← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 168

Sashe 67

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ya ɗago idonsa daga rubutun da yake yayma Jabeer kallo ɗaya ya ɗauke, “Ka buɗe mugani” ya faɗa hankalinsa akan Computer ɗin gabansa, sai dai sam bama ya fahimtar aikin da yakeyi ɗin.
        Buɗe  takardar Jabeer yayi, cikin nutsuwa yake bin komai da kallo daki-daki, a firgice ya kalli Jay cikin rawar harshe yace, “Ka duba wayarka, alama ta nuna kaine wanda ya turama saƙo na ƙarshe ta manhajar WhatsApp a ranar asabar da ƙarfe shida da mintuna talatin da huɗu (6:34pm), sai kiran wayoyi barkatai da akai masa amma babu wanda ya ɗaga a ciki, kuma wayardai tana a cikin jejin nan da muka gani jiya, abin farin cikin kuma har yanzu layin yana kan waya yana aiki alamar wayar tana a kunne”. Duk saurarensa suke, yayinda Jay keta ƙoƙarin duba saƙon Gimba, tabbas kuwa ya tura masan, amma sam hankalinsa bai kaiba saboda hidimarsa bata barima ya leƙa wata kafar yanar gizo ba a gaba ɗaya satinnan daya gabata. Babu wanda hankalinsa bai tashiba a cikinsu da wannan voice note na gimba, tuni jijiyoyin kan Jawaad duk sun miƙe ruɗu-ruɗu, muryarsa cike da damuwa yace, “Hafiz kaima Sir Ahmad magana ina buƙatar helicopter”. Cikin matsanancin tsoro suke kallonsa su duka, Aliyu yace, “Boss wannanfa dajine mai haɗarin gaske da ko soji suna masa shiri na musamman kafin su shigesa, idanma sun shigan ƙalilanne a cikinsu ke dawowa da ransu, baka tunanin ma wayar aka kai can dan a kauda mana hankali”. Cikin rufewar ido Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa, “Aliy!! ya kakeso nayi ne shin? Nabar yaron mutane mai mata da ƴaƴa har uku da uwa da ƙannen da suka dogara dashi a hannun waɗanda suke azzalumai?. Aliy ta dalilinafa suka kamashi, wlhy kaji na rantse maka sai ƙafata ta taka wannan jejin koda kuwa Gimba bayacan kokuwa nima ajalina nacan!”.
      Babu wanda bai firgita da alwashinsaba a cikinsu, sunaji suna gani ya fice daga office ɗin, basu da zaɓin daya wuce goya masa baya dan wannan shine alƙawarin da suka ɗaukama kawunansu duk rintsin da ɗayansu zai shiga suna tare dashi ɗari bisa ɗari. Cikin mintuna ashirin suka samu amsar helicopter daga hukumar sojoji tare da soji biyu da zasuyi musu rakkiya bisa tsayawar Sir Ahmad.
      Office ɗin Jay ɗin dai suka koma suna tsare-tsaren yanda zasu tunkari Jejin.

         A dai-dai wannan lokacin motar masarauta ta kawo bilkisu, godiya naima drivern da ko sunansa ban saniba na fice, shi kuma ya juya inda ya fito.
         Kaina tsaye office ɗinmu na nufa, a raina sai jina nake wani iri idan na tuna waifa akwai aure a kaina yanzun, aurenma na Boss. kowa yazo sunata aiki, shigowata yasa sukaimin caa da ido har gabana na faɗuwa da tunanin shikenan na mutu kowa yasan komai. Ummie ta taso da gudu ta ɗaleni tana murna, “Babie ALLAH banyi zaton ganinki ba yau a office”. Murmushi nai mata ina amsa gaisuwar sauran daketa min yaya jiki, sai naji daɗi da Ummie bata sanar dasu komaiba sai rashin lafiya.
         Na zauna a mazaunina idona akan Ummie da itama ta jawo kujerarta jikin table ɗina ta zauna. “Yanzu angonki yazo ya gama haukatamu da masifa anan”. Ta ƙare maganar da dariya. ɗan hararta nai na ɗauke kai bance komaiba, danni kam dama ta ambatosa jinai gabana ya faɗi. na shiga duba aikin dana bari,  Ummie kuwa na cigaba da tsokanata dan na tanka amma na shareta kamar banajinta.
     Dawood daya shigo yanzun ya ƙaraso gabana yana faɗin, “Bily Boss na kira”. Babu shiri na ɗago ina kallonsa, shiko yay ƴar dariya yana zama a kujerarsa dake kusa da tawa, “Kitafi da addu'a a baki dan wlhy yau a sama yake, yanzu naje office ɗinsa jinai kamar nai fitsari a tsaye da yanda yaketa masifa”. Ban iya cewa komaiba, Banida ikon kuma cewa bazanjeba, dan haka na miƙe cike da haushi na fita har Ummie namin dariyar ALLAH yasa aiki za'a bani dan taga kwana biyunnan hutawa kawai nake tunda bana zuwa office, ban kulataba na fice abina.
         Ina fitowa na hangesu sun fito tamkar zakuna, kowa fuskarsa a ɗaure musamman ma boss, gabana ya faɗi, a fili nace, ‘Ni balki ina kuma zamuje haka?’ bani da mai bani amsa na isa inda suke, babu wanda ya saurari gaisuwata ma a cikinsu, Jabeer ya nunamin na shiga mota da boss yake, gaba na buɗe na shiga

, dai-dai da isowar Rose wajen, hararata tayi tana jan tsaki, ta buɗe indasu Aliyu suke ta shiga, Hafiz kuma ya shiga kusa da Boss.
       Mun fara tafiya Hafiz ya miƙomin bindiga, juyowa nayi zan amsa na samu damar satar kallon boss, kansa a duƙe yake yana sakama bindiga alburusai, amsa nayi na juya zamana nidai a raina ina addu'ar ALLAH ya maidomu lafiya...............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

 [12/17/2020, 10:03 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Ƙwai cikin ƙaya
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
Page 30

................Daga station Barrack muka nufa, acan muka iske jirgi mai saukar ungulu dake jiranmu.
     Motar na tsayawa Jawaad da Hafiz suka fita, kafin bily tai yunƙurin fitowa Hafiz dake kallon Jay yace, “Boss amma Mami jiya ta fito asibiti miyasa baza ai mata afuwa da tafiyarnan ba?” Jay dake daƙilar waya ya ɗago yana kallon Hafiz, sai kuma ya dafa kafaɗarsa da hannunsa da ya ciro aljihu, “Nasan tana buƙatar hutu Hafiz, sai dai nima bansan miyasa nakejin kamar tafiya tare da ita yanada nasaba da nasararmuba”. Hafiz ya jinjina kansa yana murmushi, shima Jay ɗin murmushi yayi ya ɗauke kansa.
     Ganin sun fita nima na fito, ido muka haɗa da boss dake ƙoƙarin saka waya a kunne da alama kira yayi, duk yanda naso janye nawa na gaza, dan tamkar ya ƙulleni ne da idanun nasa yayi. Murya ƙasa-ƙasa tamkar mai gudin wani ya jisa yace, “Koma ciki ki jira”. Ƙasa nai da idona ina sauke ajiyar zuciya, na buɗe motar na koma ciki ina kallonsu. Sojoji uku ne suka ƙaraso wajen, daga inda nake banajin mi suke faɗa su da su Oga Jabeer, boss dai na gefe yana waya har yanzun.

      Bayan Jawaad ya kammala waya da Alhaji babba akan a tayasu da addu'a shima nufar inda su Aliyu suke tsaye tare da sojoji ukun nan yayi, cikin mutunta juna suka gaisa, wanda ya kasance babba a cikinsu mai yawan shekaru kuma ya kalli Jay yana faɗin, “Jejin nan jejine mai haɗari, Sojinmu sunsha wahala sosai a cikinsa kafin ALLAH ya kawo mana ɗauki ya haɗamu da Ƙaura na bakin kadarko, a bakin jajenin yake rayuwa shida iyalansa, sannan a cikin jajen yake farauta, sai dai wani babban al'amari ya faru a shekaru biyu da suka wuce wasu azzalumai suka tashi gidansa dukkan iyalansa babu wanda ya tsira sai shi, shima dai ya rasa hannunsa guda, daga nan ne muka ɗakkosa mukazo dashi nan yay jiyya har ALLAH yasa ya warke, yaso komawa jajenin saboda ya saba sosai dacan, yakan faɗa mana zama a cikin gari shi baya masa daɗi, to adai taƙaice har zuwa yanzu da nake muku magana bamu barsa ya komaba, dan yama tsufa kawai jarumtace irin ta mutan da da ALLAH ya azurta da sani.........” isowar ƙaura da wani soji wajen ya saka Lieutenant General Mubarak Kambawa yin shiru, ya zubama waje ɗaya ido. Duk juyawa su Jay sukai suma suna kallon inda yake kallo, tsohone mai shekaru da yawa wanda basusan adadiba, babu wani gashi a jikinsa da zaka iya gani baƙi sai wanda UBANGIJI ya ɓoye. Yana sanye cikin kayan fatu, ya ɗaura fatar zaki a ƙasa yay riga data damisa wadda take tamkar ƴar shara, dan kai kawai aka fitar sai gefe da gefe akai mata maɗauri, yana rataye da jikkar fatar kura a wuyansa, sai dai bashi da hannu guda. Daka gansa kaga ƙauran kuwa. Yanda sukaga lieut.. General na gaidashi cikin girmamawa yasa suma suka gaidashi da girmamawa, dan koba komai ya wuce uba sai dai kaka. Dattijo ƙaura dake amsa musu idanunsa kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa bayayi, ya saki murmushi yana kauda idonsa daga kallon Jay ɗin. babu wanda kallon bai bama mamakiba hatta lieut.. General, dan haka yaja Ƙaura gefe guda.
       “Baba nasan baƙwa kallon banza, akwai matsalane? Dan na lura ka kafe yaron can da kallo har  murmushin ka ya kasa ɓoyuwa” murmushin yanzuma Ƙaura ya sakeyi tare da juyawa ya kalli Jay da Jabeer ke taimakawa yana saka bullet proof jacket a jikinsa kafin ya sake maidowa ga lieut.. General yace, “Shima sojan kune yallaɓai?”. Lieut... General yace, “A'a baba, sune nai maka bayani ai zakuyi tafiyar”. “Oh na shafa'ane wlhy, kasan ƙwaƙwalwar yanzu sai a hankali takan manta wasu abubuwan”. L. General dai murmushi yayi kawai, dan yasan wanene baba ƙaura, yakuma tabbata akwai abinda ya gani tattare da Jawaad, amma tunda yake wani kakkaucewa bayason ya sanine, dan haka ya ture maganar Jawaad gefe ya shiga masa bayani akan taimakon da sukeso yayma su Jay saboda sanin sirrin jajen da yayi. Sunɗan tattauna sannan suka dawo inda su Jay da suka gama shiryawa tsaf suke harda Bilkisu data fito bisa umarnin Jawaad bayan yaje da kansa har cikin mota ya taimaka mata ta saka bullet proof jacket ɗin itama suka dawo wajen tanata sinne kai saboda kunya, yayinda Rose ta shaƙa tai fam da haushi tamkar zata f
Chapter 67 · 0% Book details