← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 168

Sashe 4

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

2
..............Koda na fito daga ɗakin saida na huta a falon saboda yanda zuciyata ke mutsu-mutsu a cikin ƙirjina, ina matuƙar mamakin wannan al'amari dake yawan faruwa tsakanina da mutumin nan, na kuma rasa wazan tunkara da maganar halin da nake tsintar kaina akansa kozan samu fashin baƙin saɓanin wanda zuciyata ke kissima min, nidai nasan ba tsoronsa nakeba, to minene dalili? Wannan amsar nake neman mai bani.
Gwiwa a sage naja ƙafafuna na fice daga sashen zuwa harabar gidan. Yanzunma dai ban sami ko ɗaya daga cikin su aunty Aamilah ba, gashi banida Number kowa a cikinsu. Dole na sake nemar guri na zauna inda babu yawan hayaniyar mutane, sai jefi-jefi nakan ɗanga sun gittani.
★★★★★
Yanda Jawaad ya nuna halin ko in kula da ganin na Bilkisu bazaka taɓa tunanin yama santaba, sai dai harta fice daga ɗakin yana kallontane ta wutsiyar ido, acan ƙasan zuciyarsa na raya masa “Ita kuma miya kawota nan?” sai dai a fili bazaka taɓa fahimtar komaiba.
Zama yay a saman ƴar dirowar dake farkon shigowa ɗakin, cikin girmamawa ya gaisa da iyayensa, sukai masa gaisuwar ta'aziyyah tare da jero addu'ar neman gafara ga mamacin, har suka cigaba da ɗan tattaunawa akan rasuwar wadda ta jasu tunowa da rasuwar mahaifin Jawaad ɗin shima da ɓatan mahaifiyarsa.
Haɗiyar zuciya kawai Jawaad yake famanyi, amma bakinsa ya kasa furta komai, daga ƙarshema saiya miƙe yana faɗa musu zaije ya ɗan kwanta, gimba zai kawo musu abincin da zasu ci.
Basu hanashi tafiyaba, dan yanayinsa ya nuna yana buƙatar hutun sosai.
★..::..★
Sai kusan ƙarfe biyar na hangi Mom suna gaisawa da wasu gungun baƙi da sukazo musu gaisuwa, da sauri na miƙe na nufeta karta sake ɓacemin, dan matuƙar gajiya na gaji da zaman ni kaɗai, danma naɗanyi cheating dasu Rebecca ne a group ɗin da muka buɗe iya mu biyar kawai na rage kaɗaici. Daga gefe na tsaya harta gama gaisuwa da mutanen suka tafi kafin na ƙaraso gareta, gaidata na farayi a ɗarare, tunda nasan bani da wata fawa a gareta, amma a mamakina sai naji ta amsa harda tambayata ina na shiga tun ɗazun bata ganniba? wani sanyi ya ratsa zuciyata, kasancewata marainiya ina matuƙar buƙatar kulawar mahaifiya koda kaɗanne, rashin samu kuma na sakani a ƙunci sosai, sai dai ina ƙoƙarin shanyewa ba kowa ke fahimtar hakanba. Cikin girmamawa na bata amsar tambayarta, saita bani umarni akan muje ciki naci abinci.
Ban sake sakashi a idonaba har zuwa dare bayan sallar isha'i da muka fito domin tafiya gida, ƙiri da muzu Aamilah da aunty Shahudah suketa ƙoƙarin zamewa haɗa tafiya dani, duk da basu fito fili sun faɗaba na fahimci haka da kaina, dan kafin nagama kimtsawa harsun fice daga sashen na Mama Atika, sai tare muka fito da Mom, sai muka iske harsun tafi wai tare da Yah Salman.
Banji haushiba, saima murmushi da nayi kawai, driver ne zai tafi da Mom, dan haka nima su zanbi dole. Mom ta tsaya gaisuwa da wasu mata da suma zasu tafi, ƴan gayune sosai da kallo ɗaya zakai musu ka fahimci naira ta zauna musu, nidai bayan na gaishesu jikin mota na koma na jingina kawai ina kallonsu da mamakin yanda naga Mom ta sake dasu sosai, yanda na santa da wulaƙanci, koda yake masu iya magana kance wata gaban tafi gaban raini ai.
Zuciyata ta motsa da ƙarfi a cikin ƙirjina, hakan ya saka tsoro ziyartar raina, koban faɗaba nasan hakan na nufin Dodona ya kusanto wajen koma yana wajen, zuwa yanzu nafara sabawa da wannan SABON AL'AMARIN namu.
Ilai kuwa ina ɗago idanu akansa na sauke, tsaye yake ɗan nesa damu kaɗan, hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ɗayan kuma ya riƙe waya dake kunnensa, wadda ke nuna alamar yana magana da wanine, ɗan taku yake ɗaya biyu cike da nutsuwa da cikar haiba, ba kayan ɗazun bane a jikinsa, daga wando har rigar jikinsa na yanzu duk fararene tas, gefe wando na duka ƙafar biyu akwai ratsin dogon zare jaa daga sama har ƙasa, sai agaban rigar shima anyi rubutu da ja, hasken dake ƙwanyar a tsakar gidanne ya sani ganin abinda aka rubuta, sai silifas fari shima, sosai kayan sukai masa ƙyau, har na iya kasa janye idona a kansa dukda wutsilniyar da zuciyata keyi kuwa.

Haka kawai Jawaad dake waya da Jabeer yaji a jikinsa kallonsa akeyi, kallon kuma irinna wanda keda kaifin gani da baiwar ƙarfin kwarjinin idanu, duk yanda yaso basarwa tamkar yanda ya saba hakan sai ya gagara, dole ya fara wulƙita nasa fararen idanun kozai samu nasarar cafko wannan mayen idon dake neman saukar masa da gajiya. Karaf kuwa idanunsa suka sauka akanta, shima ƙirjinsa ya motsa alamar harbawar zuciyarsa. Tabbas yaji a ransa itace ke kallonsa, amma a mamakinsa sam idanunta da hankalinta basa kansa, karon farko da miskilancin yarinyarnan ya motsa zuciyarsa, tun ganinsa da ita na farko a airport ya fahimci miskilace ta bugawa a jarida, kasancewar ALLAH ya azurtashi da ilimin karantar hallayyar ɗan adam cikin lokaci ƙanƙani, zuwa yanzu mamakin ganinta yabar ransa, dan ya kula akwai alaƙa tsakaninta da Qaseem.......
“Hello...hello...” Da Jabeer keta ambatane ya sakashi dawowa hayyacinsa, dan tuni ya saki wayar da suke ya kama sabgar bilkisu, abinda bayayi sam a rayuwarsa (wato shiga abinda bai shafesa ba), yaja siririn tsaki yana murza goshinsa da hannunsa daya ciro daga cikin aljihu.
Dai-dai lokacin da Bilkisu ta buɗe gaban mota ta shiga ta zauna, dan Mom harta shige baya itama.
Wani irin harɗaɗɗen numfashi ya sauke har Jabeer na tambayarsa “ko lafiya?”.
Gutun tsaki yaja yana yanke wayar batare daya bashi amsaba, yakuma jan wani tsakin har sau biyu yana takaicin kansa da shiga hurumin da ba nasaba.
_______________________________
Washe gari ban biyosuba, dan inama barci suka fice, babu wanda yace a tasoni, nima koda na tashi kuku ke sanarmin sun tafi banji komaiba a raina saima daɗi, tunda nasan zuwana bazai ƙara komaiba koya hana, hasalima banason gamuwa da Dodona.
Bayan na karya ɗaki na koma nai wanka, nai shiri cikin doguwar riga ta atanfa data samu zaunannen ɗinki, bawata kwalliya naiba, nasaka turare sama-sama na fito bayan na yafa ƙarmin gyale.
Kai tsaye gate na nufa wajen baba maigadi dake zaune shida mai bayin filawar gidan suna hira, suna ganina suka shiga gaisheni cikin girmamawa, sam banason hakan da sukemin, dan kuwa niba kowa bace a gidan face maicin alfarma, sannan duk sun girmeni, baba maigadi ma a haife ya haifeni, shima mai bayin fulawar kobai haifi kamata ba nasan yanada manyan ƴaƴa.....
“Hajiya fita zakiyine?”.
Baba mai gadi ya katsemin tunanina, kaina na girgiza masa ina murmushi. “A'a baba ba fita zanyiba, hasalima wajenka nazo muyi magana idan ban takura makaba dan ALLAH”.
Da sauri yace, “Haba wace takura kuma” yay maganar yana miƙewa da sauri, babu jimawa sai gashi da farar kujera, ajiyemin yay gefensu alamar na zauna, mai bayin fulawa kuwa yay mana sallama akan zaije gida yakai cefane.
Sake gaisawa mukai da baba maigadi, yay min ta'aziyyar rasuwar da akayi, nako amsa masa tare da tambayar lafiyar iyalansa, bayan amsamin da yay muka ɗanyi shiru, tunani nake ta ina zan fara abinda ya kawoni garesa?. Zuwa wasu ƴan mintuna sai dabara ta faɗomin, nai murmushi ina sake maida hankalina gareshi da kunna voice recorder dan na samu damar kwashe dukkan abinda zamu tattauna nayi nazari a tsanake a kansu.
“Uhm... Baba dan ALLAH niko wata tambayace dani?”.
Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “ALLAH Yasa na sani hajiya”.
Murmushi naɗan masa, nace, “Insha ALLAHU inada tabbacin kama sani ɗin”.
Baice komaiba sai hankalinsa daya maido kaina baki ɗaya, nima sai na sake nutsuwa sosai.
“Baba dan ALLAH ko zaka iya tuna ranar da abinnan ya faru da Amina a gidannan da wanda ba'asan ko waneneba?”.
A bazata maganar tazo masa, dan haka kawai saiya hau tari babu shiri. A rikice na shiga masa sannu, na jawo ruwan dana fito dashi daga ciki na miƙa masa da sauri bayan na ɓalle murfin, amsa yay har hannunsa na rawa ya kafa goran a baki ya ɓaɓɓaka, saida yasha kusan rabi kafin ya sauke, idanunsa harsun kaɗa sunyi jajur, sai naji tausayinsa ya kamani, koda ya dawo dai-dai shiru nai ban sake masa tambayarba har tsawon wasu mintuna.
Na sake jeho masa tambayar a karo na biyu, yanzunkam a mamakinawa shiru yay bai tanka minba, sai dai yanata ƴan kalle-kalle tamkar mai tsoron a ganmu ko wani ya jimu. Jin bashi da niyyar bani amsa ya sakani kallonsa, a karo na uku na sake maimaita masa tambayar da sigar kwantar da kai.........
“Ɗi!! Ɗi!!! Ɗi!!...” mukaji horn ɗin mota daga waje, hakanne ya sakashi tashi da sauri ya nufi gate ɗin, na tabbatar dama hanyar da zai gudu yake nema, sai kawai na samu kaina da ƙura masa idanu ganin yanda har yanzu jikinsa ke mazarin rawa.
Hancin motar Dad ne ya danno kai cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya ina miƙewa tsaye, saboda tsayawar da driver yayi a saitin da nake zaune, shi kuma Dad ya sauke glass ɗin ɓangarensa yana mani murmushi.
Nima murmushin nake masa ina miƙewa na nufesa, da hannu yaymin nuni nazo, dole nabi motar da direba yaja zuwa ciki inda zaiyi fakin.
Chapter 4 · 0% Book details