushin da ya fidda lotsar dimples ɗinsa masu ɗaukar hankali, ya duba waiter ɗin yana bashi umarnin ya bashi list ɗin abinda suke da shi ya duba.
Da girmamawa ya amsa yana barin wajen, saurin yin ƙasa nai da idanuna ganin ya maido kallonsa gareni, murya ƙasa-ƙasa yace, “Ina sake gargaɗinki a karo na biyu”.
Kaina na jijjiga masa ina saurin gyara yanayina. Sallama wata matashiyar budurwa taimana saɓanin wanda yazo ɗazun, sanye take da Uniform ɗin wajen itama, cikin girmamawa ta ajiye goran ruwa biyu da kofuna dake saman tire ƙarami, kafin ta miƙa masa ɗan littafi dake a hannunta. Amsa yay yana dubawa, tare da yin alama da pen ɗin data haɗa masa da shi akan duk abinda muke buƙata, baifi sakan sha biyarba ya miƙomin littafin yana fadin, “Duba yayi?”.
Amsa nayi ina kuma matse nutsuwata, nai nazarin duk abinda ya zaɓadin kafin na ɗago ina murmushi, cikin salon da bansan nayiba na ɗaga masa gira ɗaya da juya ƙwayar idona kaɗan alamar yayi.
Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana sakin wani lallausan murmushi da yafi na ɗazu.
‘Innalillahi....’ Na iya ambata ina saurin maida fitsarindake neman kufcemin.
Tana barin wajen ya kalleni da sauri, murya ya rage ƙasa sosai, wanda yake nesa damu zai ɗauka soyayya mukeyi, maganar da ya faɗamince ta sakani jinjina masa kai da sauri, ina kuma murmushi, badan tanada alaƙa da murmushin nawa bane, sai dan kawai barin murmushin akan fuskar tawa ya zama tilas saboda kiyaye gargaɗinsa...........✍

🙄saura kuma ai gulmar Jay😏

ALLAH ka gafarta iyayenmu😭🙏🏻Bilyn Abdull 📚:
😂🤣😂🤣😆😆😆Kunsan miyasa nake dariyarnan? Akan yanda kuke ganin kamar bily tsoron Jay takeyi, dukfa halin da take shiga shiba fahimta yakeba, hasalima kallon miskila idan kun lura yake mata, akwai masu samun kansu a irin yanayin bily akan wani ko wata, sai daga baya suke fahimtar dalilin shigarsu irin wannan halin, itama bily lokaci zai warware mata komai har muma mu sami amsa, ina muku fatan alkairi aduk inda kuke, sosai Comments naku na sakani nishadi da sani typing kodama ban niyyaba.
I love you wujiga-wujiga irin trillions ɗinnan🤸🏼🤸🏼🤸🏼 😍😘😍😘😍😘🤗.

Page 6
Chapter 13 · 0% Book details