← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 168

Sashe 108

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

              Su Abdul-raheem kuwa suna isa masarauta clinic aka wuce da Anuwar, likitan da yay aiki da rana ma har yana shirin tashine na dare kuma zaizo ƙarfe tara, dole ya dakata, taimakon gaggawa ya shiga bashi, cikin amincin ALLAH ba'a wani ɗauki lokaci ba numfashinsa ya dawo dai-dai. Hannun Abdur-raham dake kusa dashi ya riƙe yana hawaye, “Abdull  kamarmu ɗaya fa da shi, komaifa iri ɗayane, Wlhy ina cikin ruɗani Abdull, ko ku baƙwa irin wannan mugun kamar dasu Abdul-Raheem ai, inason ku maidani wajensa naji wanene shi? Idan kuma kun sani ku faɗamin Please, karkuce na rasa hankalina wlhy a rikice nake, jinake zuciyata na wani irin tsitstsinkewar da bantaɓa jin tayi ba.....”
     Abdur-raham bai samu damar bama Anuwar amsaba aka sanar da zuwan gimbiya. Kanta tsaye kan Anuwar tayi, tashi Abdur-raham yayi ya bata wajen zama, ta zauna tanama Anuwar sannu. Hawaye na shatata a kumatunsa yace, “Ummu yau naga mai kama dani kama mai ban al'ajabi da saka zukata ruɗani”. Murmushi Ummu tai masa cikin sigar lallashi tace, “Nasan da hakan Anuwar....” “Kin sani? Kenan kema kinsan shi? Kuma kinsan muna kama Ummu?”. Kanta ta jinjina masa tana sake faɗaɗa murmushinta, “Anuwar muma kamanninku ba ƙaramin sakamu a ruɗani sukai ba alokacin da muka gansa, hakanne ya saka muka tura Bilkisu wajenku, muka kuma ƙirƙiri hanyar da zakuzo ƙasarnan danmu sake tabbatarwa...”. “Ummu kin sake sakani a duhu wlhy”. “Zaka fita insha ALLAH Anuwar, amma lokacin hakan baiyi ba. abinda dai nakeso shine ka kwantarmin da hankalinka kaji, komai zai warware fiyema da abinda muke hasashe”. “To Ummu, amma inason na sake ganinsa dan ALLAH”. “Eh to banƙi ta takaban ba, amma ina ganin mubarshi basai ka koma ba, hakan zai saka ya sake zaƙuwa da ganinka kaima, dan inason ku wuce saudia goben idan ALLAH ya kaimu, lokacin da zai biyo sawunku nan ku kuma kun wuce, hakan zaisa yaso zuwa saudia ɗin, mukuma dama wannan damar muke buƙata ai”. Kansa kawai ya iya ɗaga mata danshi ta sake dulmiyasa a ruɗani, amma sai yay shiru bai sake tambayar komaiba. A take ma Doctor ya shigo ya bashi sallama suka tafi sashensu Abdul-Raheem.
           A wannan dare inhar Anuwar yayi barci to ragaggene, gashi Ummu ta gargaɗesa karya kira Umm-Anum balle sukai ga tunanin sanar mata wani abun, kuma koda komawa sukai karsu sanar mata komai har sai Jay yaje saudia da kansa.
       Washe gari jirgin safe suka bi shi da Anum cike da tsarabar biki daga Ummu, daka kallesu kasan basa son tafiyar dan ransu duk a cinkushe yake musamman ma Anuwar, har jiyake kamar ya zauna yayta kuka, sam bayason tafiya bai sake ganin Jawaad ba, baiji wani abu daga garesaba kuma.

_____________________________

                Ɓangaren Shahudah kam an sallamota itama sun dawo gida, taji sauƙi amma dukta rame ta ƙara wani irin haske maiban tsoro kamar wadda bata da jini a jiki, gashi yanzu ko yawan magana batayi sai dai ka ganta tayi zugum kamar wadda abin duniya ya dama. Koda yake ya dametan, dan Shahudah tanama Jay so mai tsananin gaske, sai dai tanaji a ranta bazata taɓa iya shearing ɗinsa da kowacce maceba ballema Bilkisu ƙasƙantacciya da tazo ƙarƙashin inuwarsu cin arziƙi. Har yanzu zatonsu na akan bilkisu asiri taima Jay ya aureta wai.
        Shi Dad harya bar ƙasar ma yau kwana biyu kenan, dan wani business ne na gaggawa yace ya taso masa, ko sallama saita waya yayma Momy ma, da yake ta rigada ta saba da irin wannan halin nasan sam sai bata damuba bakuma ta kawo komai a ranta ba.

_________________________

              Koda na kammala shirin barcina ban nema inda ya keba nai kwanciyata a ɗakina, har barci ya fara figata naji shigowarsa ɗakin, banko motsaba balle yay tunanin idanuna biyuma, gadon ya hawo yana faɗin “Wannan amaryar dai matsoraciya ce, nasan idanunki

biyu ai”. Guntun murmushi nayi kawai batare dana motsa ɗinba. Mannani da yay da jikinsa ya sakamu sauke ajiyar zuciya a tare, ya busomin numfashi a saman wuyana zuwa kunne yana sake ƙanƙameni. “Kin fasa jin labarin kenan?”. Da sauri na girgiza kai, “Naga kamar ka gaji ne shiyyasa nai shiru, amma cike dake da zaƙuwa wlhy”. Murmushi ya saki mai sanyi yana matsa yatsun hannuna daya riƙe, “To aike miskilancinki bai bari asan kinason abu”. Sosai maganarsa taso bani dariya, amma saina dake nai murmushi kawai, wai ni yake kira miskila, ai shinema ya dace da wannan sunan bawai niba. Yanzunma bance komaiba ina dai saurarensa, saida ya gama jan ajinsa da shan ƙamshi sannan ya juyo dani muna fuskantar juna, idanunsa a kaina yace, “Idan kuma na fara kikace zakimin barci saina ƙarya ƙasusuwanki”. A zuciyata nace, ‘Ai tun daren jiya ka kakkarya ƙasusuwan nawa da sauyamin kamanni Alhaji’. Dariyarsa da naji ciki-ciki ya sakani fahimtar maganar zuci ce ta fito fili. Baya nai zan juya yay saurin riƙoni ya maidoni, dole na haƙura tunda dai nariga nayi katoɓarar.
      Yaɗanja hancina kaɗan, “Wato tun daren jiya na sauya miki kamanni da karya ƙasusuwan ki? To a yafeni bazan sakeba Zinaraina”.
         Bance masa komaiba dan naji kunya. Ya fara shafa bayana a hakali da gyara kwanciya, “Jawaad Abdul-Azez Yuseef ɗane da ga. zuri'ar Alhaji Yuseef Tafida. Alhaji Yusif talaka ne mai rufin asirin ALLAH, domin kuwa manomine kuma makiyayi, duk dai a birni yake rayuwarsa da iyalansa to dukkan wani sabgoginsa na ƙauyensu, acan yake nomansa da kiwo, hakan yasa hankalinsa rabuwa biyu, harma zamansa a ƙauyensu ya so ya rinjayi zaman birnin. Matan Alhaji Yusif uku ne cif, kuma kowacce a cikinsu ALLAH ya azurtata da haihuwa, matarsa ta farko hajiya Atika yaranta shida huɗu duk maza biyu mata, sai ta biyu badiyya yaranta huɗu itama, mata uku namiji ɗaya, sai amarya Rahina ke da uku maza biyu mace ɗaya...............

           Tunda ya fara nake hawaye, sanda ya dire ƙarshe tuni kuka yaci ƙarfina har ina shashasha, ya jani jikinsa ya rungume yana lallashi, “To kuka ya isa haka mana uhmyim, haka rayuwa take, ganin wani a cikin ni'imar rayuwa bashine yake nufi ya samu komai ba, kowacce irin rayuwa zaki samu akwai rauni da jarawa a cikinta, da yawan dariyar da mutane keyi idanda zaki zauna dasu kiji suwayesu zaki fahimci iyakarta haƙori ne kawai, Haƙuri rahamane, duk wanda yay haƙuri baya yin asara, idan kayi haƙuri kaga babu riba a cikinsa to ɗan kaɗan kayi, sannan ka binciki kanka maybe kana zaluntar waninka ne, dan bakowacce jarabawa bace ga ɗan adam take zama daga ƙaddararsa, wasu mutanen sune da kansu suke shuka sharri sai kiga suna ta naɗar sakamakonsa da sharrika suma. Duk sanda na samu wani bakin zare na binciken mahaifiyata koxan dace da samunta sai kaina ya kulle Miemaa, kiga hankalina ma da tunanina sun gushe daga wajen, bansan miyasa hakanba?”.
           “Al'amarinta kamar akwai sihiri a ciki boss”.
     Saurin ɗagoni yay daga jikinsa, yace, “Miyasa kikace haka?”. Hawayena na share ina ɗan jan hanci kaɗan, “Duk musulmin ƙwarai ya yarda akwai ƙaddarar mutuwa, kuma wajibice ga kowa babu fashi, a ganina rasuwar Abba bazata gusarma Mamah hankali ba, koda zata shiga ruɗani bazai yuwu ace na gushewar hankaliba har akai gayin haukan da za'a bar gida ma gaba ɗaya. Matar dana zauna da ita a saudia bansan asalin sunanta ba, amma haka kawai tun ganina da ita na farko naji ƙaunarta mai tsanani ta shigeni har nakanyi mamaki, itace mahaifiyar Anum da Anuwar, aɗan zamana da ita na fahimci abubuwa da yawa daga gareta waɗanda suka sakani a ruɗani,  bazan yanke hukunci akan gaibu ba, dan ALLAH shi kaɗaine masanin gaibu, saidai ga shawara”.
        “Wace irin shawara?”. “Mizai hana muje Saudia a zuwan kamar na kai mata kai ku gaisa, dan dama ta roƙeni akan wataran na kai mata kai, haka kawai a ranta takejin son ganin mij.......”
         “Ƙarasa mana to”.
Fuskata na ɓoye cikin ƙirjinsa ina murmushi. Murmushin shima na jiyo yanayi, ya tura hannunsa cikin sumata yana yamutsawa kamar maimin susu. Tsawon lokaci muka ɗauka a haka babu wanda ya sake magana, daɗin yan

da yakemin a cikin kai ya sakani fara lumshe idanun barci, cikin mintuna ƙalilan kuwa barcin yay gaba dani.

               Tunda Bilkisu tai barci sai idanun Jawaad suka sake bushewa, kalamanta kawai yakema fashin baƙi dalla-dalla, daga ƙarshema zameta yay daga jikinsa a hankali ya kwantar, bayi ya shiga ya ɗauro alwala yazo yayta nafilfili, ya jima yana miƙama ALLAH kukansa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa, harda hawayensa shaɓe-shaɓe, fatansa ALLAH ya buɗa masa haske akan al'amarin nan ya fahimci sirrin dake ɓoye, duhun dake lulluɓe da shi da matarsa ALLAH ya yaye musu shi ya zama haske. Bai kwantaba sai kusan ƙarfe uku. Yana kwanciya barcin yay gaba dashi dan idanunsa dama har zafi suke saboda barcin.

          Kiran sallar asuba da aka ƙwalane ya sakashi farkawa a ɗan firgice hannunsa dafe da kansa, sai da ya jero addu'ar tashi barci kafin ya iya furta Aunty Mah-mah, yau kam ya sake mafarkinsa daya saba na ƙaddarar jini a cikin jini, sai dai yau ya farka bai manta fuskar matar dake masa kalaminba, Gwaggonsa ce Rahma wadda suke kira da Aunty Mah-mah. Juyawa yay ya kalli Bilkisu data cure waje guda cikin bargo ta rufe har rabin fuskarta. Yaɗan lumshe idanu ya buɗe yana sauke ajiyar zuciya, tsahon lokaci yana kallon Bilkisun da nazarin abubuwa masu yawa har aka fara kiraye-kirayen sallar shiga masallaci. Nannauyan numfashi ya sauke sannan ya sauka a kan gadon da ƙyar dan jikinsa ko ina ciwo yake masa alamar barcin bai ishasa ba.
      Alwala yayo, ya fito a gaggauce ya tada Bilkisu sannan ya fice masallaci.
Chapter 108 · 0% Book details