← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 168

Sashe 23

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assalamu alaikum.
Inason naɗanyi bayani da nake fatan a fahimceni, akan maganar aikinsu Jawaad, inason mai karatu ya fahimci wani abu anan, aikin da muka dangantasu dashi bawai yana nufin ainahin abinda ya shafi ma'aikatan zahirin bane, bamusan komai da ya shafesu ba, tayaya zamuce komai nasu sai ya shigo labarinmu, domin ba'akan hakan muke rubutu ba, da yawanmu ma idan za'a tambayemu bazamuce munsan waɗanan ma'aikatanba kai tsaye, domin su aikinsu bawai a bayyane yakeba kamar ƴan-sanda da dai sauransu da suke cikinmu ba, aikine na wanda kai kanka idan ba wani daliliba bazaka taɓa ka gansu suna yawo gama gari ba ko wani aikinsu a bayyane, so na danganta waɗanan jaruman littafine da hakan saboda mutunci da himma da ƙwazo na irin jami'anmu da mu kanmu bamu saniba, matasanmu kuma su zama masu himma dason bama ƙasarsu gudunmawa da zuciya ɗaya a kowace ƙasa suke ba lallai sai tamu ba, tom inaso ku kalli wannan kawai a matsayin labari bawai lallai abinda yake a zahiri ba, ko yake lallai mu bibiya, matsayinsu, misukeyi? Mizasuyi? Duk iyakarsa labari irin na marubuci {ƙirƙira}, bani da hurumin shiga abinda bani da lasisi a kai, domin bamma sani ba, waɗanan jami'an littafine bawai na zahiri dake aiki a ƙasarmu ba, idan kun kula sam babu wani sunan gari dake nunama a ina suke, ko a wane waje suke, musa a ranmu kawai ƙirƙirarren labari muke karantawa, ilimantarwa, nishaɗi, da faɗakarwa, ba akan kowaba, domin ba'akan kowan mukeyi ba, duk abinda zamu iya ganin yaci karo da waccan rayuwar ta zahiri to kawai fiƙira ce irin ta marubuci bawai dan inada ilimin sani ba ko bibiya balle bincika, ina fatan duk wanda ke bibiyar wannan littafi a ko'ina yake zai kasance maiyin ƙyaƙyƙyawan fahimta akan inda muka dosa, sannan abinda kake ganin na karkace ko shiga hurumin da banawaba ina fatan zakuyi gaggawar dawo dani hanya, ALLAH yasa mu dace, ALLAH kuma ya ƙarama dukkan jami'an tsaronmu lafiya da ƙwazo da nagarta a duk duniyar da suke.🙏🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

Billyn Abdull:
Page 10

    ............‘Kutumelecy’ na faɗa a cikin raina ina saurin janye idanuna dana ware a kansa da tsaida taunar cingam ɗin da nakeyi lokaci ɗaya, ganin yanda ya tsatstsareni da muggan idanunsa.  Zungurin ƙafata dana ɗora saman tebir ɗina Ummie tayi.
     Kallonsa na sake sata sai naga shima idanunsa yanzu akan ƙafar tawa suke harma da sauran ƴan uwana, da sauri na sauke ƙafar ƙasa na nutsu kamar yanda kowa yayi. Bai tankama kowaba ya ida takowa tsakiyyar ɗakin yana binmu da kallo daki-daki, har tsawon mintuna biyu muna a haka tamkar ɗan doka da ƴan gidan kallon ƙwallo ko ɓarayin agwagi, nidai sai faman jan addu'a nake saboda jin yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri tamkar ko yaushe idan na samu kusanci da shi.
     Ganin bazai tankaba sai muka shiga gaisheshi ɗaya bayan ɗaya, hannu kawai yake ɗaga mana amma bai sake kallon kowaba baikuma amsa mana da bakiba. Yaja kujerar dake gaban tebir ɗin Uchie ya zauna, bamusan mi suke tattaunawaba har kusan tsawon mintuna sha biyar kafin ya miƙe ya fice. Yana fita muka shiga sauke a jiyar zuciya, yayinda wasu suka shiga gulmarsa musamman ma matan cikinmu, nidai sabon cingam na ɓare na jefa a baki na cigaba da sabgar gabana.

________________________________

               A gidan su Jawaad kam taron meeting Mom ta tara da ƴan uwanta, sunɗau tsahon lokaci suna tattaunawa akan Jawaad da maganarsa da Shahudah, duk da dai da farko Uncle Nasir yaso bijirewa, a cewarsa suma sunada ƴaƴan da zasu bama Jawaad ɗin ai ya aura. Shahudah ta kiya musu hankalin da bai kamata su sake sakata a sabgarsu ba.
       Kuka mama Atika ta fasa musu, tare da ɗakko musu maganar data saka suka nutsu waje guda.
        “Munsan Sabira tayi laifi da tafka kuskure a baya, amma kuyi haƙuri munada tabbacin zuwa yanzu ta magantu za'a samu gyara musamman idan mukai dubi da yanda take son yaron, amma ni na yarda da shawarar Nasiru, mu fara ma Jawaad maganar auren wata a cikin yaran gidannan, idan ya nuna rashin amincewa saimu tirsasashi ya maida Sabira ɗakinta, dan baikamata mu zubamasa ido yana yawo sakaka babu aureba, shekararsu kusan biyar kenan da rabuwa, amma yaƙi aure, inba neman matan banza yaron nan yakeba yaza'ai mutum mai lafiya kamarsa ace yanaƙin aure?, su waɗancan dangin uwar tasa sakarkaru da yake tsoronsa sukeji sun gaza masa magana kuma, tomu bai kamata mu saka masa idoba, dan kuwa mune duniya zata zaga basuba, amma yaya kuka gani? Danni dai shawarace na kawo matsayina na uwa a gareku, da Badiyya nada isashiyar lafiyama tare zamuyi muku, yanzu saiku zauna ku yanke shawara a tsakaninku” ta ƙare maganar da tashi ta fice daga falon.
     Duk binta sukai da kallo harta fita, Uncle Sulaimam ya sauke numfashi yana faɗin, “Nidai ƴan uwana na yarda da maganar mama, dan nidai zaman Jawaad bayamin daɗi a haka, da Abdul-aziz nada rai bazai zubama gudan jininsa ido kamar yanda mu muka kasa riƙe amana mukaiba, duk da bana zargin Jawaad da neman mata, dan mu shaidane akan tarbiyya da sanin yakamata na yaron nan”. Duk shiru sukai basu ce komaiba, wasu na hararsa ta gefen ido wasu na ƙunƙuni a cikin rai, dan suma sunsan ƴaƴan Mama Badiyya sam nasa tare da burinsu a gidan, su kaɗaine masu ƙaunar Jawaad dan ALLAH badan dukiyarsaba. Jin shirun yayi yawane ya saka Mom yin magana. “Nima na aminta da maganar mama, kuma ina goyon bayan ɗan uwana Sulaiman”.
         Daga maganar Mom sai kowama ya fara faɗar abinda ke ransa, daga ƙarshe dai suka ajiye shawara akan zama da Jawaad ɗin idan ya dawo aiki da wuri yau, kokuwa weekend idan ALLAH ya kaimu.

_________________________________

             A makare yau Jawaad ya tashi a wajen aiki, saboda fitar da sukai shi da Hafiz zuwa wani waje da yamma, basu dawoba sai bayan magriba, akwai abinda zai ɗauka a office shiyyasa suka dawo, amma da daga inda sukaje gida zai wuce. Bayan ya tattaro abinda zai ɗakko a office ɗin nasa sai yaga lokacin sallar isha'i ma yayi, dan haka suka tsaya sukai a station ɗin.
           Koda suka fito yunwar dake cin cikinsa yasa yace su tsaya wajen wani haɗaɗɗen gashin kaji, gimba ya amsa masa da girmamawa.  gimba ne ya fita domin

amsowa, kasancewar wajen ba baƙonsu bane akaima gimba tarba ta sanayya, kamar yanda Jawaad ya bashi umarni takeaway biyu akayi sai fura da yogurt masu sanyi aka saka ɗaɗɗaya a ciki, gimba ya bada kuɗin sannan ya dawo mota suka ƙarasa gida.
         Ganin da sauran mutane da keta shigi da fici a sassan gidan sai ya bashi mamaki, a ganinsa dai tunda anyi addu'an bakwai mikuma mutane keyi tunda ba taron biki bane. Saurin kauda abin yay a zuciyarsa dan a ganinsa hakan ba huruminsa bane, yaso shiga sashen Uncle Usman ya gaida Mama Zainab matarsa kamar yanda yakeyi kullum tunda akai rasuwar, sai dai a matuƙar gajiye yake, ga masifaffiyar yunwa dake cin hanjinsa.
         Tare suka shiga sashensa da gimba dake ɗauke da tarkacensa, bayan ya ajiye masa a falon ƙasa yay masa sallama ya fita, shima bai iya ƙarasawa bedroom ba ya yada zango a falo, sai da ya huta na wasu mintuna sannan ya miƙe ya haura sama, duk da yana buƙatar fara cin abinci haka ya daure, dan shi mutumne mai yawan cin abinci, idan bai samu bane dai yakanyi haƙuri kawai. Ɗakin barcinsa ya ƙarasa ya watsa ruwa, kusan ƙarfe tara ya fito tsaf dashi sai baza ƙamshi yake. Ya shiga kicin ya ɗakko kofi da filet, a falon ƙasa ya zauna ya kunna tv domin kallon labarai, yana kallonne yana cin abinci, lokaci-lokaci kuma yakan amsa waya idan an kirashi, ya daɗe zaune a falon har aka kammala labaran kafin ya miƙe yay ciki dan yana matuƙar buƙatar hutawa.

SHAHUDAH

      Saboda son haɗuwa da Jawaad yasa yau taƙi binsu Mom gida, a cewarta nan zata kwana, Mom bata hanata ba, suka tafi ita da Aamilah kawai saboda Salman ne yazo ɗaukarsu dama ba driver ba.
     Wajen ƙarfe goma ta kammala kwalliyarta, tai shiga cikin kayan barci masu taushi da ƙyau, dan sunyi masifar fidda mata surarta, sai ƙamshi take kamar jikar gidan mai turare, a ranta ta ƙudiri aniyar maido hankalin mijinta kanta yau, dan ta gaji da wannan wasan ɓuyan da sukeyi, ta kuma shirya karɓar cikin da yake buƙata. (Karku manta Shahudah batasan Jawaad ya saketa ba fa😥🤦🏻, ɓoye mata shine kuskuren dasu mom suka tafka).
     Hijjab ɗin mama Atika da ya kai mata har ƙasa ta ɗauka ta saka, babu kowa a sashen na mama Atika, itama tayi barci ma tun ɗazun, kai tsaye Shahudah ta nufi sashen Jawaad tanata zuba murmushi, dan ita kaɗai tasan abubuwan data shirya masa, yau ɗinan basai gobeba sai ta zautar da gayen nan, ta sake sakin tattausan murmushi lokacin data murɗa ƙofar taji ta buɗe. Jawaad ya manta shaf bai rufeba ya haye sama, sai da ta gama ƙarema falon kallo, komai tsaf tamkar ba namiji ke zauneba, tasan Jawaad yanada tsafta, sam bayason ƙazanta, duk jin kan nan nasa baya ƙyashin tashi yay shara yay morping wa sashen,, ya samu wannan horonne a zamansa da kakarsa Mama maryam, hatta da girki Jawaad ya iya, kawai rashin isashen lokacin kai ne ke hanashi yi. batasan miyasa bayason masu hidimaba. Ta sake sakin murmushi kafin ta fara taka steps ɗin a hankali tana wani yauƙi saikace tarwaɗa, a falo ta cire hijjab ɗin ta jefa saman kujera, ta kuma gyara rigarta da gashinta sannan ta nufi hanyar ɗakinsa.
Chapter 23 · 0% Book details