← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 168

Sashe 74

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

saurin ɗauke idona nai daga garesa ganin gajeren wandone a jikinsa wanda iyakarsa rabin cinyarsa. Bai sake cemin komaiba tsahon lokaci yanata safa da marwa a ɗakin, nidai gittawarsa kawai nake iya hangowa ban yarda na ɗago na sake kallonsa ba. Yazo gabana ya tsaya, hakan yasani ɗagowa na kallesa a tsorace, “Wa bincikenki ya nuna yayma Amina fyaɗe?”. Wani irin muguwar bugawa ƙirjina yayi akan wannan tambaya batare da nasan dalilin hakanba, maimakon na bashi amsa sai kawai na fashe da kuka.
      Tsura mata idanu kawai Jay yayi cike da mamaki? Yanzufa ta bashi labarin komai tiryan-tiryan, amma ya mata tambaya ta saka masa kuka. A dake yace, “Qaseem ne?”. Kasa bashi amsa nai saboda wani irin juyawa da kaina keyi tamkar ana bugamin guduma, da sauri nakai hannu biyu na riƙesa ina faɗin, “Ya ALLAH kaina”.
      Babu shiri Jawaad ya durƙusa a gaban gadon ya tarota ganin zata faɗi, saurin kwantar da ita yay ya kama kan ya riƙe cikin hannunsa yana janye nata hannun, addu'a ya shiga yimata jin kan ya ɗauki wani mugun zafi maiban mamaki, ga jikinta ya ɗauki wani irin rawa. Cikin matuƙar sarƙewar halshe take faɗin, “Kamin addu'a, kamin addu'a dan ALLAH, kaina zai fashe, wayyo kaina”.
           Tsahon lokaci yana mata addu'a har tai shiru, jikinma ya daina rawar da yakeyi, bai dainaba cigaba yay da mata har saida yaji zafin kan ya ragu sosai barci ya ɗauketa kafin ya miƙe, alwala yaje ya ɗauro yazo ya saka dogon wando ya kabbara salla.
       Kusan ƙarfe uku da rabn ta farka, nama manta a ina nake sai dana gansa a zaune da alkur'ani a hannu sannan na tuna. Yunƙurawa nai na tashi da ƙyar dan jikinna kam ciwo yake min, nima alwalar na ɗauro nazo bayansa na saka wani abin sallar na tada.
    Jay duk yanajin motsinta, sai dai baiyi maganaba saboda karatun da yakeyi.

      UBANGIJI mai rahama da jinƙai sai ya bama Bilkisu da Jawaad damar raya wannan dare da ibada har akai kiran sallar asubahi.

★★★★★★★

             Tunkafin ya dawo sallar asuba na gyara ɗakin na wanke har toilet, ina cikin gyaran falon saman ya shigo, dauriya kawai nakeyi dan wani irin barci nakeji fiye da zato, batare dana kallesa ba nace, “Ina kwana”. “Lafiya, waya saki wannan aikin?”. Kaina a ƙasa har yanzu nace, “Babu kowa”. Gaba yay yana faɗin, “Ki barsa iya nan kizo ki shirya na ajiyeki inada ayyuka da yawa yau”. ban iya cewa komaiba harya shige, dubana na maida ga agogon falon, ƙarfe shida da minti talatin da huɗu. Ƙarasa mopping ɗin nayi da sauri-sauri.

      Yanda tai gyaran gadon sai ya kasa daina kallonsa, da ƙyar ya iya ɗauke idanunsa, abu ya ɗauka ya fita daga sashen gaba ɗaya yana jaddadama Bilkisu tai wanka kafin ya dawo.
          Kayan sharan naje na ajiye na nufi ɗakin, a gaggauce nai wankan dan banason yazo ya iskeni, babban tawul da yafi kowanne girma na ɗauro na maida hijjabi jikina na fito, ina isa gaban mirror yana shigowa da sallama, ALLAH ya soni ban cire hijjabinba, na amsa masa kaina a ƙasa. Ledar hannunsa kawai ya ajiye saman gado ya nufi toilet yana faɗin, “Ga kayan da zaki sakanan”.

        Sauri-sauri na shirya cikin doguwar rigar dake cikin ledar ruwan sararin samaniya, sai sabon hijjab har ƙasa fari tamkar wata matar liman, na fita dan bana fatan ya fito ya samini a ɗakin.

___________________

             Misalin ƙarfe bakwai da mintuna arba'in Bilkisu da Jawaad suka fito daga sashensa.
     Addu'a naketayi a raina ALLAH yasa karmu haɗu da kowa, ALLAH kuwa ya amsa min ma muna fitowa ashe motar da zamu fita na a kusa. Da kansa ya buɗemin na shiga, sannan ya maida ya rufe ya zagaya mazaunin driver. Bazan ɓoye mukuba banason tuƙinsa, dan na kula ya iya zuga gudun tsiya a hanya. To amma babu yanda na iya.
      Haka muka tafi babu mai cema wani uffan a cikinmu, sai dai naji daɗi sosai yanda naga mun nufi masarauta kai tsaye. Yauma kamar ranar a ƙofar farko ya tsaya, waya ya ɗauka yay kira. bayan ya ajiye wayar ya juyo yana kallona.
          “Ya sunan anguwar da kuka zauna?”. kaina a ƙasa nace, “Bankaura”. “Zaki zauna a gida yau sai gobe idan ALLAH ya kaimu zaki koma aiki, ki dage da addu'a, kina dai ganin duk abinda ke faruwa”.

Kaina na jinjina masa nace, “Insha ALLAH, amma dan ALLAH miyasa jiya kace ban cancanci nai sadaukarwa ga Dad ba?”.  
      Shiru kamar bazai tankaba, kusan sakan biyar sannan ya juyo yana kallona, “Lokaci zai nuna mana komai, babu abinda zaki iya fahimta a yanzu sai ruɗani, kije idan lokaci yay zaki sani”. Kafin nace wani abu su Amaturrahman da Amintacciyar baiwar gimbiya sun fito a mota. Gaishesa sukai cikin girmamawa, ya amsa shima fuska aɗan sake yana faɗin, “Kucema Ummu ga amanarta nan ban ciba”. Dariya Amintacciyar baiwar gimbiya tayi tana faɗin, “Jiya kam ai tayi faɗa tamkar ta ari baki anƙi maido mata ƴarta”. Murmushi Jay yayi kawai yana ɗan kallon gefen da Bily take suna magana da Amaturrahman kafin ya ɗauke kansa.
         Sallama yay mana ya tafi, Muna shiga daga ni har Amaturrahman barci muka kwanta dan shi nakeji fiye da komai a yanzun.

__________________________

         Jay yana ajiye Bilkisu Office ya nufa, ayyukane fal kansa har baisan da ina zai faraba, yana zama abinda ya farayi shine bige-bigen waya, a kiran farko Umarni ya bada a nemo masa gidan da Bilkisu ta sanar masa sun zauna da iyayenta a Anguwar Bankaura, tare da ainahin maigidan da halin da gidan yake ciki yanzun. Kira na biyu kuwa Ainahin gidansu Baba makaho inda aka haufesa yasa a binciko masa shikuma a Anguwar Tudin Jarƙasa.
       Sunyi zaman awa biyu shida su Aliyu, duk da yaga ɗacin ran da Rose takeyi baibi takanta ba, bayan sun kammala ta buƙaci yin magana dashi, ca yay mata bashi da lokaci yanzun kam saita bari wani lokacin. Cike da takaici ta riga kowa fita. Haka ya cigaba da rage akainin gabansa.
         Misalin sha biyu yabar station zuwa Barrack ɗin sojoji da suka fara zuwa jiya kafin su tai jejin nan, ya samu ganawa da Lieutenant General a tsaitsaye dan ya iskesa yana shirin fita, ya sanarmasa wajen baba ƙaura yazo. Lieut G ya saka wani soja yayma Jay rakkiya har gidan da baba ƙaura yake zaune a cikin Barrack ɗin.
           Baba ƙaura ya tarbi Jay da murmushinsa mai tsayawa mutum a rai, bayan sun gaisa ya sake yima Jawaad ta'aziyya. Jawaad yay masa godiya akan gudunmawar da ya basu jiya. Fuska ɗauke da murmushi baba ƙaura yace, “Yaro bani nayiba ALLAH ne yayi”. “Hakane baba” Jawaad ya faɗa cikin sake tabbatarwa. shiru suka ɗanyi na wasu sakanni, baba ƙaura yace, “Mike tafe da kai?”. Ɗagowa Jay yay ya kallesa da ƙyau, ya tsufa sosai sai dai yana tare da ƙarfinsa, bashi da tsaho sosai sannan shiba wada bane, ya risinar da idanunsa yana faɗin, “Maganganunka na jiya baba na kwana juyasu a rai, sai dai har safiyar yau ban iya samo amsar ko guda ba, baba mika sani a kanmu?”. Murmushi baba ƙaura yay idonsa akan Jawaad, yace, “Yaro bansan komai a kanku ba, hasalima jiya na fara ganinku a iya tsahon rayuwata, kowane irin mutum a duniya yanada baiwarsa, ni tawa baiwar kenan, fahimtar wasu abubuwa daga mutane, akwai mutane masu irin wannan baiwar tawa da yawa a duniya, sai dai mafi yawansu sunfi zaɓar aikata saɓon ALLAH da tasu damar, sai kaga mutum ya zama ɗan tsubbu ko naɗama kansa wani girman da zai halakar da mutane daga barin ALLAH, ko ya maida baiwar tasa ga zalunci da neman duniya. wlhy kaji na rantse maka bansan komai daya shafekuba face abinda UBANGIJI ya bama idanuna ikon gani tattare daku jiya.....”
      Cikin jinjina al'amarin baba ƙaura Jay yace, “baba ko zamu iya sanin abinda ka fahimta ɗin?”
       Murmushi Baba yay da faɗin,  “Yaro minene sunanka?”. Jay yace, “Jawaad”. “Masha ALLAH, malam Jawaad bawani abune na gani a rayuwar kuba, domin kuwa ƙaddarar da duk ke cikin rayuwar kowanne ɗan adam wannan ɓoyayyen sirrine daga taskar ALLAH, abinda ALLAH ya bani ikon gani tattare daku kawai shine rayuwarku na ɗaure da wani al'amari mai girma, sannan kunada taurari masu ƙarfin haske da suka hana duhun dake zagaye daku tasiri, dan har na waccan yarinyar sunfi nakama haske, abinda nazarina ya bani bayan faruwar abubuwa a dajin nan shine akwai sihiri mai ƙarfin gaske jingine da jininku, su wanene sukai muku? Miye dalili? Saboda mi? Daga yaushe ne? Shine ban saniba sai abunda ALLAH yasio sanar daku nan gaba”.
Chapter 74 · 0% Book details