← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 168

Sashe 76

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

        Jawaad kam daga wajen baba ƙaura tashar da Gimba ke shiga mota idan zai tafi gida ya nufa. Wajen bawani babban tsasha baneba, dan motocin garin su Gimban ne kawai sai masu ƙarisawa cikin ƙauyikan dake maƙwaftaka dasu. Kowa na sabgar gabansa daga masu talla har matafiya da masu sauka, sai ƴan mashinan Napep dake ɗaukar masu shiga cikin gari idan an saukesu a tashar. Sai da ya gama ƙarema wajen kallo daga cikin motarsa kafin ya ɗauki glasess ɗinsa baƙi ya toshe idanunsa dashi, baya wani cikin mood ɗin farin ciki, hakan yasa sam fuskar babu alamun sauƙi balle rangwame. Tamkar zakin dake taƙama bayan yaci ya ƙoshi haka ya fito daga motar, dama tun fakawarsa mafi yawan jama'ar dake kai kawo a wajen suka zubama motar ido da tsumayen waye zai fito daga cikinta, dan kuwa dai taci ta ƙoshi ita kanta motar balle kuma mamallakinta a ganinsu dole ya zama abin kallo. Yako zama abin kallon dan shi kansa saida ya takura dajin yanda idanu ke yawo a kansa har jinin jikinsa na tsitstsinkewa. Guntun tsaki yay yana sake ɗaure fuska, ya fara taku a hankali yana tunkarosu kansa tsaye.
       Tuni da masu kallon nasa da masu gulma suka nutsu, aka shiga gaishesa da tambayarsa ko akwai abinda yake buƙata?. Ta cikin glasess ɗinsa yake ƙare musu kallo ɗai-ɗai, sukam sam basa ganin idanun nasa, sai ƙyawun da glass ɗin yayma fuskarsa ba ƙaramin ɗaukar hankalinsu yayba. Jawaad ya shiga ƙarema saurayin dake gabansa tamkar zai duƙa kallo, nuni yay masa da hannu alamar ya miƙe da ƙyau. Babu musu kuwa ya miƙe. “Inason ganin shugaban wajen nan naku ne”. Jay yay maganar yana maida hannunsa guda cikin aljihun wandonsa. Kafinma saurayin yace wani abu wani dattijo da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci wahalace ba tsufaba ya ƙaraso wajen yana mai amsa maganar Jay data shiga kunnensa. “Gani nan Alhaji, barka da zuwa, naɗan zagayane kama ruwa shiyyasa”.
    Shi dai jay kallonsa kawai yake harya dasa aya. Dattijon ya kuma faɗin, “Muje daga cikin runfa Alhaji nan kaga rana na dukanka”. Babu musu Jay ya bisa suka shiga rumfar da ƙuda keta faman bi saboda sanyinta, ga robobin abinci da sukaci harda na fura duk ƙudan ya baibaye, gefe kuma masu saida abincinne ƴammata da yara ƙanana abin gwanin ban tausayi. Shi kallonsu yake da tausayawa sukuma suna kallonsa da birgewa da sha'awa. Duk da Jay yaji ƙyanƙyamin tebiran dake wajen matsayin abun zama haka yay shirin zaunawa akai da farin wandonsa tas daketa ɗaukar ido. Da sauri dattijon nan ya dakatar dashi, abin sallar dake can kan babbar tabarma shimfiɗe ya ɗakko bayan ya bugata ƙura ta tashi,  yazo ya saka masa kan bench ɗin. Jay baice komaiba ya zauna duk da itama dai sallayan sai a hankali.
        Dattijo yace, “Alhaji bara a kawo maka ruwa ko fura”. Da sauri Jay yace, “A'a nagode karka damu, tambaya nazo yi”. Dattijo yace, “ALLAH yasa na sani to Alhaji. Jay yaɗan gyara zamansa, idanunsa dake cikin glass kafe akan Dattijo, yace, “Akwai wani yaro saurayi da bazai wuce shekaru talatin da ɗaya ba mai suna Gimba, duk ƙarshen mako yake zuwa nan ya shiga mota ko k

un sanshi?”. Cike da jimami Dattijo yace, “Tabbas munsan Gimba, ai a wajenan kaf Alhaji babu wani driver da zai ce maka baisan marigayiba, danshi mutum ne na mutane ga barkwanci ga alkairi”. Jay Cikin nuna alamun kamar bai sani gimban ba yace, “Naji kace marigayi; kana nufin ya rasu ne?”. Zama Dattijo ya gyara yana matsar ƴan ƙwalla, “Alhaji ashe bakasan ya rasuba? Ai jiya-jiya akai zana'idarsa ma, muma yau labari yake zuwa mana akan duk yanda abun ya faru, ance ogansa da yakema aikine yajasa cikin ƙungiyar asiri, dama anata ƙananun magana akan yanda Gimban kema mutane ɓarin abin arziƙi  a garin musamman a irin wannan watan na Ramadhan dazai kama, to dai kasan mutanenmu da kwaɗayi, dukda anajin tsoro dai haka ake amsa a lashe, sai ya gusa kaji anayi dashi, saifa yanzunne da suka tsotse jinsa zance keta fitowa abubuwa gasu nandai barkatai babu daɗin ji”. Tunda Dattijo ya fara magana jikin Jay ke wani yaamm na mamaki, haka kuma aka maida zancen rasuwar gimban ahi baida labari?, kai ɗan adam sai dai ka gansa ka barsa da halinsa kawai, baiji komai a ransaba tunda yasan ba hakan bane, abinda kawai ya ɗauka jahilci ne ke aiki cikin ƙwaƙwalen kansu. Ya gyara zamansa cike da ƙwarewa cikin salon aiki yace, “Ai nima akan batun mai gidan nasa nazo daman, yanzu haka mun kamashi a hannu bincike mukeyi, idan ka bamu haɗinkai kaima kanada naira dubu hamsin sabbi ƙar a takarda. Jimm Dattijo yayi yana ninƙaya a nazari, mikuma ya tuna sai ya kalli Jay yace, “Nikuwa mina sani akan wannan zance Alhaji?”. A karan farkio Jay yay murmushi, “Ba canai ka saniba daman ai, sonake dai naji abinda ka sani ɗin, ranar juma'a Gimba yazo tashar nan taku?”. Dattijo yace, “Eh to kamar dai yazo”. Jay daketa dannewa bayason ya tsoratashi yace, “Banason ƙwana-ƙwana a magana, ka fitomin a mutum mu wanye lafiya”. Ya ƙare maganar da zare glass ɗin idonsa sukai ido huɗu da Dattijo. Sosai kwarjinin Jawaad ya sake cikama Dattijo idanu dama wajen baki ɗaya. kasa jurar kallon idon da Jay ke masa yayi ya duƙar da kansa. Jawaad yay wani munafukin murmushi yana ɗauke kansa shima, “Yaya zan samu amsar gaskiya?”. Kai Dattijo ya ɗaga batare da ya yarda ya sake kallon Jay ɗinba. “Tabbas yazo nan ranar juma'a nayan an sakko masallaci”. “A motar wa ya tafi gida?”. “Bai shiga motar kowaba ranar a tashar nan”. Cikin ƴar fusata Jay yace, “To motar wa ya shiga?!”.  “Ni...ni bansanshi ba Alhaji”. Murmushi Jay ya sakeyi irin na zan lailaya kanka a titi ɗinan ya ɗaga jacket ɗinsa ƙaɗan yace, “Kalli nan”. Koda Dattijo ya ɗago yauy arba da bindiga sai ya waro idanu waje, kafin kace kwabo zufa ta gama jiƙesa. Jawaad yace, “Saika zaɓa, amsata ta gaskiya kokuma rasa numfashi?”. “ALLAH ya baka haƙuri oga, wlhy inada iyali da ƙananun yara a gida, abinne wuya garesa shiyyasa”. “Kai kake ganin wuyarsa”. Cewar Jay yana haɗe fuska fiye da farko. Cikin kakkausan murya yasake faɗin, “A wace mota gimba ya tafi gida ranar juma'a?”. “Tare da ɓaleru” Dattijo ya faɗa da sauri kamar zai haɗiye harshensa.
            Jay ya sake zare glass ɗin idonsa a karo na biyu, sun sake kaɗawa sunyi ja da ɓacin rai, “Wanene Ɓaleru?”. Ya faɗa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya da harɗe hannayensa saman ƙafar yanaɗan juya glasess ɗin hannunsa idanunsa kafe akan dattijon. Kan Dattijo a ƙasa yace, “Shima ɗan garinmu ne, zanma a iya ce maka kamar abokai suke da marigayi gimban, dan duk sa'anni ne kuma unguwarsu ma kusan ɗayane”. “Ina zan samesa yanzun?”. “Wlhy oga ban saniba, kawai dai nasan yana anan birni shima yana aikin drivernci a wani gida”. Miƙewa Jay yayi tsaye da cewar, “Koma ina yake ni zan memosa, ba'a cin kuɗina a matsayin cin hanci, amma ina biya idan na saka aiki, zan baka aiki nakuma biyaka yanzunan, ya rage naka kaimin da gaskiya kokaci amanata idan anzo an biyaka abinda yafi nawa, biyoni”.    
        Jiki a saɓule dattijo yabi bayan Jay har zuwa isa inda ya faka motarsa. Jawaad ya buɗe motar ya shiga ya zauna batare daya rufeba, ƙafafunsa duka a waje, takarda ya ciro da pen ya kalli Dattijo dake tsaye, “Ka iya karatu ne?”. Da sauri Dattijo yace, “Eh nayi sakandire Oga”. Jay baice komaiba ya maida kansa y

ay rubutu da hausa a takardan sannan ya miƙa dattijon tare da kuɗi bandir ɗin ɗari biyar. “Wannan aikin zakaimin, ga kuɗin aikinka nan”. Daga haka ya shige motar sosai ya rufe abinsa yaymata key tare dayin reverse yabar wajen.
Chapter 76 · 0% Book details