← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 168

Sashe 140

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

r ana kiran sallar isha'i sai Jay yay gyaran murya. ɗagowa sukai duk suka kallesa. Ya sakar musu murmushi da waro idanunsa waje kaɗan ya miƙa musu kwalin tissue da ya ɗauka saman centre table. Babu musu suka amsa. “Yauwa Momys ɗina ababen alfaharina, kukan ya isa haka nan kar ku ƙarar mana da hawayenku, lokacin kuka ya wuce yanzu farin ciki ake buƙata da godiyar ALLAH da ya kawo ranar da ba'a taɓa tunani ko tsamanin zuwanta ba, idan kuna kuka mu kuma mi zamuyi to?”. Cikin kaɗa kai Ummah babba tace, “Hakane Jawaad, ALLAH yay maka albarka kaida sauran ƴan uwanka kaji, a ina ka gano mana Zuciyarmu ne yaron albarka?”. “Ihhhmmm karku damu zan faɗa muku komai sweet Ummahs ɗina, amma ba yanzu ba sai tsohon can shima yana gefena”. Daƙƙuwa Ummah ƙarama tai masa tana faɗin, “Sai dai idan iyayenka ne tsoffi”. Dariya ce ta nema kufcema su Bilkisu, suka saka hannaye duk suka kare bakunansu banda Aunty Batool da tayi abunta sosai. Miƙewa yay ya dungurema Aunty Batool kai yay ficewarsa domin yin sallar isha'i.
          Bayan sallar isha'i natsuwa da ga UBANGIJI ta kuma saukar musu a zukata, duk da su Ummah suna ƙage da sonjin wani abu daga yayar tasu, kamar yanda itama a ƙagen take sai Jay ya hana, a cewarsa sai sunci sun ƙoshi sannan hakan zata kasance. Babu yanda suka iya suka yarda da batunsa, dan suma sunsan ya cancanci Umm-Anum taci abin ma ta kwanta ta huta, sai dai zukatansu bazasu iya jure hakanba.
      Ummah babba da kanta ta bama Anuwar da Anum abinci a baki cike da so da ƙauna, hakama Umm-Anum ta bama Aunty Batool da Nabeelah da Bilkisu, Jay kuma Ummah ƙarama ta bashi. Cikin wani irin farin ciki mai wahalar misaltuwa sukaci abincin suka ƙoshi, dan Umm-Anum har su Ummah ma sai da ta dinga basu a baki da kanta. Abin dolene ya sakaka kuka ya kuma birgeka. Sai da sukai nak da girki suka godema UBANGIJIN daya basu badan ƙarfinsu ba ba kuma dan sunfi kowa ba sannan su bily suka tattare wajen tas. Da taimakon aunty Batool da Nabeelah da Anum suka wanke komai tsaf. Yayinda a falo kuma Jawaad ke ta bama su Ummah labarin yanda komai ya kasance game da ganin Umm-Anum ɗin duk da dama tun a wancan lokacin ya labarta musu a sanadin Bilkisu ne. Wata iriyar ƙauna da soyayyar Bilkisu sai ta ƙara faɗaɗa da daɗuwa a cikin zukatansu. Duk yanda mai hasashe zaiyi tunaninta a zukatansu tafi gaban hakan ta wuce.
        Sabon babin fira aka buɗe a cikin falon ba tare da sunma tuna darene ba ranaba, babu mai kallon lokaci babu mai tunawa ma da shi. Ba suba ko Jay da baisan yawan surutu yau sai yaji hakan bai gunduresa ba, wani wajen ayi kuka wani wajen ayi dariya, wani wajen ayi tausayi da al'ajabi. Haka kawai bilkisu ta tsinci kanta da yin matsanancin kuka akan labarin Aunty Mah-mah (Rahmah), haka kawai taji tana ƙwaɗayin ganinta koda kuwa a hotone. Hakama Umm-Anum ta shiga matsanancin mamaki da jin wai Bilkisu ba ɗiyar Rahmah bace ba. Yayinda shi kuma Jawaad al'amarin yay masa tsaye cak a zuciya baisan dalili ba, kawai yanaji a ransa kamar akwai wani abu dake a binne game da rayuwar bilkisun, musamman idan ya tuna da maganar baba ƙaura akan duhun dake biye da Bilkisun, da kuma furucin baba ƙauran a jiya da yaje wajensa saboda kiran da yay masa. ‘Kai anya kuwa babu wani abu........?’ ya faɗa a cikin ransa yana kafe Bilkisu da idanu harta tsargu ta ɗan ɗago suka haɗa ido.
            Barci ma da kansa yasan inda yake zuwa yay sata, dan kuwa idanun waɗanan bayin ALLAH ko gyangyaɗi basaji balle ai maganar barci, suna zaune dingangan har agogo ya nuna ƙarfe uku saura na dare. Jay ne ya katse firar tasu da roƙonsu akan suje su kwanta haka da safe idan ALLAH ya kaimu saisu ɗora. Badan sunso hakan ba suka miƙe dan suma susan Umm-Anum na buƙatar ace ta huta kodan doguwar tafiyar da tayo wadda bata saba ba. Su mamaki ma abin ya basu dan basusan lokaci yaja haka ba, jima suke tamkar daren bai wuce ƙarfe goma ba. Dole dai yau su kwana gidan ɗansu.
       Ummah babba Umm-Anum da Ummah ƙarama ɗakin bily aka kaisu su kwanta tare da ƴar uwarsu, duk da dai ba kwanciyar sukaiba wani babin sabuwar hirar suka sake buɗewa ma su. Batool da Anum da Nabeelah kuma ɗaki

n dake kusa dana Bilkisu, Anuwar yana a ɗakin baƙi. Jay ya nufi nasa ɗakin, Bilkisu na shirin shigewa wajensu Nabeelah Ummah ƙarama ta korata ɗakin Jawaad.

        Sosai kunya ta lulluɓeni har inaji kamar ƙasa ta tsage na shige, to amma yaya na iya suɗin ba abin wasana bane balle nai tunanin musu gardama ma, haka na nufi sashen nasa kamar na nutse dan kunya. Ina jiyo su Nabeelah namin dariya harda Yah Anuwar. Sam banso hakanba, dan naso ace mun samu nisa da juna ni da shi koda na kwanaki biyu ne dan ya fahimci inajin zafin abinda ke faruwa tsakaninsa da ƴan uwana, ƙila ta hakan zan samu ya faɗamin abinda ke faruwar. Badan a ciwon kan da nake ji ba da falo zanyi zamana na ƙarasa daren, haka dai na daure fuska a ciskule na nufi bedroom ɗinsa, ciki ciki nai sallama na shiga, yana kwance a saman gado da ga shi sai noxer kawai, idanunsa a rufe suke amma na tabbata ba barci yake ba, na ɗauke kaina daga garesa na nufi bayi. Ban wani jimaba na fito dan fitsari kawai nayi da abinda baza'a rasaba. Yanda na barsa haka na fito na samesa, bani da kaya a ɗakin, sai naita tunanin mizan saka na kwanta dan bazan iya barci da kayan jikina ba. Ganin lokaci na sake ja ga zazzaɓi nama neman saukarmin yasa na nufi Wadrobe ɗinsa, cikin sa'a kuwa idanuna saka sauka akan t-shirt ɗinsa mara nauyi ruwan toka, nasan indai na saka zata sakkomin dan babbace kuma girman ba ɗaya ba.
        Zagayawa nai ta ɗayan gefen na kwanta can ƙarshen gado na juya masa baya.....
       “K har kin isa mu kwanta a gado ɗaya ki juyamin baya!”. Na tsinkayi saukar muryarsa da furucinsa a fusace cikin kunnuwana. Ɗan rintse idanu nayi ina haɗiyar yawu da ƙyar, zuciyata sai harbawa take da sauri-sauri na tsoro. A hankali na juyo ina tura baki da sake ɓata fuska sosai, abin mamaki har yanzu yana a yanda yake. A ƙasan ido naɗan hararesa naja bargo na rufe har fuskata ma.
         Wani haushi ya sake kume zuciyar Jay, jiyake kamar yay mata filla-filla ɗin da saita ƙarasa daren da kuka, sai dai yanata ƙoƙarin danne fushinsa kawai.
        Ba ƙaramar razana naiba jin an fincike bargon, na waro idanuna dake cika da ƙwalla a kansa, fisgoni yay na faɗa jikinsa ya matseni tsam-tsam, wani marayan kuka na buɗe baki zan sakar masa sai dai kuma ya hana hakan ta hanyar baƙar muguntarsa da ya ƙware a iyawa, nasan bani da wani ƙarfin ƙwatar kaina daga garesa musamman ma a irin wannan lokacin da sam banajina ma garas. Ɓacin ransa baisa shi kasa bidani cikin salon natsuwa da salo mai tsayawa a zuciya ba.............

....
..........✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

👇👇👇👇👇

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
[2/4, 11:10 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🥚ƙwai Cikin Kaya🥚
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
Page 57

_______________________________
SHAHUDAH
_______________

                 Saukar su Umm-Anum ƙasar haihuwarta tayi dai-dai da komawar Shahudah gida. Mom da Aamilah ne kawai a gidan, Dad ya fita tun bayan barin su Jay gidan. Waya Mom keyi da Mama Atika. A take ta saki wayar ƙasa ta tarwashe bisa tiles jikinta na tsananin tsuma.
         Shahudah da ke cikin wani yanayi kamar ba'a hayyacintaba ta ƙaraso cikin falon tana tangaɗi ta zube saman carpet. Da ga Mom har Aamilah zubewa sukai a gabanta jikinsu na rawa, sai kuma Aamilah ta miƙe da sauri taje ta leƙa waje. Babu kowa sai maigadi daya taimakama Shahudah ta shigo ya juya zai koma wajen gate. Komawa falon Aamilah tayi bayan ta rufe ƙofar ruf ta garƙama mata key. Ta koma wajen su Mom da gudu tana faɗin “Mom ita kaɗaice fa wlhy babu ɗan iskan”.
     Mom tace, “Nashiga Uku ni Aysha, Shahudah daga ina kike haka? Miyayi miki ne?”. Bata da mai amsa mata waɗanan tambayoyin dan Shahudah sai faman lumshe idanu kawai take. Mom ta ƙanƙameta a jikinta ta fashe da kuka tana jama ɗan-fir'auna mugayen addu'oi. Suna cikin haka akai knocking ƙofar, duk ɗagowa sukai suka zubama ƙofar falon ido kawai, sai dai daga Mom ɗin har Aamilah babu wanda ya iya motsawa. Shiru ba'a sake bugawar ba, hakan yasa suka share suka maida hankalinsu ga Shahudah.
        Salman dake buga ƙofa ganin ba'a buɗeba sai ya zagayo ta kitchen, shikansa ba ƙaramin mamakin ganin Shahudah yay ba, jikinsa har rawa yake wajen ƙoƙarin kiran Dad ya sanar masa Shahudah ta dawo.
Chapter 140 · 0% Book details