← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 168

Sashe 53

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

           Bayan sallar la'asar su Uncle Nasir suka wuce gida harda Dad da Qaseem da aka tilastama dole akan yadace suje su watsa ruwa kodan suji ƙarfin jikinsu, anbar momy kawai wajen Shahudah, Ummie da maman Amina kuma suna tare da Bilkisu, Jawaad bai shiga duba kowaba a cikinsu.
      Suna isa gida ya shige sashensa, wanka yay yasha magani saboda kansa ciwo yake masa sosai, duk yanda yaso ya kwanta ya huta hakan ya gagara, ya shiga zagaye bedroom ɗinsa cikin faɗawa wani dogon tunani akan wannan dambarwar da suka wayi gari da ita yau, tabbas yasan kaso mafi yawa na abinda ya faru, musamman akan sarƙaƙiyar ɗaurin auren, sai dai akwai wani al'amarin daya ɗaure masa kai sam ya kasa samun amsa akai, kuma yazama dole ya nemo wannan amsar, Tabbas saiya nemota, itace zata zama tsanin buɗe masa hanyar fahimtar abinda ya kasa fahimta a yanzu da duk sauran jama'a ma. Ya sauke numfashi mai zafi tare da kwanciya a kan gadonsa ƙafafunsa a ƙasa.
        Shi da kansa shine ya canja list ɗin ɗaurin aure a masallaci, sai dai daliline mai ƙarfi ya sakashi aikata hakan, kuma duk wanda zaiji dalilinsa anan gaba zai tabbatar abinda yayi shine dai-dai kuma shine ya dace, to amma tayaya zai fahimtar da mutane sukuma su fahimta batare da ya fito da ainahin maganar filiba?. Wannan tambayar itace keta cin ransa da sukarsa a ƙahon zuciya. Barci ɓarawo shine ya sacesa a wannan lokacin batare daya shiryama hakanba, bai farkaba sai gab da magriba, wasu massallatanma har sun fara kiran sallar. Wanka yay a gaggauce yay shiri cikin ƙanan kaya ya fita riƙe da key ɗin mota da wayoyonsa, mota ya buɗe ya zubasu sannan ya nufi massallacin ƙofar gidansu sukai sallar magriba.
           Koda ya dawo bayan an idar mota ya shiga ya fice daga gidan.

★★★

MASARAUTAR GAGARA BADAU

              Koda su Amaturrahman suka iso masarauta sai suka iske gimbiya Munaya tana sashen mai martaba, haƙura sukai akan idan ta fito saisu sanar mata da duk abinda ke faruwa.  Safah dai batace komaiba, tana ganin yayun nata sun nufi ɗakinsu ta zare jiki zuwa sashen mai-martaban batare da sun saniba. Sai dai koda ta nema Jakadiya tai mata iso saitace mata gimbiya na tare da takawa, tasan kuma babu mai shiga ganinsa inhar yana tare da matansa. Tarbiyyar da su Safah suka tashi ciki akwai girmama hadiman gidan, dan koda wasa Gimbiya Munaya bata yarda yaranta suce zasu taka koda bawa na gidan yanda suke soba, tsaye take kan tarbiyyarsu daga ita har mai martaba da Mommah. Safah sai ta kwantar da kai cike da shagwaɓa tana lallaɓa jakadiya, harda bata ƙyautar dubu biyar. Baki Jakadiya ta washe, tace, “A uwar masu gida ai dolene nai miki iso, ammafa inhar basa falon farko to saidai kiyi haƙuri anjima saiki dawo.
      Safah tace, “Na yarda, amma dai ba falon farko kawai ba, dan ALLAH harna biyu, dan kinsan inhar Ummu na tare da Abbu bazasu zauna a falon farko ba, nikuma maganace mai muhimmanci zanma Ummu”. Rigimar Safah da Jakadiya ta sani yasa ta amince zataje har falo na biyun. Safah na nan tsaye a ƙofar ƙatafaren falon mai-martaba Jakadiya ta shiga domin mata iso. Iyakarta falon farko tai kira ta wayar landline kamar yanda tsarin Sarki Sameer yake. Munaya ce dake masa tausa ta ɗaga, cike da girmamawa Jakadiya ta isar da saƙon Safah. Daga can Munaya zata fara faɗa akan Safah ta jirata saita fito Sarki Sameer yaymata nuni data bari Safah'n tazo, badan tasoba tabi umarninsa.
        Cike da ɗoki Safah ta shiga kamar yanda Jakadiya ta sanar mata anbata izini, tun daga falon farko har zuwa na uku bata iske kowaba, hakan yasata wucewa ƙaramin falon da bakowa keda lasisin shigarsaba saisu da iyayensu. Tai sallama a bakin ƙofa suka amsa mata kafin a bata izinin shiga. Sarki Sameer na kishingiɗe a ƙasan lallausar daddumar da

aka ƙawata falon da ita, ya zubama ɗiyar tasa da bazata gaza shekaru sha uku ba ido yana murmushi, itama murmushi take masa tana satar kallon Ummu dake zuba mata harara ta gefen ido. Ganin tayi tsaye taƙi ƙarasowa garesu mai-martaba yakai dubansa ga gimbiya Munaya, hannu yakai yanda Safah bazata ganiba ya Mintsineta, gimbiya Munaya ta ɓata fuska irin taji zafinnan, gira ɗaya ya ɗaga mata yana murmushi da cewar, “Kin tsaremin yarinya da ido takasa ƙarasowa, Ummuna kinga zo naji mike tafe dake?”. Da sanɗa Safah ta raɓa gefe taje ga mai-martaba daya tashi zaune sosai, hannunta ya kamo ya zaunar da ita kusa dashi. Safah akwai shagwaɓa da ƙulafucin iyaye, gashi tsiwarta data gada ga Munaya yasa Sarki Sameer ke tsananin sonta sosai, danshi idan tana abu Munaya kawai yake gani a zamanin ƙurciya. A jikinsa ta lafe tana kumbura fuska, cikin raɗa tace, “Abbu dan ALLAH kacema Ummu tabar hararata ni tsoron idanunta nakeyi, kumafa abu mai muhimmanci zan faɗa”. Murmushi mai-martaba yayi, ya maida dubansa ga Ummu data tsume fuska. “Ummu Please kiɗan saki fuska mana, kinga dai tsoron idanunki mukeji”. Yanda yay maganar cikin marairaice fuska ya sakata yin murmushi ta ɗauke kanta daga garesu.
      Safah ta gyara zama ganin Ummu tabar harararta tace, “Abbu kasan miya faru a inda mukaje kuwa?”. “Saikin faɗa Ummuna”. duk abinda suka iske na rikici a gidansu Bilkisu shi Safah ta zauna tsaf ta zayyanema mai-martaba da Ummu, sosai abin ya basu mamaki, sai dai basuce komai akan batunba Ummu tace, “Tunda kin gama faɗa tashi kije idan na fito zanyi magana dasu Amaturrahman”. Sosai Safah ta kumbura harda hawaye, tace, “Abbu kajifa ni bandani za'ayi maganar bayan aunty nace”. Murmushi takawa yay yana mai girgiza kansa, ya shafa kanta yana faɗin, “Ai dolenema ayi magana da magajiyar Ummu, bayan ma kece kika kawo zancen”. Cikin ɗoki tace, “Yauwa Abbunmu shiyyasa nake sonka, bara naje na faɗama Mommah itama”. Kafin wani cikinsu yay magana ta fice da gudunta.
      Ummu tace, “ALLAH dai ya shiryeki Safah, nikam bansan irinkiba”. Murmushi takawa yay tare da ɗora kansa saman cinyarta, yakai hannu ya shafi kumatunta yana mai lumshe idanu, “Dukfa rawan kan Safah a wajenki ta gada, kinsan kawai dai shi ɗan gado idan ya gaji abu saiya zarta mai shine”. Murmushi gimbiya Munaya tayi itama tana shafa kansa, tace, “Kaikuma gashi baka mantuwa yallaɓai”. Sosai ya buɗe idanunsa a kanta yana mata wani sassanyan kallo, cije lips ɗinsa da yay tare dayin ƙasa-ƙasa da murya kamar mai tsoron ajisu yace, “Yallaɓiya ai Sameer bai cancanci mantawa da ƙuruciyarki ba, kin bani wahalafa da yawa madam”. “Kamar yanda nima ka baniba”. Dariya sukayi a tare. Saida suka tsagaita takawa ya tashi zaune sosai idanunsa akan gimbiyar tashi. Yace, “Ban fahimci zancen Safah ba, mike faruwane?”. Cikin nutsuwa gimbiya munaya ta zayyane masa komai akan farkon haɗuwar Bilkisu dasu Safah ɗin a wajen Saloon ɗinta, har tafiyarsu yau domin kaimata l'd cards ɗin da Safah ta zama sanadin ɗakkosu. Shiru baice komaiba tsahon wasu mintuna, itama Ummu bata sake cewa komaiba. Harma ta sakin zancen sai y jeho mata tambaya akai “Toke yanzu mi kika fahimta a zancen nata kenan?”. “Eh to inason nasamu ƙarin bayani wajensu Amaturrahman ne, daga nan sainaga idan maganar nada muhimmancin da zamu shiga ciki, dan na lura a zancen Safah kamar ita yarinyar ba ƴar gidan bace”. Kansa ya jinjina mata kawai, daga nan suka saki zancen suka cigaba da hirarsu.

_________________________________

                Kai tsaye asibiti Jawaad ya nufa, Ummie ta wuce gida tun ɗazun bayan zuwansu Batool da Jawaad ya kira Ummah babba ɗazun yace taje asibiti ta kwana a can wajen Bilkisun, babu musu batool ta amsa sukazo tare dasu Ummah suka duba Shahudah da bilkisu, su su Ummah sai suka koma gida akabar batool din anan, da Nabeelah ma ta tubure nan zata kwana tana ta hawaye ganin halin da Bilkisu ke ciki, harda rantsuwar saita rama mata, saida ummah ta lallabata saboda sunyi yawa, kuma Jawaad tunda ba ita yaceba idan yazo ya sameta tasan kaniyarta zaici ne..
      Batool na zaune suna ɗan hira itada maman Amina aka

n abinda ya faru yay knocking ƙofar, a zatonsu Doctor ne ya dawo. Ganin Jawaad ya saka Batool mamaki, dan cayayma Umma sai da safe zai dawo daga inda yaje, zatai magana yay saurin saka yatsansa saman baki alamar tai shiru, shirun kuwa tayi. Ya gaida Maman Amina cikin girmamawa dan dama sunsan juna tun lokacin da take aiki gidansu Shahudah kafin ta barma Amina saboda matsalar ciwon ƙafa data isheta.  Takawa yay zuwa gaban gadon da Bilkisu ke kwance dama tunda ya shigo idanunsa a kanta yake, baya ganin fuskarta saboda ta juyama ƙofar baya. Cikin dabara maman Amina ta fita daga ɗakin.
         Ta inda bily ta juya fuska Jay ya zagaya, tsaye kawai yay ya zuba mata manyan idanunsa da sukai jazur da ɓacin rai, tsawon mintuna uku kafin ya kalli Batool dake tsaye itama tana kallon bilyn. Cikin ɗacin murya yace, “Waye yay mata wannan dukan?”. Itama Batool muryarta da alamun baƙin ciki ta bashi amsa da cewar, “Su Aamilah ne akace, inason dan ALLAH kaci uban yarannan Brother, saboda wannan abin da sukai tsabar cin zaline ai da hauka, yaran gidannan naku sam tarbiyya bata ishesuba na lura, mtsoww!”.
    Baice da Batool komaiba, sai dai yanda fuskarsa ta ƙara tsukewa zakasan lallai ran ƴan maza sun ɓaci, tsahonsa ya rage tare da ranƙwafowa akan bily da duk batasan anaiba, yakai hannun damarsa a hankali gefen kumatunta da yafi ko ina kumbura, motsawa tai tare da yatsine fuska alamar taji zafin taɓawar da yay ɗin, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana mai janye hannunnasa. Tsaye ya miƙe idonsa har yanzu akan Bilkisun yace, “Mi Doctor yace yanzun?”. “Sunyi magana da Ummah, bansan miyace mataba gaskiya”. Bai sake cewa komaiba ya cigaba da kallon Bilkisu na tsahon lokaci, kafin ya sauke numfashi da zare hannunsa ɗaya daga aljihun wandonsa ya ɗauki file ɗin daya gani a drawer gefen gadon, saida yagama dube-dubensa sannan ya ajiye yay ficewarsa batare da yacema Batool komaiba. Itama da kallo kawai ta bisa, haka kawai yau takejin matsanancin tausayin ɗan uwan nata da ya kasance shi ɗaya tilo, babu wa babu ƙani, babu iyaye baki ɗaya sai dangi.
Chapter 53 · 0% Book details