← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 168

Sashe 131

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

................Kanmu duk muka ɗaga mata, da amsawa da “Insha ALLAHU mama zamuyi ƙoƙari, a cigaba da tayamu dai”.  rakkiya tai mana har soro. Ganin ya nufi mota na dubesa cikin rawar murya nace, “Yayanmu gidan Dad ɗin fa?”. Bai tankaminba yaja hannuna ya turani mota shima ya shiga, Sadiq ya tayar muka bar anguwar.
         Kallonsa nake idanuna cike da ƙwalla, ya juyo shima ya kalleni fuska a cinkushe. “Kinsan idan kika bari hawayen nan suka zubo sai ranki yay matuƙar ɓaci wlhy!”. Ƙasa na maida kaina ina ƙoƙarin haɗiye kukan dake neman ƙwace mani, bai sake kulaniba har mukaje gida, kowa ɗakinsa ya nufa zukatanmu duk babu daɗi, sai da na rufe ƙofar sannan na saki kukan da ya hanani yi amota irin mai cin rai ɗin nan kuwa. Harnai wanka na fito hawaye basu daina min gudu a kumatuba, a haka na saka wando da riga marasa nauyi nai sallar magriba, ina idarwa na fita kitchen, banji motsinsa ba harna kammala girka abinda zamuci, na ɗauki na maigadi zan fita na kai masa mukaci karo a ƙofa zai shigo. Uffan baice mani ba ya miƙamin hannu alamar na bashi. Bashi nayi na juya ciki shi kuma ya tafi kai masa. Ɗakina na nufa dan banyi sallar isha'i ba, ina farawa ya shigo. Ganin ina salla sai ya juya yana faɗin, “Idan kin idan ki sameni falon baƙi”.
              Koda na idar ban cire hijjabin ba na fita, ruwa na ɗauka sannan na nufi falon baƙin, nai sallama suka amsamin da bani izinin shiga. Dattijon tsohon nanne da muka haɗu da shi ranar akan zancen maman yara, na ajiye ruwa na zuba musu sannan na zauna muka gaisa. Miƙewa na sakeyi dan na kawo masa abinci, ban jimaba na koma da abincin, sakamin albarka baba yay tayi, shi kansa boss na fahimci yaji daɗin hakan da nayi. Abincin ya faraci, boss kuma yana cigaba da latsa wayarsa ta fama, tashi nai zan barsu yace, “Dawo ki zauna, magana zamuyi da shi yanason komawa da wuri”. Na amsa masa da “to” na koma na zauna. Cikin ƴan mintuna Baba ya kammala cin abincinsa yana sake sanya mana albaka, sai da ya sha ruwa sannan ya maida hankalinsa ga boss. “Yauwa ɗana ina saurarenka”. Ajiye wayar boss yay yana furzar da huci. “Baba kamar yanda na fara maka bayani shine ta wace hanya kake gani zan iya shiga gidan domin ɗakko abinda tace? Matsalar shine a ɗakinsa tace abin yake, ɗakinma a tsakkiyar ƙarƙashin gado”. Baba ya jinjina kansa yana gyara zama, “Wato ɗana, ba wai ɗaukar ko shigar bace matsala ma, dole al'amarin sai da lura, su shaiɗanun mutane irin waɗan nan al'amarinsu baya buƙatar fuska da fuska, kamar yanda suke ƴan yaƙin sunƙuru haka masu cinsu da yaƙi ya kamata su kasance suma”. “Hakane baba”. “Yauwa to kagani ni a nawama tunanin wannan aikin kam da mace yafi dacewa ta wani ɓangaren, wani ɓangaren kuma namijinne, ɗakinsa dai bazai shigu gareka matsayin namijiba cikin sauƙi”.
      “Baba to mizai hana ni kawai naje”. Na faɗa kaina tsaye babu ko ɗar a raina. Shiru duk sukai suka zubamin ido. Cikin jinjina kai baba yace, “Shawararki kam abar dubawace, sai dai kuma ai bazai yuwu kije kai tsaye ba, sai dai mu duba wasu ƴan dabaru haka?”.
       Kafin nayi magana boss yace, “Baba bazai yuwu taje ba, mudai sake wata shawarar”. Murmushi naga baba yayi kawai, cikin rawar murya nace, “Miyasa to? Yanzu idan bajeba wa zamuce zamu saka wannan aiki? Ni a ganina baba zai iya ya kaini gidan matsayin jikarsa, insha ALLAHU ni kuma zan ƙarasa sauran aikin inhar na shiga gidan dai da matsayin da zan iya shiga wasu ɓangarori shikenan”.
       Shiru yay bai tankaba, baba yace, “ƴata idan mijinki baya so karki matsa, dan gaskiya wannan aikine mai haɗarin gaske, inaga zanje na ƙara tunanin wata hanyar, kuma sai ku sakeyi, yazam dai kafin safiya idan ALLAH ya kaimu ya muna da abinda muka riƙe, dan na tabbata nan da kwana biyu zai dawo daga tafiyar da yayi yau da safe. zan koma dan banason a farga da bani bane a gate ɗin”. Godiya mukai masa ya tashi yay masa rakkiya, ni kuma na koma ciki ina ƙunƙuni, dan insha ALLAH zanta lallaɓasa nikam harya amince naje nai wannan aikin da kaina. Ganin halin da maman yara take ba ƙaramin zaburar da zuciyata yayiba, na fahimci al'ummata na buƙatar jajurtattun mata irin su ma

man yara, wayasan shekarun data ɓata domin bibiyar wannan tukunyar? Amma gashi har tana a cikin magagin wahalar da aka bata bataji ta gajiyaba da son cimma ƙyaƙyƙyawar manufarta ba.
      Jin an taɓani na sauke sassanyar ajiyar zuciya, kujera yaja ya zauna idonsa a kaina har lokacin. Kallonsa nai cikin ido ko gezau babu a karo farko na tarihin rayuwata, dukda bugun ɗari-ɗari da zuciyata keyi haka na daure na dake ban cire idanuna ba, “Kar kace a'a, dan ALLAH, mune ya dace muyi aikin nan basai mun saka kowa a ciki ba, sannan bamu da isashen lokacin zaman yin tunni ko binciken wanda zaiyi mana ma.  ɗiyarsa ta ɗakko mana wayoyi ba shine ke nufin zata ɗakko mana wannan ba kuma”.
           Gani kawai nai idanunsa na ƙyalli tamkar hawaye sun taru a ciki, ya girgizamin kai a hankali yana kauda kansa, hannunsa nai saurin kamowa cikin nawa, ya sake juyowa ya kalleni, nawa hawayen ne suka silalo a hankali saman kumatu, “Please yayanmu karkace a'a, nima ka barni nai hidima ga Umm-Anum kamar yanda tayi a gareni tun batasan wacece ni a gareta ba, har raina jin ahalinka nake a zuciyata da ɓargo, idan ka hanani yin wannan aikin zanji matuƙar zafi a raina bakuma zan daina jiba har na koma ga ALLAH, dan zanke ganin kamar ni ɗin dan ba ahalink.....”
      Jawoni kawai yayi jikinsa ya rungumeni batare da ya barni na ƙarasa faɗa ba, da sauri-sauri zuciyarsa ke harbawa a ƙirjinsa, kamar yanda nima tawa keyi, cikin kuka na sake cewa, “Please Yah Jayyyy”.
       Jawaad ya lumshe idanunsa a hankali yana wani cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi, “Jay” sunane da mafi yawan mutane ke kiransa da shi, bai taɓajin ambatar sunan da wani banbanci na daban ba ga mai faɗarsa sai yau a bakinta, musamman ma data ja “y” ɗin ƙarshe sai yaji gaba ɗaya tsigar jikinsa ta tashi.
      Ɗagoni yay a hankali na sake zama sosai a kujerar dining ɗin, ya riƙe fuskata a cikin tafukan hannunsa yana sharemin hawayen da babban yatsansa, muryarsa a shaƙe yace, “Miyasa kema kin iya rigima ne Miemaa?, aini Kin riga kin gamai min komai a rayuwa tunda kika zama sanadin haɗuwata da mahaifiyata”. Sake ɓata fuska nai alamar tahowar wani kukan, nace, “To dan ALLAH ka barni na cika ladana”. Murmushi ya ɗanyi mai ciwo yana sake turani cikin jikinsa, “Shike nan bar kukan haka, zanyi tunani daga nan zuwa safiyar da yace insha ALLAHU, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. “Amin” na faɗa ina murmushi.
          Yau shine ya bani abincin da kansa, bayan mun kammala ya taimaka min muka tattare kwanikan zuwa kicin, ina wankewa yana ɗaurayewa har muka kammala sannan muka fito bayan na kammala tanadar abinda zan haɗa mana breakfast insha ALLAHU da safe. Yau kam bamuyi zaman wani aiki ba, brush kurum mukai da yin shirin barci muka kwanta. Babu jimawa barci yay awon gaba damu kuwa. Kusan ƙarfe uku na dare ya tadani, alwala mukai muka shiga yin nafilfili domin miƙa buƙatarmu wajen mahaliccin kowa da komai, mai rahama da ƙari ga bayinsa. Bamu sake kwanciya ba sai da mukai sallar asubahi, da yake a gida yayi shima muna idarwa ya jani muka haye gado, zanyi magana yasa tafin hannunsa ya rufemin baki ruf. Dole na haƙura muka kwanta, barci kuwa yay cak damu zuwa duniyarsa.

       Bamu farkaba sai 8:11am, nice ma na fara farkawar, na waro idanu a waje dan ganin makarar da nake gudu dai ta tabbata, jawoni yay zai maida ya sake kwantarwa nace, “takwas fa ta wuce boss”. Buɗe idanunsa yayi yana ɓata fuska, da alama ba haka ya soba. Da ƙyar ya iya tashi muka shiga wanka tare, a gaggauce mukai muka fito, batare da mun tsaya neman abinci ba muka shirya, tea ɗin dana haɗa manama cayay muje masha a mota, shi dai maigadi ya miƙa masa nasa tare da kuɗi akan ya sayo bread mun makara yau. A motar kuwa muka sha tea ɗin abin dariya da tausayi (lol😂😜). Aiko yau ina rakasa office na fito dan ban kammala aikin jiyaba nima, a ƙofar office ɗin naci karo da rose, ko kallonta banyiba nai gaba abina, harna sauka ƙasa ina jiyo idanunta dake yawo a jikina, nidai ban fasa neman tsarin ALLAH da ga sharrinta ba harna ɓace abina.

     Kusan sha biyu da wasu mintuna ya kirani akan idan anfito salla nazo na samesa. Amsa masa

nai da to ana idarwa kuwa can na nufa, shi kaɗaine a office ɗin yanata ayyuka, duk da da alama shima yanzu ya shigo ɗin, ban zaunaba har sai da ya bani izinin zama. Tasowa yay daga kujerarsa ya dawo ɗayar dake kallon wadda na zauna, ya kamo hannayena cikin nasa yana mai tsareni da idanunsa nan masu takurani. “Miemaa na amince kije gidan Alhaji kokino, amma da sharaɗi”. Cike da ɗoki nace, “Minene shaɗarin?”. “Sharaɗin shine kwana ɗaya kacal da yini biyu zakiyi, idan yayi tsaurine kikai biyu, sannan tare zamuyi aikin dan bazan taɓa barinki ki shiga wannan aikin mai haɗari ke kaɗai ba”. Rungumesa nai saboda jin daɗi, hannu biyu ya amsheni yana murmushi, nace, “Na yarda da duka sharaɗin, ALLAH ya bamu sa'a da nasara”. Yace, “Amin Beejay, yanzu zaki tashi Sadiq ya kaiki gida kiɗan shirya, shine zai kaiki inda zaku haɗu da baba, sai ya ƙarasa da ke”. “Wow da wuri haka?, insha ALLAHU zaka sameni fiye da yanda kai tunani, kaida kaitamin addu'a boss ɗinmu abin alfaharinmu”. Ɓata fuska yay cikin wasa yace, “ke da wa?”. Ganin yanda yay da fuska ya sakani ƙyaƙyƙyawa da dariya, “Ni kaɗai mana, sai su oga Jabeer ”. Hararata yay, “K nifa kibarma kirana da wani boss na gaji da ji”. Kunya naji sosai, dan haka na ɓoye fuskata a ƙirjinsa ina dariya.

★★★★
Chapter 131 · 0% Book details