← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 168

Sashe 81

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi, dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
     Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
     Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss, murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa tsakanin...........
          Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da ɗakuna biyu a ciki.
      Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake kasheni taketa sakarmin.
           Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita. Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana, sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama, murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango kaina da ita kanta.

        Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace, ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata, zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku zama huɗu bayan ke”.
         Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.

            Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi, aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana koyamin

girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
     Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
        Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara hankalina gareta baki ɗaya.

____________________________
Chapter 81 · 0% Book details