Sashe 130
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kai, dan na kula shi mutum ne mai tsananin kishi. Yinai kamar banjisa ba na hau gyaran agogon ƙarya, “Nasan kin jini ai”. Yay maganar daɗan kallona. “Nifa banji komai ba, yi haƙuri mikace?”. Shareni yay muka ƙarisa, bayan mun gaisa da su Sadiq ya buɗe mana mota muka shiga.
A motarma bai hutaba, aiki ya keta faman yi har muka iso office, nazata zamu biya ta wajen maman Yara, amma jin baiyi maganarba saina share abina. Yauma sai da na masa rakkiya har office sannan na koma namu inda na tarar da Rebecca kawaice tazo a cikinmu, itama ta cemin nanda goma zata fita saboda aikin da boss ya raba musu jiya, akwai abinda tazo yi shiyyasa amma da sai ta kammala zata shigo kamar su Ummie, ni dama bandani ya ba shugaban ƴan kishin, dana tambayesa bayan mun fito amsar daya bani itace, yanzu duk inda nasa ƙafa yana wajen ai, duk aikina zai kasance tare da shine insha ALLAH, nidai najisane kawai, watarana ai za'a iya canjama wani wajen aiki a cikinmu ko wani abun daban, naga yanda zaiyi kuma. Tana aikin muna hira danni aikin gabana mai sauƙine, jiya nema oga Hafiz ya banishi da yamma. Goma nayi ta fice, saina maida hankali ga nawa aikin. Yau bamu da yawa a office ɗin, mafi yawansu sun fita operation, wasuma ko office ɗin basu zoba.
Wajen sha biyu na amsa kiran boss da yaymin, na iskesa shi da Jabeer, na gaishesu sannan nace masa gani. “Na ganki ai” ya faɗa yana cigaba da aikinsa a Computer batare da ya kalleni ba. Ina daga tsayen ban zauna ba, dan baibani izinin yin hakanba, yanzu a matsayin shugaba yake wajen aiki ba miji ba. Kusan mintuna huɗu sannan ya juyo gareni yana tattare takardun gabansa da yake aiki akansu. Miƙomin yay fuskarsa dai babu walwala sam, a boss ɗinsa dana sani yake. abinda zanyi ya faɗamin, na amsa ina jinjina masa kai, kafin na juya na fita.
Aikin nan daya bani shine ya jani lokaci daƙyar na turesa naje nai salla na dawo na sake cigaba, a lokacin ne su Zuhrah suma suka dawo, sam banajin yunwa, koda ya kirani akan miza'a kawomin nace masa ni banama jin yunwa, baice komaiba ya yanke wayar, bayan wasu mintuna saiga doughnut da fresh milk an kawomin. Murmushi kawai nayi nama wanda ya kawo godiya na cigaba da aikina, shine su Nazifa suka iske inaci, ƙarshe ma tare da su muka ƙarisa.
★★★★★
Ƙarfe biyar muka bar office, barci nakeji sosai a idona, dan haka naɗan jingina kaina da kafaɗarsa. Ɗan kallona yay ya ɗauke kansa yana murmushi, tun ina kallon aikin da yake a lap-top har barci ya ɗaukeni a haka. A hankali na buɗe idona jin an jamin hanci. “Sorry kin gaji ko?” yay maganar yana shafamin gefen fuska. Kaina na ɗan ɗaga masa da lumshe idanu na sake buɗewa a kansa. “Daure mu shiga, bazamu jimaba, sai mu tafi gida kinji”. A hankali nace to ina tashi.
Koda muka fito da mamaki na kallesa, “Lah! Dama nan mukazo?” na faɗa cike da zumuɗi. Ƙin tankamin yayi, sai ma nunamin gidan su Amina da yay da hannu alamar muje. A tunanina nan zamu fara shiga kafin gidan Dad, dan haka nai gaba raina fari ƙal.
Cikin farin ciki Mama ta tarbemu, sai faɗi take, “Kai masha ALLAH, lallai Jawaad kana kularmin da yarinya sosai, kaga duk ta sake canjawa, kai Alhmdllh”. Murmushi mukaita yi mudai, inata ɓoye fusaka dan naji kunya kuma ALLAH. Tunda naga banga Amina ba nasan basu taso aikiba, mama ta nuna mana ɗakin kusa da nata, “Ku shiga to, dama yanzu na gama kimtsata, mun samu yanzu taci abincin Alhmdllh”. Shine ya amsama mama da Alhmdllh, ni dai da ba fahimtarsu nai ba sai nabi bayansa kawai.
Babbar mace muka tarar a ɗakin kwance, kallo ɗaya nai mata na gane maman yara ce da nagani jiya a video call, kenan nan aka kawota ashe? Shine koma faɗamin baiyiba. Kallonsa nai irin na tuhuma ina kumbura fuska, ya ɗan waro idanu da ɗage kafaɗatsa alamar “shima babu ruwansa”. sake tura bakin nai, yaymin gwalo da ɗauke kansa daga gareni..
Shigowar mama tasa na ƙyalesa, yace, “Mama barci take ne?”. “Eh to inaga ta koma, dan tun allurar da sukai mata jiya da daddare bata gama sakinta ba, likita yace da gani ko barci bata samu a can shiyyasa ta jigata sosai”. “Humm” ya f
aɗa cikin ƙunar rai tare da matsawa gaban katifar da take ya durƙusa saitin fuskarta.
Jin motsin mutum gab da ita yasa ta buɗe idanu a hankali, ƙure boss tayi da kallo ko ƙyaftawa batayi, har zuwa wasu sakanni, sai kuma ta saki murmushi cike da ƙarfin hali, hanunta dake rawa ta ɗaga da ƙyar ta miƙo masa, babu musu ya miƙa mata nasa shima ta riƙe, murmushin ta sakeyi hawaye na ziraro mata akan kumatu.
Hawayen ba ƙaramin sake tunzura zuciyar Jay sukayi ba, ya risinar da kansa ƙasa yana haɗiyar zuciya, jijiyoyin kansa harsun fara mimmiƙewa, cikin muryarta da bata fita sosai tace, “Jawaad”. Da sauri ya ɗago idanunsa da sukai jazur ya zuba mata. “Na godema ALLAH da ya ƙaddara haɗuwarmu kafin nabar duniya, nagode ma ALLAH dana samu hanyar da zan ƙarasa abinda na fara kafin nabar duniya. Babu isashen lokaci Jawaad, kayi ƙoƙari a kwanaki biyun nan daga daren yau zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu kaje gidan Alhaji kokino, akwai wata tukunya na nan a tsakkiyar ƙarƙashin gadonsa, ka tabbatar an ɗakko maka ita, karkayi wasa da an fiddota daga gidan ka fasata, sannan ka ƙona abinda ke ciki koma minene, itace makarin........” tari ya sarƙeta.
A take hankalinmu duk ya tashi, ya tallafota jikinsa yana girgizata da kiran sunanta duk ya ruɗe. Da ƙyar aka samu tarin ya lafa, yanda ta jigata yasa bai nema jin abinda take son faɗarba tunda ta faɗi mai muhimmancin, mama ta gyara mata kwanciya dan danan sai barci yay gaba da ita. Fitowa mukai a ɗakin jikinmu duk a sanyaye.
Mama ce ta fara magana cikin damuwa, “Tunda ta farka maganar da taketa maimaitawa kenan Jawaad, na rasa wace irin tukunyace wannan?”. Nannauyan numfashi ya sauke yana gyara tsaiwarsa, muryarsa cike da ɗaci yace, “Koma wace irice, kuma kota micece insha ALLAHU zan ɗakkota mama. Bara muje gida Doctor yace zai zo anjima ya ida kawo mata sauran maganinta sai ya ƙara duba jikin nata”. “Eh haka yace mana, ALLAH ya bada nasara to amma banda ganganci dan ALLAH, karkuma a manta da addu'a kunji ko?..............✍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[1/22, 2:43 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🥚Ƙwai Ciki Ƙaya🥚
.
Book Two
.
Billyn abdul:
Page 54