← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 168

Sashe 114

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ama yaranmu sukan ɗanje musu, idan kuma sabga ta tashi matarsa na zuwa har cikinta ya shiga wata takwas. Rana tsaka yazo ya sanar mana wai tana asibiti babu lafiya, likitoci sunce ɗan cikinta ya samu matsala cireshi zasuyi dan rabin jikinsa a ruɓe yake, ma'ana dai bamashi da rai kenan, suna buƙatar kuɗaɗen da za'ai mata tiyatar, shi kuma na wajensa basu kaiba amma dan ALLAH mu ranta masa a hankali zai biyamu idan komai yay dai-dai. To mudai bai samu ko sisiba daga garemu, dan bamu dashi saboda kuɗin sunda yawa gaskiya, haka ya tafi. Mukuma anan mukai shiri domin zuwa mu duba matar tasa sai dai kuma mun manta bamu tambayesa asibitinba. Haƙura mukai muka zauna zaman jiransa kozai sauyo saiya kaimu. To adai ranar bai dawo ba sai washe gari mu mukaje can gidan da yake hayar muka tambaya, daga can akai mana rakkiya asibitin, tun kuma kafin muje an sanar mana ai anmata aikin an cire ɗan babu rai. Amma abin mamaki sai muka isketa da jaririyar yarinya a hannu. Babu wanda ɗunbin mamaki bai kamaba a cikinmu, har muka kasa haƙuri mukai magana tunda ita amma ce ɗa namiji aka cire mata kuma baizo da raiba. Amma sai cewa sukai ai jaririyar dake wajenau itace ƴar tasu, yaran ƴan biyu ne, ɗayane babu rai ɗaya da rai. Sam bamu yarda dasu ba, hakan yasa mukai fushimuka bar musu asibitin, munta sauraren muga Adamu ya biyi bayanmu yay mana cikakken bayani akan gaskiyar al'amari sai mukaji shiru, a haka har shekaru suka shuɗa yarinya ta fara girma, kowa dai yasan tabbas ƴarnan ba ɗiyar Adamu bace akwai abinda suka ɓoye dangane da samuwarta, amma kuma a zahiri ga wasu abu na kamanninsa na bayyana ga yarinyar, sannan idan ka nutsu da kallon yarinyar lallai zakaga wasu abubuwan na Asiya tattare da ita dukda sam batayo asalin fuskarta ta fulaniba dan Asiya farace tas kuma ƙyaƙyƙyawar gaske, wahalhalun rayuwane kawai suka ɓoye kaso mafi yawa daga ƙyawunta, wannan abu shine ya kawo mana ruɗani maiban mamaki wanda har a yanzu da kuke a gabana bamu fita daga cikinsaba, kuma har Adamu ya rasu shida matarsa basu taɓa faɗa mana komai daya shafi yarinyarba”.
Alhaji babba daketa sauke tagwayen ajiyar zuciya na tausayin gudan jinin nasa da son zuciya ya saka mahaifiyarsa nisantasu ya share ƙwallarsa, muryarsa a raunane yace, “Tabbas bakai dake bamu labarin nanba, hatta dani nan ka sake dulmiyani a ruɗani, taya za'ai kuna zargin ba ƴarsu bace amma kuma take kamanni dasu ta wasu abubuwan? Koni dana kalli hotonsa da yarinyar naga tabbataccen jini na haƙiƙa tattare da junansu, na tabbatar koda kutu akaje wannan yarinya za'a iya tabbatar da tasuce babu wani haufi a cikin hakan”. “Tabbas hakane Baba, sai dai mai warware ainahin gaskiyar lamari sai ALLAH sai kuma su da suka kasance da yarinyar, gashi kuma a yanzu duk basa a raye”.
Jawaad da baice ƙalaba, saima latsa waya da yakeyi, batare da ya ɗagoba yace, “Yanzu Kunsan inda yarinyar take ku?”. Yanda yay maganar babu wasane ya saka Alhaji babba da Malam ɗan inna kallonsa, dukda yasan kallon nasa suke bai ɗagoba, baikuma gyara fuskarsa dake a ɗaureba. Malam ɗan inna da duk ya daburce yace, “E.. e eto saurayi yarinyar dai tana gidan da ayka zauna”. Ɗago idanu Jay yay ya kallesa, “Kenan babu wanda ya ɗauketa a cikinku bayan rasuwar mahaifinta saboda kunaji a ita ba jininku bace bayan kuma UBANGIJI ya baku komai a bayyane tunda ya fidda kamanin iyayenta a jikinta?”. “Saurayi ba haka bane ba”. “To yayane?”. Kasa cewa komai malam ɗan inna yayi, sai zufa data jiƙe ta cikin babbar riga, shi dama tun shigowarsa bai hangi sauƙi da ga yaron nanba sam.
Ajiye wayar Jawaad yayi yana fuskantarsa sosai, “Malam da farko dai yanzun bara na fito maka a mutum, wannan da kake gani dai shine mahaifin Adamu makahon, mijin ƴar uwarka Sa'a wanda ta gudar masa da ɗa bisa son zuciyarta, ina fatan ka gane”..
Sallalami malam ɗan inna ya kwaso daga samaniya ya dire bisa ƙasa yana zare idanu jikinsa na ɓari, “Wai dan ALLAH da gaske kana nufin Mati ne? Dama kana raye? Adamu yayta nemanka ruwa a jallo amma ko labarinka bai taɓa samuba daga wani, dangi da duk muka sani a baya mun sakashi ya abi amma duk sun rasu bai samu ko guda ba a ciki”.
“Ha

kane Hamza, kasan idan UBANGIJI nason saukar da wata aya ga bayi saiya datse al'amarinsu ya ɓoyesa a rasa bakin zaren a dalilin ƙaddara, muduka ƙaddarace ta ɓoyemu dukda muna a cikin gari ɗaya, nima nasha bibiyar ahalinku dalilin son ganin ɗana ya dawo gareni, sai dai hakan bata kasanceba har gashi ƙasa ta rufe idanunsa, hakan jarabawace, dan tabbas tun daga Zazzafar soyayyar danaima Sa'a har zuwa zaman aurenmu da guduwarta da yarona duk jarabawace a garemu da wata hikima ta UBANGIJI, naso ace na sake ganinsa, naso ace na kwatanta sauke haƙƙinsa dake kaina matsayin mahaifi a garesa, naso ace shima ya tashi cikin ƴan uwansa da a yanzu sune suka zamema rayuwata haske, ALLAH ne yaymin komai da kaini matsayin da nake a yanzu amma ta dalilinsu ne, na yarda abinda kakeso bai zama lallai ya kasancema rayuwarka alkairiba, wanda kake ganin yay kutse ma rayuwarka sai kaga shine alkairin, naso Sa'a so mai tsanani, harnaso bijirema iyayena a kanta, sai dai itaɗin ashe ba itace abinda nake ma hasashenba, wadda iyayena suka auramin ina baƙin ciki da takaici, na ƙuntata rayuwarta a zamanmu sai tazama ashe itace abinda banyi zatonba, dan gashi yanzun albarkacin zuri'arta nakeci ita bata raye, wannan aya ce ga masu ZUCIYA irin tawa, ɗan adam shidai abinda akeso ya nema zaɓin ALLAH akan dukkan al'amarin sa ba wai son zuciyarsa ba”.
Sosai Malam ɗan inna keta faman jinjina kansa, Jawaad dai yana saurarensu amma bazaka taɓa fahintar yanayinsa ba sam, saida Alhaji babba ya gama share-sharen hawayensa sannan Jawaad ya ɗago ya sake kallon Malam ɗan inna, “Na biyu kuma zamuje da kai gidanda suka zauna danka nuna mana yarinyar, mu zamu ɗauketa mu riƙe, basai munsan gaskiyar yanda suka sametanba”.
Sosai ruɗani ya bayyana ga Malam ɗan inna, ya shiga matsar hawaye yana bada haƙuri da musu bayani akan suma basusan inda Bilkisu take zaune ba, amma kwanaki taɗan zazzo gaishesu, sai dai maganar gaskiya ko tazo ɗin basu wani sake mata fuska, danshi sau ɗayama ya taɓa ganinta, kusan shekara uku kenan ya kuma ja mata gargaɗi akan karta sake zuwa masa gida tunda basu da alaƙa da ita, dan saida ya titsiyetama yaji wanene ya nuna mata gidan kafin yaymata korar rashin arziƙi. to amma yaji kwanaki iyalinsa suna gulma wai tana zuwa wajen Ramatu, kuma ma har tayi aure kwana nannan ita Ramatun taje.
Kafesa kawai da kallo Jawaad yay ransa a matuƙar ɓace, ganin hakanne ya saka Alhaji babba riƙe hannunsa yana murzawa alamar lallashi, hannunsa ya zame ya tashi ya fice daga zauren.
Alhaji babba yay murmushi yana girgiza kansa, sannan ya maido kallonsa ga Malam ɗan inna da shima yabi Jawaad ɗin da kallo, “Haka yake yana da matuƙar zuciya, sai dai yanada kirki sosai, shine jikana na farko da ƙanwar Adamu mai suna Bilkisu ta wajen Amina kenan ta haifa, ɗan tsohon shugaban ƙasa da ALLAH yayma rasuwa Alhaji Abdul'aziz yusif tafida”. Idanu sosai malam ɗan inna ya zaro, cikin ɗan rawar baki yace, “Dama yarinyar wajenka ce matar marigayi A.Y tafida?”. “Hakane, gama yaronsu da ya bari nan”. “ALLAH maiyin yanda yaso, ALLAH mai hikima, lallai zaɓin ALLAH shine zaɓi kam bawai son zuciya ba, wanene zai iya mantawa da tsohon shugaban ƙasa Abdul-aziz Yusif Tafida a ƙasarnan ai saida azzalumi, adalin shugaba da har yanzu ba'a ƙara samun makamancinsa ba ma”. Murmushi Alhaji Babba ya dingayi jin ba'a manta da ɗan matarsa ba, surikinsa kuma uba ga babban jikansa. A take ya warwarema Malam ɗan inna gaskiyar al'amari dan gane da bilkisu harma aurenta da jikansa Jawaad, wanda a dalilin hakanne kuma yasaka su ma bincike har suka ganosu ta dalilin kamannin bilkisu da Adomu daya gani, da kuma ƴarsa data rasu Rahmah, wanda yake ganin bilkisu ta ɗakko kamanin Rahama ne saboda ƙarfin jini, to gashi sukuma sunmace basu yarda ADamun ta haifi bilkisu ba, to shi ina zasu kama su fahimci gaskiyar wannan ruɗanin ne. Al'ajabi ya sake kama Malam ɗan Inna har takaisa ga sharar hawaye, yayta ban haƙuri da neman afuwa ga alhaji Babba tundaga laifin da ƴar uwarsu ta zama sila har wanda suma suka tafka. Tarr syka fito har wajen mota yana bama Jawad da yay kicin-kicin da fuska haƙuri shima. Hannu kawai ya ɗaga

masa da jinjina kansa, dan ransa a ɓace yake, kuma bayaso kosau ɗaya fushinsa yakaisa ga aikata abinda bai daceba ga dattijon da zaiyi sa'a da mahaifinsa, gashi koba komai akwai alaƙa.
Sun rabu akan zai faɗama sauran ƴan uwansa komai auzo kuma har gida su ƙara bada haƙuri.
Chapter 114 · 0% Book details