← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 168

Sashe 129

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a wani kalar tausayi ya amshi wayar, cike da ladabi yay sallama. Cikin Kakkausar murya Jay yace, “Idan ka gadama kaci amanarmu, idan ka gadama kayi aikin da zaka ceci ranka, wannan bomb ɗin da kake gani a tashi ɗaya zai tarwatsa naman jikinka ko kalar ƙashinka baza'a gani ba ma balle kaiɗin”. “Oga dan ALLAH kaimin rai, komai kake buƙata zanyishi”. “Ya rage naka”. Jawaad ya faɗa yana yanke kiran.
         Computer ɗin da ya haɗa a saman centre table tun ɗazun ya kunna, ya koma saman kujera ya zauna, ya jona wayarsa jikin USB sannan ya daidaita muryar Alhaji kokino da maigadin gidansa yay mana recording. cikin wayoyin da yazo da su ya ɗauki ɗaya, itama ya haɗata da Computer ɗin sannan yay kira. Nidai inata aikina ina kuma kallonsa lokaci-lokaci, da hannu yaymin nuni dana zo, matsowa nai garesa, ya miƙamin mouse ɗin Computer da faɗamin yanda zanyi da zaran an ɗaga wayar, saboda muryar Alhaji kokino yazam ita suke ji. Kaina na jinjina masa, ya saka abu a kunne sannan yay kiran wayar. Bugu biyu aka ɗaga, cikin wata buɗaɗɗiyar murya aka fara gaisuwa da tsantsar ladabi. Amsawa naji yanayi da salon da ba nasa ba, kafin ya fara magana cike da tsumewa, “Yaron da ya kawo matar nan gashi nan na turosa shi da wasu yara su uku zasu ɗauketa”. “To amma oga ya kuma zaka canja shawara? Ɗazunfa ba haka mukai da kai ba, wai miyasa kuketa canja mana aiki bakamar yanda yake a baya ba?. Kawai saboda sakacin mutum ɗaya, gaba ɗaya gazawarsa tasa komai sai rushe mana yake nemanyi a ƙungiya, a kaudashi mana”. Kallon juna mukai ni da boss, ya ƙara tsaurara muryarsa da gyara zaman abinda ya ɗaure wuya dashi, “Sabon yanka kaima kasan muhimmancinsa ai a garemu, amma ka ajiye wannan maganar zamuyita wajen taron ƙungiya na ranar bauta, a basu matar dai dan akwai matsalane zasu canja mata wajen zamane”. “To babu damuwa oga, saisun ƙaraso”. Ya yanke wayar da sauri yana kunce ƙyallen wuyansa da sauke nannauyan numfashi, saurin miƙa masa ruwa nai, ya amsa yasha yana lumshe ido da murza wuyansa. sai kuma ya ɗauka wayarsa ya turama su Munkaila saƙo akan suje komai yayi.
          Daga ni har shi kowa juya zancen ƙungiyarnan da sabon yanka ya faɗa mukeyi a ranmu, ya kalleni yana miƙewa “Mikika fahimta a zancensa Miemaa?”. “Sunada wata ƙungiya, da gaji kuma bata alkairi bane, to amma wanene ya ɓata musu aikin?”. “Nima wannan shine tambayata, maganar gayen nan ta sake ɗarsamin abubuwa a cikin raina da yawan gaske, kuma insha ALLAHU saimun bincikosu. Inada tabbacin duk wani wanda muke buƙatar samu a dalilin bibiyar numbers ɗin dake cikin wayarnan zamu samesa, tsabar munafurci babu wadda akai saving nata da sunan mai ita, yanzu dai mu jira dawowarsu da maman yara, insha ALLAHU daga nan zuwa asuba nasan zasu shigo”. Kaina na ɗaga masa jikina duk a sanyaye.
    Dawowa yay ya zauna muka ƙarisa aikin, kusan sha ɗaya muka kammala, muna cikin tattare komai Munkaila ya kira ya sanar masa yanzu haka sun ɗakko hanyar dawowa, amma gaskiya maman yara na cikin mawuyacin hali sosai, dan a yanayin da take ciki su da farko ma sun zata bata numfashi, sai daga baya suka fahimci tsabar wahala ce da azabar da ake gana mata.
         Hankalinsa tashe ya basu Umarni akan su gaggauta tahowa kawai, su kuma ringa mata addu'a suna tofa mata.

            Mun kwanta ne kawai badan muna tare da nutsuwa ba, duk bayan wasu mintuna sai ya kirasu yaji suna a ina ne? Barci gaba ɗaya ya ƙauracema idanunmu. Bamu sami ƴar nutsuwa ba sai da suka iso kusan ƙarfe uku na dare. Likitan da zai dubata isowarsu kawai yake jira, dan haka suna isowa ya duƙufa kanta kamar yanda suka kirasa video call mukaga komai.
       Mawuyacin da take ciki saida nai kuka dan tausayi duk da a yaune na fara ganinta, shi kansa ajiyar zuciya kawai yake saukewa a jajjere. Barci ya sacemune kawai kasancewarsa gwanin iya sata, amma badan mun shirya kwanciyarba.

              ★★★★

    Da asuba kiran sallar farko yay alwala ya fice gidan, na zata massallaci ya nufa, sai da najiyo ƙarar tada mota da buɗe gate na fahimci fita yay. Addu'a na bisa da ita na tashi nai alwala nazo nai zaman yin nafilfili nima har aka kira sallar sh

iga.

         Koda Jawaad ya fito kansa tsaye gidan Alhaji kokino ya fara isa, ya bama baba maigadi wayoyin sannan ya wuce inda aka ajiye maman yara. Ba ƙaramin tashi hankalinsa yayi ba ganin mawuyacin halin da baiwar ALLAHr nan ke a ciki, a hakama Munkaila ya tabbatar masa tayi fasali fiye da yanda suka ɗakkota, Jawaad ji yay kamar yayta dukan ɓaleru har sai ya daina numfashi, amma ya danne ransa suka fita salla. Bayan an idar baro gidan yayi akan zai dawo zuwa anjima tare da wadda zata kula da ita.
      Ina kitchen ya shigo gidan, na leƙo nai masa sannu tare da gaisheshi, a yanda ya amsa min kawai nasan zuciyar ƴan mazan a kusa take, ɗakinsa ya wuce, nikuma na cigaba da aikina dan na samu na kammala da wuri ba sai na makarar damu kamar jiya ba.
       Bayan na kammala sai da na fara leƙe ɗakinsa, wanka yake, dan haka nima na fito zuwa nawa ɗakin na shiga wankan. Harna fito nai shiri bai shigoba yau, ban damuba na kammala abinda zanyi sannan na fito gaba ɗaya, ɗaura bag ɗina nayi a dani na kuma nufar ɗakinsa inajin duk babu daɗi, shi indai yanada damuwa to shikenan sai kiga duk ya ƙuntata, duk wani walwalarsa gushewa take ya koma miskilin gaske, nikam a ɗan zamana da shi ɗin nan na fahimci ga iyalinsa shi mai sauƙine, miskilancin sa sai a waje yake zubashi kamar ba shiba. A shirye na iskesa, rigar saman suit ɗinsace kawai bai sakaba sai tie...,  zaune yake a bakin gado da waya a kunne alamar waya ya keyi. Ƙarasowa nai na gyara saman mirror ɗin da ya gama hargitsawa, ya riƙo hannuna ya ɗaurani bisa cinyarsa yana faɗin “Gata Ummuna, amma ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, muna nan munata shirin dawowar ai”. Sai yanzu na fahimci da ƴan saudia yake wayar, kafin nace wani abu ya ɗauran wayar a kunnena. Cikin girmamawa da ɗoki nai sallama, daga can Umm-Anum ta amsa min cike da kulawa, sai dai yanda naji muryarta na sake fahimtar tana tare da damuwa. Bayan mun gaisa tace, “Ɗiyata wai da gaske yake kuna shirin dawowa?”. Murmushi nayi ina kallon fuskarsa, ya wani narkemin idanu da fuska, na sake murmusawa sannan nace, “Eh Ummu da gaske ya keyi”. Wata sassanyar ajiyar zuciya naji ta sauke, sai tausayinta ya kamani har ƙwalla suka cikamin ido, munyi ƴar hira kaɗan ta bama Anuwar wayan shima muka gaisa, sannan Anum ta amsa itama, ganin mun fara nisa a fira dan Anum ma dai babu laifi akwai magana tamkar Nabeelah, ƙwace wayar yay, “K sai anjima aiki zamu fita”. Ina jiyota tana kukan shagwaɓa ya kashe wayarsa bai saurareta ba. Kai ya dunguremin, “Idan kina biyema Nabeelah da Anum sai kin zama parrot irinsu, nidai nafison matata haka mara son hayaniya”. Murmushi nayi tare da miƙewa daga cinyar tasa batare da nace komaiba. Shima bai sake cewa komaiba ya miƙomin tie.. Ɗinsa, “Nifa ban iya sakawa ba”. “Sai ki fara koya daga yau” ya faɗa yana miƙewa. Ya fini tsawo, dan haka na ɗauki filon dake saman sofa na ajiye ƙasa na taka, duk da hakan ma dai ban kaiba, amma nafi ɗazun, shine ya rinƙa nunamin yanda zanyi har muka kammala, yace, “Woow kinyi ƙoƙari”. Daɗi naji sosai, nace, “Da gaske?”. “Ehum” ya faɗa da ɗan lumshe ido. “Thanks” na faɗa nima ina murmushi.
          Tare muka fito daga ɗakin, ya ɗauka abincin maigadi da Sadiq tunda yana nan da safe ya kai musu, nikuma na zuba mana namu a plate ɗaya, sai tea dana haɗama kowa dan nasan shikam in bai sha tea ba akwai damuwa, ina mamakin yanda yakema tea so na masifa haka. Koda ya dawo muka zauna cin abincin sai naga bayaci sosai, ya raba hankalinsa biyu, ɗaya a aiki a tab... ɗaya ga abincin, cire nauyinsa da nakeji nayi na amsa cokalin na fara bashi da kaina, baice dani komaiba ya fara amsa, da yake hankalinsa nakan wayar sai yaci abincin sosai batare da ya fargaba. “Miemaa Please barni haka karnaje office na kasa aiki, ashe wayo kikemin kinata nausamin abinci a ciki”. Ƴar dariya nai kawai na tattare kayan zuwa kitchen, sauri-sauri na ɗaurayesu na fito, tsaye na iskesa riƙe da bags ɗinmu alamar ni yake jira. “Anya kuwa bazaki ajiye wannan aikinba ki zama matar gida kawai?”. Gabana ne yay masifar faɗuwa da jin wannan furuci nashi, dama kullum cikin addu'a nake kar wannan tunanin yazo masa a
Chapter 129 · 0% Book details