← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 168

Sashe 125

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Page 52
................Wata tarbar karramawar na sake iskewa wajen ƴan office ɗinmu nima, suka baibayeni mazansu da matansu suna mai tayani murnar aure da samun boss matsayin miji, su Ada iyayen gulma harda cewa na musu wayo nai wuf da boss. Ni dariyama suka bani wlhy. Na musu godiya da fatan suma ALLAH ya basu nasu musha biki. Fassara muku farin cikin dana tsinci kaina a ciki saboda dawowar su Nazifa station ɗinmu ɓata lokacine, muka sake rungume junanmu daɗi na ratsamu, a karo na uku mun sake kasancewa tare, ALLAH dai yasa muci amfanin wannan ƙawance har a gidan aljanna. Gaba suka tasani da sheri wai nayi ɓul dani kodai an samar musu baby?. Yinai kamar banjisu ba, da suka isheni sai nace suje su tambayo boss ɗin. Dariya suka sanya kowa na miƙewa duk suka koma mazauninsu da aka basu suma a office ɗin namu. Daga haka na samu lafiya daga iskancinsu.
Ban tarar da kowanne aikiba, Ummie ta sanarmin ai duk oga Jabeer ya bata ta ƙarasa ayyukan dana bari, naji daɗin hakan sosai, saina miƙe ƙafa ina hutawata, da wannan lokacin nai amfani wajen zurmawa duniyar tunane-tunane kala-kala, ciki harda neman amsar yanda akai aurena da Yah Qaseem ya fasu aka maida shi kan boss, sai abinda na gani yau a ɗakina da duk nama rasa wane tunani ya dace nayi akan hakan, dan duk wanda nayi mai ƙyau sai naga bai zauna da al-amarin ba sam, sai marasa ƙyawunne keyin dai-dai. Ban sakejin ɗuriyar boss ba har muka fita sallar zuhur, bayan an idar mun fito su Nazifa ke faɗin ya kamata muje muci abinci, dan wasu a cikinsu ma basu ko karya ba suka baro gida, nima ɗin sai yanzun na tuna ban karyaba, ruwan tea ne kawai a cikin nan nawa. Shiru nai ina tunani, ni dai banda damar cewa zan bisu wajen cin abincin nan boss bai saniba, ni kuma bana wani son zuwa Office ɗinsa.... Taɓanin da akai ne ya katse tunanina, na sauke numfashi da kallon Rebecca da hannunta ke a kafaɗata, "Matar nan ina kika tafine? anata magana". Murmushi na mata ina tura hannayena cikin aljihun wandona, "Ba komai, kinsan zuciya da tone-tone, inaga kuje kawai banajin wani yinwa nikam". Har Ummie ta buɗe baki zatai magana sai Zuhrah ta katseta, "Kai inagama fa bai kamata ta bimu ba mijinta bai saniba gaskiya, tunda yana cikin station ɗin shima ta fara sanar masa, yanzufa ba da bace da muka saba shirmen mu kai tsaye". "Hakane kuma gaskiya" cewar Nazifa tana komawa kalar tausayi. Fahimtar inda ta dosa yasa muka kwashe da dariya mu dukanmu, dan itama dai bai wuce nata auren da ya rage six weeks ta tuno ba. Office muka koma bisa shawar Zuhrah, ita da Ummie kuma suka tafi sayo mana abincin..
★★★★★★
Tunda suka baro cikin Barrack ɗin Jay ke ƙullawa da kwancewa, lumsassun idanunsa da launinsu ya gushe da ga farare zuwa ɗan jaa ya buɗe a hankali yana furzar da nannauyan numfashin da har sadiq sai da ya saci kallonsa ta mirror. Wayarsa ya ɗauka ya shiga daddanawa kafin ya saka a kunne dayin sallama, Munkaila na amsawa bai tsaya bi takan gaisuwar da yake masaba yace, "Zan tura maka wasu sunaye guda huɗu, inason daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu a nemomin inda suke, sana'arsu ko aikinsu, abokan mu'amularsu na rayuwa dana kasuwanci". "Okay sir insha ALLAHU zanyi ƙoƙari, akwai ma waɗan can ayyukan na wajena guda biyu suma duk na kammala". "Saika haɗosu kawai". "Okay Sir" Munkaila ya faɗa cike da girmamawa.
Suna isowa cikin station ɗin baima jira Sadiq ya buɗe masaba ya buɗe da kansa ya fita, sallamar Sadiq ɗin yay akan yaje zuwa biyar sai ya dawo, shi kuma kai tsaye massallaci ya nufa saboda lokacin salla yayi.
Bayan an idarne ya fito zai koma office yaga su Bilkisu, sai dai su sam basu ganshiba dan hankalinsu baya ta wajen, yazo zai ɗan gittasu yaji hirar da sukeyi, ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yaba hankalinsu, yanda yake musu kallon yara ƙanana bai zaton sunada zurfin tunani irin hakaba, dan daidai zai wucene maganar zuhura ke shiga kunnensa akan bilkisu bai kamata ta bisuba mijinta bai saniba. Sai da ya shiga office ya zauna sannan yay kiran gidan abincin da yaji su Ummie zasuje, umarni ya bada akan a basu duk abinda suke buƙ

ata kar kuma a amshi kuɗinsu shi zai biya. Kasancewar sa babban Customer babu ɓata lokaci aka haɗa musu komai.
Su Ummi basu san wainar da ake toyawaba, sudai sukaga an haɗa musu abinci kala-kala harma da wanda basuce ɗinba, amma dai-dai abinda zasu iya cinyewa ba almabazaranci ba, sannan akaƙi amsar kuɗinsu, da suka matsa da tambaya aka basu amsa akan an biya. Sosai sukaita mamakin da tambayar waye ya biya ɗin?, babu wani ɓoye-ɓoye aka sanar musu.
Tunda suka dawo suka sanarmin yanda akai wajen sayen abincin sai naita mamaki akan yaya akai yasan zasuje? Shin kodai idanu ma yasa a sakamin ne? Kai bana tunanin hakan daga garesa, sai kace wanda bai yarda dani ba. waya na ɗauka na tura masa saƙon godiya da fatan alkairi.

Jawaad na zaune ya duƙufa aiki saƙo ya shigo masa, kasancewar Number da kowa ya sansa da itace ya zata akan wani aiki ne, dan ya kashe wayarsa da mutane masu muhimmanci kaɗai ke ciki, gudun kar Alhaji babba kosu Ummah su kirashi susan ya dawo, baiyi tunanin bily bace tunda bai saka Numbar ta anan ba, ɗauka yay ya duba, a mamakinsa sai yaga itaɗin ce ashe, yay murmushi da ɗan lumshe idanu ganin abinda ta rubuto, ajiye wayar yay kawai ya cigaba da aikin gabansa. Cak ya tsaya daga abinda yakeyi yana mai ƙure takardar daya saka sunayen da suka samo wajen Umm-Anum da ido, waya ya ɗauka da hanzari yay kiran Jabeer, yana ɗagawa yace, "Jabeer bama wani ya kawo min file ɗin matarnan".
Daga can Jabeer ya amsa masa da "to". babu jimawa kuwa sai gashi ɗan aike daga jabeer yay knocking, damar shigowa ya bashi.
Cikin girmamawa ya ƙame da sarama Jay kafin ya gaida shi, sannan ya ajiye file ɗin hannunsa. Ɗaga masa hannu Jay yayi alamar ya tafi kawai. Yana fita ya ɗauki takardar dake da sunayen bayan ya zagaye sunan macen dake a ƙarshe da jan biro, sannan ya buɗe file ɗin wajen Jabeer. tsai Jay yayi a zaune yana ƙarema sunayen kallo, sam babu wani banbanci hatta da sunan gari, waya ya ɗauka ya shiga dannawa. Kira yayi, bugu biyu aka ɗauka, bayan sun gaisa yace, "Malam Rabo, yanzun nan inason Ka binciko min Hajiya Safara'u a cikin ƙauyen nan naku, gashi nan zan turo maka cikakken sunanta da sunan mahaifinta nasan zaka gane, banason ɓata lokaci, yanzun nan nakeson kabar tasharnan ka tafi". "Insha ALLAHU kuwa oga yanzun nan zanbi motar datai lodi kuwa, koma na amshi mashin ɗin Madu naje yanda zanfi sauri". "Hakan yayi, ka zuba mai idan ka dawo sai a bashi wani abu shima". "To oga babu damuwa, sai ka jini".
Jay na ajiye wayar ya maida dubansa ga file ɗin yana bin komai dalla-dalla, dogon nazari ya shiga akan abinda ke cikin file ɗin da wanda ke a ƙwalwar kansa, 'Wato na fahimci akwai wani kuskure da nayi ƙwarai da gaske' yay maganar a fili yana dafe kansa, takarda ya ɗauka ya hau rubutu, sai kuma ya ajiye biron ya kwanta jikin kujera da faɗawa duniyar tunani.
Rasuwar gimba ta rikitashi ainun har yama manta abubuwan da ya kamata ace ya bibiyesu. Akwai Number ƙarshe da gimba yay waya da ita ya kamata yasan wanene ma? da wuri, sannan matarnan da gimba ya ambata ta gidan Alhaji kokino tabbas da itane suka taɓa haɗuwa a gidan Alhaji Kokinon, kuma itace tai aiki a gidansu kenan? Idan binciken ya zama dai-dai. Yaya akai hakan ta faru bai taɓa fahimtaba kai tsaye, kalamanta na wancan karon sun isa su bashi dukkanin amsar da yake buƙata. tabbas wani baƙon al'amarine da bai taɓa sakashi a lissafisa bane ya shigo masa kai yanzun nan musamman akan kashe Gimba da akayi yake tunanin da babu gaira babu dalili. Abinda yake tunanin ya faru akan kisan gimba ba shi bane ashe. Alhaji kokino sunyi abotar siyasa da Abba kamar yanda Ummuna ta faɗa, sun kumayi ta kasuwanci, indai har matarnan tayi aiki a gidanmu mizaisa ta koma can gidan tana aiki? Lokacin da aka sace Alhaji kokino itace ta bani dukkan sirrikan da nabi na samosa a hannun ƙaninsa, maganar gimba a al'amarin, yace akwai dalilinsa na zuwa aiki ƙarƙashina, na kuma nemeta zanji abubuwa masu muhimmanci. Idan har zan haɗa wannan maganar tashi da maganganunta na waccan ranar da muka taɓayi to lallai tamin farin sani kenan?. Miƙewa Jay yayi yana ɗan dukan tabirinsa da faɗin, "Yah ALLAH ". Ya sa
Chapter 125 · 0% Book details