Sashe 155
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
a fara hango Jawaad dake tsaye daga can ƙofar ɗakin yana facing nashi, ya ɗan kafesa da kallo tamkar dai yanason gano wanene?. takowa Jay yay a hankali zuwa gaban gadon, ya tsaya kusa da Umm-Anum tare da ɗan ranƙwafawa yanama Alhaji babba murmushi, hannu ya saka da kansa ya cire masa na'urar da aka saka masa. cikin magana a hankali yace, “Tsoho mairan ƙarfe!”.
Karan farko Alhaji babba yay wani ɗan murmushi kaɗan da sake motsa hannunsa sai ya jisu duka biyu an riƙe. “Babah!” Umm-Anum ta kira sunansa cikin sanyin murya. Cikin wata irin faɗuwar gaba Alhaji babba ya juya saitin inda yaji muryar da bazai taɓa mantawaba a rayuwarsa, to kodai mafarki yakeyine har yanzun? Ya ayyana a ransa yana ware idanu akan Umm-Anum dake kallonsa tana murmushi da hawaye.
Ya mata kallon kusan minti ɗaya kafin ya sake juyowa ya kalli Jay, sai kuma ya kalli Anuwar da Anum, ya sake maidawa ya kalli Ummah ƙarama da babba da Batool, Bilkisu da Nabeelah, cike da ƙarfin hali ya yunƙura zai tashi zaune dan ba'a ƙaramin ruɗani ya tsinci kansaba. Saurin riƙesa Jay yayi yana girgiza masa kai. Alhaji babba ya kalesa cikin muryar dake nuna bashi da lafiya yace, “Jawaad mafarkin dana sabane ko? Yo inba mafarkiba a ina nikam zanga mahaifiyarka ido da ido irin haka? Dan ALLAH kaga karka tadani a barcin nan barni nayi tayi ko ALLAH zaisa itama Rahmah da Maryam da Amina da Adamu zasuzo gareni duk mu haɗu anan”.
“Baba ba mafarki ka ke ba, Bilkisun ka ce a gaske gabanka, nice na dawo gareku, ni ce ban mutuba baba”. Umm-Anum ta faɗa tana rushewa da kuka. Ai yanzunkam babuma wanda yaga sanda Alhaji babba ya tashi dingangan zaune yana riƙo hannun Umm-Anum cikin nasa duka, jikinsa sai rawa yakeyi, hannunsa ya ɗaura saman idonsa ya murza, ya kai kuma kan fuskarta ya shafa. Tabbas ba mafarki yakeba Bilkisun sa ce a gabansa, bilkisun daya rasa kusan shekaru ashirin dashida, bilkisun daya fidda rai da gani a wannan duniyar dukda yana tsananin ƙwaɗayin hakan. “Bilkisu dama kina raye?”. ya faɗa da tsananin rawar murya.
“Ina raye baba, ganima ALLAH ya ƙaddara sake haɗuwarmu, na godema UBANGIJINA daya saka ka kasance mai tsahon ran da zan dawo na tadda, da ace na dawo baka raye bazan taɓa daina yima mutanen nan munanan addu'oi ba har randa numfashina zai yanke”. Fashewa Alhaji babba yay da kuka, ya kamo kan Umm-Anum ya ɗaura saman cinyarsa ya rungume yana sake fashewa da kuka mai ban tausayi da tsuma rai.
Da ƙyar Jay da Doctor suka samu damar lallashin Umm-Anum da Alhaji babba, harma dasu Ummah dasu Bilkisu, sai dai fa Alhaji babba ya tubure akan ya warke a sallamesa ya tafi gida, anyi lallashin duniya yace sam baisan wannanba wlhy shifa bazai kwana a asibitin nanba koma mi za'ayi.
Ganin ya rikice musu harda hawaye Jay yace Doctor ya basu sallama kawai, sai su sami likitan dazai dinga zuwa gida yana dubashi babu damuwa. badan Doctor yasoba ya basu sallama.
Jay da Anuwar ne suka kama Alhaji babba aka kaisa har mota, yayinda itama Ummah ƙarama ke riƙe da Bilkisu da keta dauriya da ƙarfafa jikinta dukda batajin daɗinsa sam, sai dai ƙasan ranta wani irin farin ciki takeyi da barin asibitin da zasuyi. Motar ta musu kaɗan, dan haka suka shiga ta Aliyu da suka iso asibitin babu jimawa suma dan an ƙaro jami'an tsaro cikin asibitin saboda mutane dake neman kawo ruɗani, acewarsu sunason suga gawawwakin da waɗanda aka samo da rai ko akwai ƴan uwansu a cikinsu.
Jay bai bisuba, cikin asibitin ya sake komawa inda Qaseem da Salman ke tare da Mom wadda ta farfaɗo amma sun mata allurar barci mai ƙarfi dan jininta ya hau sosai, Doctor ma yace badan ALLAH ya taƙaita mata wahalaba irin wannan faɗuwar da tayi zai iya sakawa ta kamu da paralysis. Sai da suka ɗanyi magana da Qaseem da shi kansa idan da za'a bashi gadon an taimakesa sannan Jay ya fito. Daya fito ɗinma wajen su Jabeer ya tsaya sukai magana sannan ya amshi key ɗin mashin ɗin ɗaya daga cikin jami'insu yabi bayan su Alhaji Babba.
_________________
Dr Tayyeb Hospital
_____________________
Shahudah dai suma tai a wajen, sai da cikin ƴan matan family
ɗin wata tai ƙarfin halin shafa mata ruwa sannan ta kawo numfashi, hakama matar Uncle Nasir ita sai dama aka bata gado, ƴaƴansa nata kuka maiban tausayi da saka zukatan mai kallonsu rauni. Kosu Uncle Sulaiman sai da suka share hawaye dan tsananin tashin hankali. A yanzun kam sun fahimci zaman asibitin sam bazai yuwu a garesuba, dan haka suka tattara inasu-inasu suka nufi gida, dan anma hana kowa shiga wajen Mama Badiyya dama, ba'ason ai mata wata hayaniya ko kaɗan.
Sun iso gida suka iske waɗanda suka bari anan cikin matsanancin tashin hankali suma, ciki harda Mama Atika da tafi kowa shiga ruɗani ganin halin da babba ɗanta yake a ciki da surukinta, tayi bala'in yin wujiga-wujiga da ita tamkar wata taɓaɓɓiya, dan sai surutai take, fitsari kuwa ba'a magana, tayisa a zane sau babu adadadi batare da tasan yanama zuba ba. Sai da ƴan asibiti suka isone suka fargar da ita halin da take ciki.
Tabbas bayyana irin kalar ruɗanin da wannan ahali suke ciki ɓata lokacine, sai dai na bama kowa gari ya ƙiyasta a ransa. Gashi an turo jami'an tsaro sun zagaye sashen Uncle Nasir ɗin babu mai shiga kamar yanda akaima gidan Dad shima.
___________________
Ba ahalinsu Jawaad ne kawai a cikin ruɗaniba, duk ahalin dake da nasaba da waɗanan mutane yau hankalinsu baya tare da tunaninsu, anje kuma duk an zagaye gidajensu da jami'an tsaron sintiri, babu mai shiga babu mai fita. Waɗanda suka tsinci kansu a wani hali kuwa sai dai likitoci ake tura musu cikin gidajen suna dubasu.
Sosai ƙasarma gaba ɗaya take a hargitse bawai jihar da abin ya faru kawaiba, idan ka buɗe tv da redio babu wani magana saita wannan tashin hankali daya faru. Masu jaje nayi masu ALLAH wadai nayi, waɗanda suka jima suna zarginsu kuwa suka shiga maimaita ai dama a rina. Ƴan uwansu masu mu'amula dasu da suka rasa wasu mutanensu da suka rasu ta wasu hanyoyin tuni suka fara yayibo hujjoji da zarge-zarge suna ɗora musu (Kusan ɗan Adam kamar jira yake🤦🏻, abinda ma ba haka yakeba sai ya maidasa hakan🙄🚶🏻😏).
Masu ƙara gishi da magi a teburan masu shayi da gidajen suna da biki kuwa harda faɗin wai tukunya tukunya aka ringa fiddowa na farfesun mutane da gasashshen nama daga gidan😂, jini kuwa drom-drom sai kace wani mangyaɗa🤣. Aifa nayi ya samu a bakunan ƴan bani na iya, kowa burinsa ace shine ya fara kawo labarin🤒.
_______________________________
ƘARAMAR HUKUMAR GWANSU
_____________________________
Gidane madaidaici mai ƙyau, dan kuwa ko'ina na cikinsa mulmule yake da suminti, sannan an shafesa da fenti ruwan madara da ganye mai haske, ƙal yake da shara sai ƙyalli fasassun tiles ɗin da aka saka a tsakar gidan yake da ɗaukar ido. Yarone da zai iya kaiwa shekara uku ke barci kwance a ƙaramar katifa ta yara a tsakar gidan babu riga jikinsa saboda yanayin zafi, sai wani da bazai wuce shekara shida ba tsaye jikin ƙofar fita daga soron gidan yanata kumburi alamar wani abun akai masa.
Matashiyar mace da bazata gaza shekaru ashirin da huku ba ta fito daga matsakaicin kicin ɗin dake tsakar gidan ɗauke da tukunya alamar abinci ta kwashe, bayanta goye da jaririya ƙyaƙyƙyawa tanata barcinta hankali kwance. Tunkuyar ta ajiye inda alamu suka nuna wajen wanke-wanke ne tana mai harar yaron dake laɓe jikin ƙofar. “Wlhy kabari na kamaka a gidannan Fharhan sai na maka dukan da ko ubanka ba ganeka zaiyiba, karkazo ka ɗauki abincin su Innata ka kakai musu tunda ni na aikeka gidan su Musbahun har aka dakeka”.
Sake tura baki yayi gaba yana share ƴar ƙwallarsa, “To Umma ni kije ki amsomin ball ɗina, inaba hakaba ni bazankai abincinba kuma”. “Karka kai dan ALLAH kaga yanda zan kirɓa namanka a gidan nan mara mutunci..........”
“Yaya?! yaya?! dai”. Da gudu yaron da aka kira da Fharhan ya nufi mai maganar daya shigo yana faɗin, “Oyoyo Abbanmu”. Buɗe masa hannayensa yay ya shige jikinsa, ya ɗagashi sama yana dariya da faɗin, “Babana duk faɗan da nai maka akan yima Umma laifi bakajiba ko?”. Yaron ya ɓata fuska yana kallon Umman tasa dake tsaye tanama mijin nata kallon mamaki, yace mata wannan satin bazaizo