← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 168

Sashe 73

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

man gafara a cikin zuciyarsa. Ya ɗau tsayin mintuna goma a haka kafin ya juya ya kalli Bilkisu, ɗauke kansa yayi murya cike da ɗaci yace, “Miyasa kika dawo gidan su Hudah da zama?”.
       Banyi tunanin ya fahimci idona biyu ba har yanzun, na rumtse idanuna da ƙarfi ina sauke ajiyar zuciya, batare dana motsaba nace, “Ƙaddarar maraici”.
      Idanu Jay ya tsurama bayanta, tsawon sakanni ya ɗauka a haka kafin ya sake ɗauke kansa daga gareta, “Ina dangin mahaifinki suke? Misa basa cikin rayuwarki?”.
     Hawayene masu zafi suka silalomin, dan yau kan Boss ya taɓomin inda yafi ko'ina ciwo a zuciyata, zaune na tashi na jingina da fuskar gadon nima, hawaye na ƴar tseren fitowa na shiga bashi amsa kai tsaye, dan na fahimci so yake kawai yasan wacece niɗin kafin zuwana gidan su aunty Shahudah, batare dana kallesaba nace, “Har iyayena suka bar duniya su dukansu basu taɓa sanar dani wata matsala dake tsakaninsu da duk danginsu ba, dukda nasha musu tambaya sai dai babu wanda ya taɓa bani amsa ƙwaƙwƙwara a cikinsu, kullum amsarsu a gareni itace, (komai da lokacinsa, idan lokacin yayi zan sani) tun ina damuwa da abun harma na ciresa a zuciya, dama ba komai ke sakani kwaɗayin son jiba sai yanda nake ganin sauran yara ƴan uwana sukan shirya a ranakun juma'a da Sallah suje gidajen danginsu, sai dai ni daga gareni ba haka baneba, tunda na girma nai wayo a gidan haya mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in na buɗi ido na ganmu, bara dai na maka gwari-gwari zakafi farimtata.
           Ni dai sunana Bilkeesu ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.
A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki. A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za'aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita. Sana'ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau'in ɗinki tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa. Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama. Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu'amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera kwana biyu babu wanka.
Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi na gansu, dan har takai mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa.  mahaifina da mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa, hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance n

akasassu, inhar za'a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kake tunanin ba za'a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci ba?. Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba'a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba. Badan bani da ƙoƙari bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum..........................

          Tunda Bilkisu ta fara bama Jay labarin rayuwarta idanu kawai ya kafeta dashi ko ƙyaftawa bayayi, ko sau ɗaya bai katseta ba har saida takai aya, fuskarta shaɓe-shaɓe da haye ta juyo tana kallonsa. “Wannan itace asalin Bilkisu da take gabanka, mai rawa da bazar Dad, badan shi ba babu mai sanin wannan BILKEESUN bare ya bibiyi tarihinta, Yah Jawaad, bazan bijirema aurenkaba, dan har yanzun bansan asalin ƙullashi ba, sai dai kasani rashin auren Yah Qaseem tamkar butulcine daga alkairan Dad a gareni, ya ɗaukeni a lokacin da kowa ke ƙyamata, ya mini gata a lokacinda masu gata ke gudun raɓata, ya tsaftace rayuwata a lokacin da datti mai ciwo ke lulluɓe da ita, shin baka ganin ya cancanci fiye da auren jininsa a gareni koda kuwa matarsa bata ƙaunata?”.
           Jawaad dake kallonta idanu jazur ya ɗauke kansa daga gareta a karo na farko, murya a dakushe yace, “Bazan musa miki cancantar Dad da abinda yafima haka daga garekiba, sai dai ni Jawaad Abdul-Aziz Yusif nace bai cancanci samun sadaukarwar komai daga gareki ba”.
        Sosai nai masifar waro idanu ina ture bargon da naketa faman rufe jikina dashi da, nama manta boss ne a gabana, dan haka cikin zafin rai nace, “Kai wanene da kake tunin Dad bai cancantaba? Yaushe ka sanni harda zaka iya aza mizanin cancantarsa da kalaman son sakamin shakku da baƙantasa a gareni, y.......”
         “Yah isheki!!”. Ya faɗa cikin daka tsawa yana ɗaga hannu tamkar zai makeni. Baya nai da sauri ina mai rumtse idanu dan nama sadaƙar mazgenu zaiyi.
      Jawaad ya rintse hannun da yakai zai maketa yana lumshe idanunsa tare da danne lip ɗinsa na ƙasa da haƙori tamkar zai hudashi, kusan sakan ashirin suna a haka kafin shi ya fara buɗe nasa idon da hannun yaja goran ruwa dake bed side drawer yasha, ahankali abinda ya tokare masa maƙoshi ya faɗa, ya maida jikinsa ya jingina da gadon yana ƙoƙarin dai-daita nutsuwarsa.
      Nima jin bai makeninba yasa na buɗe idanuna, karan farko a rayuwata da nakejin zafinsa, miyasa yakeson aibantamin Dad ɗina bayan shine yaymin gatan da har shiɗin ya shiga cikin jerin masu sanina....?
          Jay daya ji ƴar nutsuwa tazo masa ya sauke numfashi daɗan ƙarfi, batare da ya juyo ga bily ba yace, “Ina su Firdausi da iyayenta?”. Kamar bazan tanka masaba sai dai nace, “Tun randa na baro gidan bayan kwaɗama Jazuga abu ban sake waiwayarsa ba saboda inajin tsoro, Nima babban burina a yanzu sanin halin da suke ciki, musamman dana yawaita mafarkinsu a kwanakinan”. 
         “Miya hanaki waiwayarsu bayan lafawar abubuwa?”.
         Kallonsa nai da mamaki, nace, “Taya za'ai batun kisan kai ya iya lafawa? Kasheshifa nayi da wannan hanun nawa”. Nai maganar ina mai fashewa da kuka da nuna masa hanun nawa.
        Murmushi naga yayi, dukda dagani kasan na takaicine hakan bai hanani jin ciwoba. Ya juyo sosai yana kallon hannuna da nake nuna masa, sai kuma ya ɗauke kansa. “Wace anguwa su Uwargida suke?”.
      “Harna baro gidan bansan anguwarba nima”. Baice komaiba ya sauka daga gadon,
Chapter 73 · 0% Book details