← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 168

Sashe 75

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Cikin ɗaurewar kai Jawaad yace, “Amma miyasa kanema sanin sunan mahaifinta?”. “Saboda duhun dana gani biye da bayanta yafi naka rintsi”. “Duhu kuma baba?”. “Ƙwarai duhu ɗana, amma da sannu zai yaye insha ALLAHU bisa rahamar ALLAH, shawarar dazan baku shine ku dage da addu'a da sadaka musamman a cikin wannan watan mai albarka na Ramadhan da zamu shiga nanda kwanaki uku idan munada rabon kaiwa. Kunika ciyar da bayin ALLAH fiye da yanda kukeyi a baya, ku saka dubunnan marayu farin ciki fiye da yanda kukeyi a baya, ku kaima UBANGIJI kukanku fiye da yanda kukeyi a baya, sannan a daren jiya naga wani haske dake nesa da kai na tunkaroka, sai dai yana nesa dakaine, bansan tayaya zakaje garesaba koshi yazo gareka”. Da sauri Jay ya kalli baba ƙaura, “Baba ko hakan nada nasaba da mafarkin da nake mai sarƙaƙiya?”. “ALLAH kaɗai yasan gaibu Jawaad, amma tun yaushe ka fara mafarkin?”. Jimmm Jay yay alamar tunanin, yace, “Baba idan har ban mantaba na farayinsa a daren da muka dawo daga wata horaswa daga ƙasar America ne, shekara kusa ɗaya kenan, sai da danayi sau ɗaya ban sakeba sai a watanan nan naketa maimaitawa, bayan ɗaurin aurena da ita sai kuma ya canja salo”. “Ikon ALLAH,to shidai mafarki sirrine yaro, sannan akwai abinda yake ishara daga UBANGIJI a cikinsa, akwai wanda shaiɗanu ke jinginuwa a cikinsa, akwai wanda keda alaƙa da saka abu a rai, to amma kozan iya jin wani abu daga mafarkinka?”. Babu musu Jay ya faɗa masa na farko da wanda yay a ƙarshe washe garin ɗaurin aurensa da Bilkisu bayan sallar la'asar. Baba ƙaura ya daɗe baice komaiba, yanata juya abun a ransa amma bai samu wani hasken da yake buƙataba, ya ɗago ido ya zubama Jay na tsahon lokaci kafin ya janye, “Alƙar jini a cikin jini yanada nasaba da kamar kun haɗa jini kenan nidai a nawa ɗan sanin da UBANGIJI ya banifa, amma sanin gaibu sai ALLAH”. Sam Jawaad bai fahimci komai daga kalaman baba ƙauraba, dan a iya saninsa babu ta inda yakeda dangantaka da Bilkisu sai ta wajen su Hudah..... Baba ƙaura ya katse masa tunani da cewar, “Sarƙaƙiyar dake ɗaure da rayuwarku tanada nasaba da wani zalincin mai tushe daga wasu jininku, UBANGIJI shikaɗai yasan sirrin dake ɓoye dai, amma a mafarkinka mutum kake gani yana sanar dakai kokuwa?”.
      “Da farko dai bana ganin kowa, amma daga bayan nan mace nake gani, gashi na santa a mafarkin, sai dai dana tashi fuskarta saita ɓacemin, duk iya hasashena bana tunota”.
      “To UBANGIJI shi kaɗai yasan dalilin sirranta maka ita a zahirin taswurar zuciya, kuje kucigaba da addu'a, ALLAH bai manta da al'amarinku ba. Ga wannan gadalin (maganin), karkaji komai sanine daga abinda ALLAH ya sanar dani nima, saboda bibiyarta da ake ana tsoratar da ita dalilin abinda ke hannunta nasu ALLAH bazai basu damaba insha ALLAH, a zubashi a Abu mai tsafta, a karanta Ayatul kursiyyu (itace aya ta 255 a suratul baƙara), suratul Yunus aya ta 79~82, Suratul Ɗaha aya ta 65~70, Suratul Kafirun, Al-Ikhlas, Al-Falaq, An-Nas, a tofa ciki,  A shafe jiki da shi akuma ringa sha safe da yamma, sannan ai turare da wannan. Insha ALLAHU duk wani baƙin aljani da aka haɗata dashi zai gusa, zaku samu haske mai yawa akan al'amarin cikin amincin ALLAH, sihirin dake jikinku zai warware da izinin UBANGIJIN al'arshi.
       Ada Jawaad ya tsani irin waɗanan abubuwan, amma jin baba ƙaura ya ambata harda ayoyin ALLAH saiya amsa yay godiya, sunɗan ƙara tattaunawa yay masa sallama ya tafi.
       Daga Barrack ɗinan tasha ya nufa inda gimba ke hawa motar garinsu idan zaije gida weekend.................✍

😉🤫👍🏻😘.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
        ƊAURIN ƁOYE
      ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
         SAUYIN ƘADDARA
        ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
           BURI ƊAYA
         ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
           KAIMIN HALACCI
           IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
          WUTSIYAR RAƘUMI...
         GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya

500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Ƙwai Cikin Ƙaya
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
Page 33

...............A ɓangaren gidan Dad komai ya ƙara caƙuɗewa, yakasa barin ƙasar koda kuwa zuwa Niger ne, komai Shahudah batayi yanzu banda aikin kuka da kiran Jawaad, ta tabbatar musu indai basu rabata da Habib sun maidata gidan Jawaad ba saita kashe kanta, kullum cikin lallaɓata suke da mata alƙawarin samun Jawaad duk rintsi kuma har ƙarshen rayuwa, zakuma su rabashi da bily koda tsiya dan ita kaɗai ta mallakesa, acewarsu tabari ya gama hayaƙin rashin mutuncinsa yanzun sunada hanyar maganinsa ne.
      Qaseem kan tun bayan barin Jay asibiti da Bilkisu ya shiga wankama Doctor mari akan ya buɗe masa ƙofa, cikin gigitar azaba Doctor ya buɗemasa ƙofar ya fita, koda ya fito sai bai iske su Jawaad ba, cike da mahaukacin gudu ya ɗauka motarsa ya fice daga asibitin. Marukan da yayma Doctor ne yasaka sauran Doctors ɗin asibitin alwashin ɗaukar mataki, atake suka kira police, ko jinin dake fita ta hancin Doctor basu tsaida masaba saida ƴan-sandan sukazo suka gani.
        Qaseem daya fita yana can yana bilayin neman su Jawaad titi-titi bayan yaje gidansu ance Jay baizo nanba, ya nufi gidan Jay na A.Y street ne ƴan-sandan da aka tura kamashi da yawun hukumar lafiya ta ƙasa sukai ram dashi, duk yanda yaso musu taurin kai da nuna musu shiɗin wanene ɗan wanene sunƙi saurarensa. Dan kuwa dai shima Doctor ɗin da ya mara ɗan wani ƙusane a ƙasar, gashi ma'aikaci a asibitin gwamnati, shiyyasa kamun Qaseem ya taho tun daga sama.
       Yau tsahon kwanakin Qaseem biyu kenan a police station batare dasu Dad sunma saniba, su duk tunaninsu Qaseem na gidansa ne tunda fushi yake dasu bazasu ganshi a yanzuba.
          Salman ma dai daƙyar suka lallashesa ya haƙura da batun barin ƙasar, dan yacefa shi lokacin mutuwarsa baiyiba da zai tsaya ɗan-fir'auna ya sakashi cikin jerin waɗanda zai watandarsu kamar kajin salla, da farko Mom masifa ta fara masa, da dai taga babu ci sai ta koma lallaɓashi har Dad ɗinma, da ƙyar ya haƙura akan shifa da yaga wani motsi zai ware abinsa, da wannan ajandar tasa suka yarda, ba komai yasa basason yay nesa dasuba sai sanin halinsa musamman akan shaye-shaye, shiyyasa basason yay nesa dasu, ALLAH dai yasosu abin bai nisaba suka tsaya kansa ya haƙura.
          Momy dake haɗama Dad tea takai dubanta garesa, yay shiru tamkar babushi a d/table ɗin, gaba ɗaya rikicewar da gidan yayi yasa sun fita hayyacinsu daga ita harshi, wani irin jin ƙarin tsanar Bilkisu tai a ranta, dan kuwa a ganinta duk itace sanadin komai, shigowarta rayuwarsu ne ya tarwatsa musu gida, da Dad bai jajubo musu itaba da yanzu suna zaune cikin kwanciyar hankalinsu, siririn tsaki taja tana mai dangwarar masa da kofin tea ɗin gabansa. Kallonta yay da mamaki, yace, “Lafiya kike tsaki? Bayan kinsan abinda nafi tsana kenan a rayuwata?”.
          Momy ta kuma jan wani tsakin tana cigaba da zuba masa farfesun bindin sa ɗin da takeyi, “Bakai nakema tsakiba nikan Dadynsu, sanadin tarwatsewar gidana na tuna, lokacin da zaka ɗako yarinyarnan dana nuna ɓacin raina fushi kaitayi dani, ka ringa nunamin batada maraba da ƴaƴanmu jininmu a wajenka, gashi kaga sakamakon daya biyo baya ai, ka ɗakkota daga inuwa ita ta turamu rana, ranarma mafi munin zafi da ƙuna, nikam dai wannan zuminci naku ai ALLAH ya tsine mar (Wa'iyazubillah, Mom zuminci ya wuce tsinuwa, dan yana ɗaya daga cikin hanyoyin shiga aljannah🙄).
       Dad yace, “Humm, wlhy kuma kingafa Aysha duk da wannan abun daya faru sai ban daina jinta a rainaba, a ganina yarinyarnan bata da laifi akan rikicinan, daga gidanku aka harɗa komai, kekuma gashi bakison laifin danginki sai nawane sakarkaru ko?!”. Yanda yay maganar da zafi-zafi ya saka Momy kallonsa da mamaki fuska a yatsine tace, “Ikon ALLAH, kaifa nagama sammun yarinyarnan yafi cinka fiye da kowa a gidannan kai da wannan shashashan Qaseem, to wlhy inma ban ɗauki matakin ƙarshe akan yarinyarnanba kuce ba sunana Aysha Humaira ba Mtsowww!!” ta ƙare maganar da buge table ɗin ta tashi tabar wajen.
    Duk wannan abu dake faruwafa tsakanin Dad da Mom Shahudah da Aamilah na zaune a D/table ɗin suma, Aamilah dai earpiece ne a kunnenta tanajin waƙa, shiyyas

a batasan mi tsoffin nata je tattaunawa ba, Shahudah kam cikin damuwa take mai gusar da hankali, zuciyarta gaba ɗaya tana ga Jawaad da tunanin ina Bilkisu?, dan a yanzu dai wannan matsalar tafi cin zuciyarta fiye da komai, ɗan-fir'auna tasan ko kotune Dad sai ya kaisa ya saketa, inmafa bai saketanba ita ahaka zatai aurenta tunda ai bada soyayya tsakaninsu aka ɗauraba, a ganinta tunda babu soyayya ai auren bai ɗauruba kenan (Hudah Kai a tukunya😖😂 lol).
      Buga table ɗin da Mom tayine ya maido hankalinsu kansu, duk suka bita da kallo kafin su kalli Dad da shima kallon Momyn nasu yake rai a matuƙar ɓace.
         Aamilah dai baki ta taɓe ta cigaba da sauraren waƙarta dacin abinci, Shahudah ce dai ta kalli Dad ɗin bayan ɓacewar Mom a idanunsu. “Dad wai faɗa kukeyi ne?”. Huda tai maganar tana mai tsatstsare Dad da manyan idanunta da suka koma ƙanana a yanzun saboda tsabar yawan kuka. Kansa ya girgiza mata yaja bowl ɗin data saka masa farfesun ya fara shan romon kawai dan kauda hankalin Shahudah daga abinda take zargin.

_______________________________
Chapter 75 · 0% Book details