← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 168

Sashe 80

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Ƙwai Cikin Ƙaya!!!
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
Page 36

.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi, matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta  daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai sa'a  itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani abu akan fuskata.
        A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina. Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar, babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
      Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har yanzun........
     Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
        Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta, “Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
         Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”.  Cikin sauke ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
          Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
             Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu kamar bansan sunaiba.

        A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai, munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema makwancinsa.
        Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo, dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake

zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin, “Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

★★★★★★★

          Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita tace a bani wayar.  Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji, kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”. Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya nai mata mukai sallama.

            Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda haka Ummu ta tsara.
          Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
       Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho, dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
          Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.

     Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah su barni anan, hakan kuma na
Chapter 80 · 0% Book details