← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 168

Sashe 7

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kawaiba, da jiyansu data shuɗe ta zama tarihi, tun haɗuwata dake ta farko na fahimci kinada wata baiwa ɓoyayya da bakowa ALLAH ya bama ilhamar hasasotaba, daga lokacin kuma da muka kasance ma'abota kusanci na tabbatar da zamu ribantu da junanmu, sai dai taki ribar da zamu samu saita ɗara tamu muhimmanci da amfani a garemu, k.......” “Sam ban gamsu da bayanankiba Ummie” na faɗa cikin ɗaga mata hannu saboda yanda ta kwararo zance. “Miyasa kikace haka Bily?”. “Banason faɗa kice na maida hannun agogo baya, mubar zancen kawai watarana ma ƙarasa, mizai hana kije wajen Doctor kimasa maganar ya sallamemu haka, banason zaman asibiti a rayuwata”. kafin Ummie ta samu damar yin magana aka turo ƙofar aka shigo da sallama, Dad ne, hakanne ya sakani faɗaɗa murmushi akan fuskata, saurin tashi tsaye Ummie tayi ta bashi kujerar da take zaune akai, kafin ta gaidashi cikin girmamawa. Nima gaidashi nai, ya tambayeni jikina cike da kulawa. Naji daɗin ganinsa sosai, nakumaji daɗin alhinin daya nuna akan halin dana tsinci kaina, sai dai nayi ƙoƙarin daƙile alwashinsa na buƙatar nabar aikin, danshi kam ya fara tsorata dajin cewa wannan aikin namu da gaske bai dace da ɗiya mace ba, musamman ma irina da nake yarinya ƙarama. Cikin murmushi da girmamawa a garesa nace, “Dad addu'arku kawai muke buƙata, idan har zamu cigaba da sakawa a ranmu mata basu dace da irin kowanne aikiba saboda matsalolin cikinsa, to lallai yankinmu bazai daina fuskantar koma bayaba, hakama sauran mata masu tasowa bazasu daina fuskantar ƙalubale na daƙile burinsu akan kansu da ƙasarsuba”. Sosai Dad yay murmushi, ya shafa kaina da cewar, “ALLAH yay miki albarka kinji, lallai tunaninki ƙyaƙyƙyawane Bilkisu, ALLAH ya kiyaye gaba to, nabiya ta wajen likita, ya baki sallama yanzu haka, sai dai ya tabbatarmin daga office ɗinku an turo ɗaukarki, ɗan aiken na hanya kuma, dan haka ni zan wuce, dama daga nan airport na dosa”. “Dad badai har zaka sake wata tafiyar ba?”. Murmushi yaymin mai ƙayatarwa yana jinjina kansa, “Hakane bilkisu, masu iya magana nacewa na kwance baiga gariba, muma addu'arku muke buƙata tamkar yanda kuke buƙatar tamu kinji, wannan karon kuma bazan jimaba, dan sati ɗaya kacal zanyi, idan na wuce hakan kuwa bazan zarta gomaba”. “To Dad ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada nasarar abinda za'a fita nema mai albarka”. “Amin ɗiyata, nagode sosai”. Itama Ummie tai masa addu'a, ya amsa mata da kulawa kafin ya ajiye mana kuɗaɗe masu kauri ya fice daga ɗakin”. Koda Dad ya fice fuskarsa ɗauke take da murmushi tare da ɗunbin tausayin yarinyar a ransa, shidai haka kawai ALLAH ya dasa masa ƙaunarta a zuciya, yaɗan juya ya kalli ɗakin yay murmushi kafin ya cigaba da tafiya........ Gaff sukaci karo da mutum, Gimba yay saurin fara jero kalamun ban haƙuri a gareshi. Batare da Dad yay masa wani kallon arziƙiba yace babu damuwa, yay wucewarsa. Binsa da kallo Gimba yay cikin wani tsagwaron mamaki da juya abinda ya gani a cikin zuciyarsa, sarai ya gane mahaifin matar Boss ɗinsace ta da, kuma mijin Gwaggonsa, afili yace, “To mikenan? Mi yazo yi nan? Minene ma'anar wannan kallon da yayma ɗakin nan? Minenema haɗinsa da ɗakin?”. Bashi da mai amsa masa wannan tambayoyin, dan haka yaja bakinsa ya tsuke dan bai dace ya shiga abinda babu ruwansaba, Boss na yawan masa nasiha da kiyaye abinda ba huruminsaba koda a inane, kuma koda akan minene. A ɗaki kuwa bayan fitar Dad yabo Ummie ta shiga jero masa, yayinda Bilkisu ke tayata tare da ƙara buɗe ƙyawawan halaye na Dad waɗanda Ummie batasan da suba. A haka gimba yay sallama a ƙofar ɗakin, sai da na suturta jikinna kafin mu bashi damar shigowa, dukda bamusan shiɗin waneneba. Mun gaisa da juna cikin girmamawa, sannan ya kora mana bayani akan cewar Boss ɗinsa Jawaad ne ya bada umarnin yazo yakaimu gida dan an bani sallama. Kallon juna mukai ni da Ummie, kowanne baki a hangame, sai dai bamu da damar bin ba'asi akan wannan umarnin, dan kuwa dai yana sama damu, mizaisa mu tuhumesa da abinda bamu da bakin zarensa. Haka muka shiga kimtsawa har Doctor ya shigo, ya ƙara mana bayani akan yanda zan kula da cuwon saboda gudun karya zarta haka, tare da kwanakin da zan ringa zuwa asibitin domin tabbatar da ingancin kulawar da nake bashi. ___________________________ JAWAAD ___________________________________ Zaune suke a office ɗinsa su huɗu, aminan juna kenan da sukejin kansu jini guda, sannan abokan amanar juna masu taruwa wajen magance matsalolin juna da ƙarfin zuciya dana aljihu. Sunyi nisa cikin tattauna abinda ya faru a yammacin jiya ne, domin dai da gaske Jabeer ne ya haɗa cinkoson jiya da gangan saboda son cimma burin kama tsagerun da suka biyo, amma sai suka ɓace musu, ganin zasu rasa wannan damarne Jawaad ya bama Jabeer umarnin nuna ƙwarewarsa kasancewarsa masani sosai ta ɓangaren na'ura mai ƙwaƙwalwa. A take kuwa ya nuna gwarzantakar tashi, ya haɗa cinkoson da su Bilkisu suka riska saboda tabbacin nan kaɗaice hanyar da masu laifin zasubi su tsira da wuri, ita kuma Bilkisu tayi tarar aradu daka akan abinda bata da tabbaci. Aliyu ne ya fara faɗin, “Maganar gaskiya na daɗe banga jarumar mace mai ƙarancin shekaru irin yarinyarnanba, a yanda labari ke fitowa da ga bakunan mutane na yanda ta tari motar mutanen da suka fara ganin farkon al'amari da yanda ta tunkari mutanen zai baka tabbacin da gaske tanada kaifin zuciya akan aikinta”. Cikin jin jina kai na tabbaci Jabeer yace, “Lallai maganarka tana akan gaskiya wlhy Aliyu, nifa abindama ya sake birgeni da ita shine, dukda mugun ciwon da taji, amma saita dake dan tabbatarma da duniya lallai ita ma'aikaciyar tsaroce ta gaske ba ƴar burgaba”. Fuska shimfiɗe da murmushi Hafiz yace, “Sosaima kuwa Jabeer, dolene ƙaimin yarinyar ya burge kowa, dan kuwa da ƙwaƙwalwa tai amfani wajen fahimtar motar tana da alaƙa da rashin gaskiya, ta kuma nuna himmarta na sadaukarwa koda hakan na nufin zata cutu a wajensu, ta cancanci kowanne irin jinjina ga hukumarnan tamu, musamman idan akai la'akari da shigowarta cikin aiki jiya-jiya kawai, bana tunanin kuma an taɓama fita da ita wani aiki makamancin haka koda sau ɗaya”. Duk wannan zance da suke faman zubawa akan yabon Bilkisu da jinjina himmarta Jawaad na zaune shima a cikinsu, yana sanye cikin baƙaƙen suit kamar sauran da a kullum suke ƙara masa kwarjinin kasancewarsa ma'aikaci, sai dai ya cire rigar sama, yana zaune ne kawai da baƙin dogon wandon da rigar ciki mai dogon hannu kalar kore mai haske, maɓallan rigar uku a buɗe, hakanne ya bayyana singlet ɗinsa kaɗan fara tas, yaci zanzaro, ya tsuke ƙugunsa da belt kalar shirt ɗinsa. Abinda zai baka mamaki ko tari bai yiba akan maganar, baima nuna ya fahimci mi suke tattaunawarba sam, yana zaune ne ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, kansa sunkuye yanata faman danne-danne a cikin tab... ɗinsa ta kamfanin Apple, sam fuskarsa babu wata walwala, kuma ba'a tsuke take sosaiba. Aliyu ne yakai dubansa garesa, tare da faɗin, “Ka fuskanci abinda muke tattaunawa game da yarinyarnan kuwa Jay?”...............✍
Chapter 7 · 0% Book details