Sashe 116
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yauma kamar yanda ta saba ɗin haka ta ƙimtsa ta fito cikin shirin zuwa gaida takawa, idan da Ummu yazo sukanje tare, idan kuma da amaryarsa ne tare itama suke zuwa, sai idan shi kaɗaine yazo sai taje tare da Anum su gaida shi ko Aunty Mahfuzah idan ta shigo. Yau kam sai suka ɗunguma gaba ɗaya, ita, Anum, Ummu, Bilkisu, sai Anuwar daya shigo gidan babu jimawa shima, dan tunda ya fita salla sai yanzu yake dawowa saboda baisan da Takawa sukazo ba balle yay tunanin harda Jawaad.
Sallama sukai a ƙofar ɗakin aka amsa musu da ga ciki, tare da basu izinin shiga, jikin Umm-Anum sai tsuma yake tanata dai ƙoƙarin dannewa da karanto addu'a a zuciyarta. Anum da Bilkisu ne suka fara shiga, sai Ummu sai Umm-Anum, sai Anuwar a ƙarshe. Jay na kwance a kujera idanunsa a lumshe tamkar mai barci, sai dai shigowarsu falon ya saka ƙirjinsa wani irin mahaukacin bugu irin wanda tunda yake a rayuwarsa zai iya rantsuwa bai taɓa jiba, ya buɗe idanunsa a hankali zuciyarsa na wani irin masifaffen tsitstsinkewa. Akan Bilkisu da Anum da suka zauna gefen Abbun su Anuwar ya fara saukewa, ya maida kan Ummu da itama ta zauna a kujerar da takawa yake zaune, sai Anuwar dake tsaye tamkar gunki idanu a ware yana kallon Jawaad, da alama dai yayi sumar tsayene na bazata. Ya maida kallonsa ga dattijuwar mace data juya masa baya suna gaisawa da takawa, tana sanye da baƙar abaya ta naɗe kanta irin naɗin larabawa. Jiyay gaba ɗaya jinin jikinsa na wani bada zuuuu!! Zuuuu! Zuuuu, bazai iya daurewa har saita juyo garesa ba, a matuƙar ɗokance yake da son ganinta duk da cike yake da fargaba da tsoron kar hasashensu ya zama kuskurene kuma ba itaɗin bace ba. Ya miƙe a hankali ƙafafunsa na harharɗewa, yayinda bugun zuciyarsa da fitar numfarfashisa ke fita a matuƙar guje. Miƙewarsa tai daidai da miƙewar Umm-Anum itama fuskarta ɗauke da murmushi sun gama gaisawa da takawa tanason komawa kusa da mijinta ta zauna sai a ɗora firar, dauriya kawai take itama tana danne halin da take ciki. Lokaci ɗaya sukai tsaiii! Suna kallon juna, kallo mai wahalar fassara ga ma'abocin yinsa da wanda ke kallo, kallo mai saka razani da firgici da ban mamaki, kallo mai ɗarsa tausayi ga duk wanda idanunsa zai iya sauka a kansu shima.
Ƙafafun Jawaad sun kasa ɗaukar gangar jikinsa, Mahaifiya ta wuce gaban wasa, jini ba ƙarya bane musamman irin na uwa da ƴaƴa, ko shekara dubu yay baigantaba saiya gane, shekarun data barsa bazai yuwu ya iya manta fuskartaba musamman da ya zam yana kallonta a hoto a koda yaushe, manyanta kawai da ƙiba da haske ta ƙara na alamun girma da jin daɗi. Ƙasa ya zube bisa gwiwoyinsa jikinsa na rawa, kansa na wani irin Masifaffen sara masa tamkar zai tsage gida biyu, cikin rawar harshe da kwararowar hawaye bisa kumatunsa yace, “Ummuna!”.
Umm-Anum dake tsaye cikin mawuyacin hali da ruɗanin zuciya da gangar jiki idanunta kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa batayi ta ɗaga hannu da ƙyar tana mai nuna shi da yatsanta manuniya jikinta na wani irin rawa, mai kama da Anuwar ɗinta! Wanene shi? Da ga ina yake? Ya akai kamaninsa da Anuwar ɗinta?! Mutum ɗaya tasan duk duniya yana kiranta da wannan sunan, sai dai wanene? A ina yake? A yaushe ne kuma?. Bakinta rawa yake amma ta gaza furta komai, sai tai luuuu baya zata faɗi.
Wani irin wawan miƙewa Jawaad yayi ya tarota jikinsa, dai dai da zaburowar Anuwar shima yana ƙoƙarin tarota, sai kawai hanunsu ya haɗe waje guda suka tallafota a tare......
Zumbur suma ƴan falon duk suka miƙe tsaye, banda Takawa kawai da ya dake abinsa duk da shima jikin nasa duk yay saƙwat. Da ga can Anum ta ƙwala kiran sunanta cikin kukan da takeyi tun farkon durƙushewar Jay a gaban Umm-Anum. Bilkisu ma hawayen takeyi.
Abin tausayi da tashin hankali daga Jawaad har Anuwar kuka suke suna faman girgiza Umm-Anum da kiranta, Jay na faɗin, “Ummuna! Ummuna Please, Ummuna ki buɗe idanunki ki ganni, nine Jay-p ɗinku ke da Abbah, karkice ba hakaba dan ALLAH, dan ALLAH Ummuna zuciyata zata buga ki tashi ki ganni kicemin da gaske kece ba gizo idanuna keyiba, ba mafarkin dana sabayi bane, ba tunain danake dulmiyawa bane, ki tabbatarmin a zahirance kece tare dani Ummuna, kitashi kiga Jay-p ɗinku yazam Jay-p ɗin gaskiya, Dan ALLAH Ummuna karkice baki ganeniba karkice baki sanibaaaaa”. Yaja (a) ɗin ƙarshe da fashe da wanu irin kuka maiban tausayi da tsuma zuciya yana mai kife fuskarsa saman tata.
Anuwar shima kukan yake yana faɗin, “Umm-Anum ki tashi da ALLAH, ki tashi ki faɗamin shiɗin ɗan uwanmu ne da gaske, wlhy inajin ƙaunarsa mai zafi a raina irin wadda ban taɓama wani mahaluki irinta ba, jinake tamkar zan iya rasa numfashina sabida shi, Umm-Anum dan ALLAH kice shiɗin jininmu ne Ummu”.
Duk wanda yace baiyi hawayeba a parlorn nan ƙarya yake, hatta da Takawa saida yasa handkherchief ya tsane hawaye, Abbun su Anuwar ya saka gefen mayafinsa da larabawa ke sakawa saman kai ya share nasa hawayen, kafin ya taka a hankali shima ya durƙusa a gabansu ya ɗago kawunansu ya rungume a ƙirjinsa yana shafa kansu, fuskarsa ɗauke daɗan murmushi ga ƙwalla da suka sake cika idanunsa, a hankali yakai bakinsa saman kan Jawaad ya sumbata, kafin ya maida akan Anuwar shima ya sumbata. Cikin harshen turanci ya shiga lallashinsu da kalamai masu sanyi. Suna cikin haka Ambulance ɗin da Abbu-Siddiq ya kira asibiti ta iso, mata ma'aikatan asibitine suka shigo su huɗu, da taimakon su Jawaad da har yanzu jikinsa ke a sanyaye suka kamata aka ɗaura a gadon gungura mara lafiya, ma'aikatan asibitinne suka fita da ita, Jawaad da Anuwar suka take musu baya suma. Bilkisu da Anum ma miƙewa sukai da sauri sukabi bayansu. Duk miƙewa suma sukai domin binsu, amma sai Abbun Anuwar yace Abu-Siddiq ya maida su Takawa masauki su huta. Noƙewa Ummu tayi akan ita dai zatabi bayansu itama. Takawa baice komaiba suka fito gaba ɗaya, su Jawaad harsun wuce, su Bilkisu ma basu iskesu ba suna tsaye suna jiran fitowarsu Ummu, Ummu, Aunty Mahfuzah, Bilkisu, Anum suka shiga mota ɗaya suka bisu. Abbunsu Anuwar kuma dasu Takawa suma suka tafi a mota guda.
Da taimakon su Jay da suma suke a motar Ambulance ɗin aka fidda Umm-Anum zuwa cikin asibitin, abinka da inda kasan darajar ɗan adam, dan danan likitoci sukai mata caa da taimakon gaggawa, yayinda Anuwar da Jawaad ke tsaye aƙofar ɗakin da aka shiga da ita kowanne cike da tsantsar damuwa, kaɗan-kaɗan saisu ɗago su kalli juna, sai dai kowanne ya kasa magana ma ɗan uwansa ko sau ɗaya, dan harsunansu sun musu nauyi, burinsu kawai suga farfaɗowar rabin numfashinsu masoyiyar zuciyarsu mahaifiyarsu abin alfaharin kowa da tinƙaho.
A wannan halin su Bilkisu suka ƙariso suka iskesu, da ga ita har Anum idanunsu sunyi luhu-luhu saboda kuka, Ummu duk tana riƙe da hannayensu. Idanu kawai Jay ya zuba musu amma bai iya cewa komaiba, sai Anuwar ne ya bama Ummu amsar tambayar da tayi akan ina Umm-Anum ɗin. Isowar su Abbu suma ya saka aka basu wajen zama, domin su Abbu sun kasance zuri'a sananniya mai daraja a ƙasar saudia musamman cikin birnin makka, nagartattun malamaine hafizan Al-Qur'ani mai girma, sunada manyan makarantu na addini da cibiyoyin magunan musulunci da suke badawa da sunansu ya zagaye lungu da saƙon birnin na makka da kewaye da saudia ke alfahari dasu a ɓangarori da dama na ƙasar.
Anuwar da Jawaad dai sun kasa zama, sai da Abbu ya kamosu duk ya zaunar tare da zama tsakkiyarsu. Jawaad shi kaɗai yasan irin matsanancin ciwon da kansa ke masa, amma ya daure ya jure, sai dai ta jijiyar kansa data mimmiƙene kawai zaka iya fahimtar yana cikin mawuyacin hali. Hannu Abbu
ya ɗaura akan Jawaad ɗin daya kwantar da bayansa jikin kujera ya lumshe idanunsa, hakan ya saka shi buɗe idanun da suke jajur ainun, addu'a ya fara karantowa yana tofa masa a kan nasa, Jay ya maida idanunsa ya lumshe jirin da yakeji na ƙara ƙarfi a cikin idanunsa. Luuuu ya kwanto jikin Abbu alamar shima dai koya suman kokuma wani abun dai daban, saurin ɗagosa Abbu yay yana girgizashi, amma ina numfashinsa yay ɗaf daga ƙirjinsa. Saurin miƙewa Anuwar yay shima jiki na rawa, hakanne ya jawo hankalin sauran suka fahimci abinda ke faruwa. Bilkisu ta cusa kanta cikin cinyoyinta ta sake fashewa da kuka mai tsuma rai. Hakama Anum ƙanƙame Ummu tai ta fashe da kuka tana faɗin, “Ummu shima yayi kamar na Umm-Anum”. Rungumesu Ummu tayi a jikinta daga ita har Bilkisu itama tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta, ‘wannan wane irin tashin hankaline haka?’. Ta faɗa a ranta cike da tausayin wannan ahali.
A take shima Jawaad aka ɗaukesa zuwa ɗakin kusa da Umm-Anum aka shiga bashi taimakon gaggawa domin ceto numfashinsa.
★★★★★★