← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 168

Sashe 31

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tsahon lokaci tare da ita yana mata tambayoyi kala-kala, wasu ni kaina idan yayi hanjin cikina saisun kaɗa balle ita da akemawa, gaba ɗaya duk ya gama rikitata da gizagonsa, sai dai ina jinjina masa akan yanda ya samu ƙwarewa akan kutse cikin al'amuran mutum yay bincike, har kai da yakemawa ɗin ka kasa saita kanka wajen bashi amsa ta gaskiya, dan lokacin da yarinyar ta iso a take-takenta na farko banga alamun zata bada haɗin kai ba, amma yanda ya fara bi da ita sai naga tuni ta zurma tana faɗin harma wanda bai tambaya ba ɗin. Ina kuma ƙara samun ilimi na aiki nima a wajensa sosai. Lokacin da muka kammala anata kiran sallar zuhur, dan haka mukayi a cikin wajen har shima da wasu mutanen, dan akwai masallaci ƙarami da sukayi, hakan yasa wajen ya sake burgeni da ƙaramin nutsuwa. Koda muka idar tafiya tayi, nima na samu waje na zauna ina jiran ya fito nai masa sallama na wuce.
Kiran da ya shigomin a waya na ɗaga, Ummie ce, bayan mun gaisa take tambayata ina inane? Dan taje gidanmu akace na fita. Amsa na bata da cewar naje wani wajene, yanzu kuma zanje na wanke kai na wuce gidan inna Zainabu, daga haka mukai sallama akan zata sameni a wajen saloon ɗin ko gidan inna zainabu, na amsa da to na ajiye wayar. Ina ɗagowa muka haɗa ido da boss dake magana da wani da nake ƙyautata zaton sunsan junane. Janye idona nai kamar yanda shima ya ɗauke nasa, basu wani jimaba wancan yay ciki shi kuma ya nufi hanyar fita. Bin bayansa nayi ina ƙunƙuni, danni ɓatamin lokaci aketa famanyi.
Kusan a tare muka ƙarisa jikin motar da nake ƙyautata zaton da ita yazo, nayi zaton gimba ne ya kawosa, amma sai naga saɓanin hakan, dan mazaunin driver ya buɗe ya shiga, ta gefen nasa naje na tsaya, nace masa zan wuce gida nima.
Kallona yay ya ɗauke idonsa, sai da yay ma motar key, batare da ya kalleni ba yace, “Kina ɓatan lokaci fa, ko jira kike na ɗaukeki na sakaki ne?”.
‘Innalillahi...’ kuji sabon sharri, na faɗa a raina ina kumbura fuska, danni dama abinda nake gudu kenan yace mu tafi tare, to amma yaya zanyi, babu fuskar wargi a garesa, dan haka na zagaya na buɗe gefen mai zaman banza na zauna.
Baice komaiba yay reverse tare da harba motar saman titi da ɗanbanzan gudu. Idanu na lumshe ina faɗin ‘Ga wanda yafi Yah Qaseem shegen gudu da mota’. Babu mai magana a cikinmu, sai shi da ke murza sitiyarin a hankali tamkar bayaso. Bai tambayeni ina zaniba, nikuma ban sanar masaba inajin shakkar magana dan sai wani shan ƙamshi yakeyi fuskarsa a ɗaure sosai.
Tafiyar da bata wuce mintuna goma sha biyu ba muka iso wani waje, da mamaki na kalli abinda aka rubuta (LADIES MIRROR) sannan na kallesa shima, ta yaya akai yasan saloon zanzo to?, cikin ƙarfin hali nace, “Nifa ba nan nake zuwa ba”.
ATM ya miƙomin batare daya kula maganata ba, nai ƙasa da kaina ina sake faɗin, “Ai ambani kuɗin a gida”. Bai tanka minba nanma, sai ajiyemin atm ɗin da yay a kan cinya tare da ƙaramar takarda. Tamkar zan fasa kuka haka naji, na buɗe motar na fice ina sake juya al'amarin mutumin nan a raina, aunty Shahudah tasha wahala yasin, ni saima ta bani tausayi, ƙilama wannan halin nasane ya sakata gudowa gida ‘Mtsoww’. Da wannan tunanin na ƙarasa cikin wajen da ya gama haɗuwa, dan yafi inda nake zuwa nesa ba kusaba. gashi ƙaton gaske. Yanda ma'aikatan wajen suka tarbeni sai abin yaban mamaki, abin akwai birgewa. Sai da na zaunane bayan na sanar musu abinda nake buƙata sannan na sami duba takardar daya haɗomin da ita, sai naga ashe password ɗin Atm ɗin nasane ya rubuta min, samun kaina nayi dayin murmushi.
An wanke min kaina tsaf da tafin ƙafa, aka gyaramin ƙumba, wadda ta wanke min kance ta bani shawarar nayi kitso, a cewarta su inhar zasu maka aiki suna duba yanayin gashinka su ɗoraka a ƙyaƙyƙyawan tsarin da bazai karye ba, kuma zai dinga tsaho, daɗin hakan da mutane ke shigane ke sakasu sake dawowa daga nan saisu zama basu da wajen zuwa sai nan. Murmushi na mata, ina cewa “Kodai za'amin daɗin bakin ƴan kasuwa ne?”. Kanta ta girgiza tana murmushi, “Sam ba haka bane auntyna, duk abinda zakiji daga bakina shine gaskiya, Gimbiya tana ajiye ingantattun kayan aiki da nagarta a wajen nan, waɗanda daga

kowacce duniya kake zaka yaba”. Kasancewar nasan boss ba jirana zai tsaya yiba sai nace, “Okey babu damuwa amin kaɗan to”.
Wani sashen daban da inda akai min wankin kai aka kaini, mutum uku kawai akema kitso, muka gaisa sannan na zauna nima, wadda zataimin ce ta iso kusa dani, muna cikinyi idanuna suka sauka akan ƙaton hoton dake sama a wajen, wanda naga wanima a can inda na baro, sai dai nesa da yay danine yasa banga waɗanda ke a jikiba, anan kam ras nake kallonsu kamar nayi magana su amsa, ƙyaƙyƙyawar mace hamshaƙiya ta gaske ce, tasha alƙyabba mai azabar ƙyau dake nuna jinin sarautace ita, gefenta ma ƙyaƙyƙyawan namijine mai tarin kamala da cikar haiba, kai tsaye na ganesa shi, dan kuwa dai sarkinmu ne Muhammad Sameer Saifudden, a raina nace ‘to ko matarsa ce wannan ɗin?’....... Maganar wadda kemin kitso ta katse min tunani da faɗin, “Duk wanda ya zauna nan baya gajiya da kallon hoton nan na sarauniya MUNAYA uwargida ga adalin sarkinmu, ita kanta wani lokacin har kishin hakan takeyi idan ta shigo takan juya hoton ya ɗau tsahon lokaci a kife”. Duk yanda naso shareta saina kasa, nai guntun murmushi, nace, “To miyasa zata barshi tunda ba dokar ƙasace ta tilasta a ajiyeba?”. kafin ta samu damar bani amsa, ƙyawawan ƴammata uku da yara biyu suka shigo wajen, biyu masu tsananin kama da Sarki Sameer, sauran kuma naɗan yanayi dasu sai dai basa tsananin kama, ukun zamu iya sa'anni dasu, biyun kuwa bazasu wuce shekara goma sha uku ba. Cike da girmamawa naga ma'aikatan na gaishesu, sai dai yanda suke amsawa babu wulaƙanci sai suka birgeni, gashi sai murmushi suke mana, nima sai na maida musu murmushin kamar yanda sukeyi, cikin manyan ɗaya ta miƙomin hannu mukai musabaha tana faɗin, “Kitsonki yayi ƙyau”. “Nagode” nace mata a taƙaice. Sauranma duk muka gaisa, suka kuma gaisa da sauran da muke zaune.
Ɗaya a Ƙaramar tace, “Aunty Amaturrahman nidai irin kitson auntyn nan nakeso” tai maganar tana nunani. Wadda aka kira da Amaturrahman ɗin ta amsa mata da cewar, “Okey Safah sai a miki ai, burina dai ayi kitson kamar yanda Ummu tace”. Ɗayar tai ƴar dariya idonta akan waya, tace, “Mudai dan ALLAH karki cikamana kunnuwa da ihunkin nan Safah, Marwah dai nasan bamai jinta, inba hakaba ALLAH muka koma saina bama kowa labari a masarauta har Momma”. Ɓata fuska yarinyar tayi, tace, “Ai bazanyiba, salon kisa su Jalaludden Su ringa rainani ko Aunty Meenal? Ni wlhy wajen Uncle Sauban zan koma india can babu ruwan mutum da wani kitso ko nabi Aunty Amatullah Niger”. Dariya sukai mata, banda wadda suka kira Marwah shugabar miskilanci da jin kai, daka ganta kaga Sarki Sameer Saifudden sak kamar yay kaki ya ajiye, ni dai ina saurarensu ne sama-sama. Bayan an gama minne na miƙe nai musu sallama na fita, ashe wajen ɗaukko Atm ɗin boss dana saka a jakka gudun basai naje wajen biya naita dube-dube ba na yarda ɗan abinda ID cards ɗina suke ciki da wasu passport ɗina dake a tare.
Ina cikin biyan kuɗin wayata tai ring, na kalla kamar bazan ɗagaba saboda sabuwar Number ce sai kuma na ɗauka na saka a kunne batare da nayi magana ba, daga canma shiru akayi, hakanne ya sani cewa, “Asslamu alaikum wanene?”. “Kin gama?” muryar wanda banyi zato ko tsammaniba ta daki kunnena a bazata. Da sauri na cire wayar a kunnena na sake kallon Number, gabana sai faɗuwa yakeyi, dan nasan nidai baida Number ta, jin an yanke wayar na amshi atm ɗin da ake miƙomin na fice da sauri domin tabbatarwa.
Jinai wani abu ya tsirgamin daga saman kai har yatsan ƙafa saboda ganin motarsa fake a inda ya tsaya ɗazun, a fili nace, “Mikenan? Zaunawa yay jirana?’. Azababben horn ɗin daya danna ne ya sani nufar motar tamkar mai tsoron hakan. Nasan duk abinda zan zaunayi bayan shiga motar laifi zai zama kuma, hakan yasa na buɗe na shiga. Baiko kalleniba ya tada motar muka fice. Sai da muka ɗauki hanya nai dauriyar cewa, “Dan ALLAH kayi haƙuri sir, wlhy nazata tafiya kayi ne, shiyyasa da suka ce na zauna sumin kitso na yarda”. harara ya ballamin ya ɗauke kansa ya maida ga titi. Ban sake cewa komaiba, nacigaba da kallon titi, kamar yanda shima yake gudu kamar shi kaɗaine a titin. Wayarsa ce ta shiga ruri,
Chapter 31 · 0% Book details