← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 168

Sashe 28

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      A ɗakin Shahudah kam bayan fitowar Bilkisu Aamilah ce ta sauke ajiyar zuciya tana mai fuskantar ƴar uwar tata da ƙyau. “Sister ga shawara mana” Shahudah da duk tazama kalar tausayi ta jinjina mata kai alamar tana saurarenta. Aamilah ta sake jan numfashi kafin tace, “Ina ganin yarinyar nan Bilkisu zamu iya sakata tai mana wani abu” murya a dasashe Shahudah tace, “Ban ganeba Aamilah ”. “Sister ina magana ne akan Brother Jawaad, da nayi tunanin Broth ne a farko, sai dai daga baya nasan bamai yuwuwa bane, musamman idan mukai dubi da yanda basama shiri tun suna yara, sam jinin Qaseem da Jawaad bai haɗuba, bankuma san lokacin dazai haɗunba, so idan mukace zamu ɗorasa akan ya taimaka mana sai dai ya ɓata komai tunda dama can bason aurenku yakeba, yanzu da yarinyar nan ta shigo, sai naga mizai hana mu amfanu da ita, dan kinsan bata da yawan hayaniya da surutu, sannan mutumin dake da irinki bazai kalletaba da sigar birgewa balle akai ga so, ballantana zuciyarmu tayi tunanin ko zata iya cin amanarmu, ko shi yaji wani abu a kanta”. Shahudah datai shiru tana kallon Aamilah tace, “Maganganunki kawai naji Aamilah, amma ban gane ina suka dosaba sam, wane taimko zamu nema akan Bb?”. “Yauwa, yanzu kikai tambaya mai ƙyau Sisi na, inaji a raina Yarinyar zata taimakemu, sai dai bani da tabbacin wajen aikinsu ɗaya, duk da dai naga kullum tare take fita da Broth, ku

ma Broth da Brother Jawaad wajen aikinsu ɗaya ne, amma wannan ba wani abu bane, zamu iya tambayarta”. Kai kawai Shahudah ta jinjina alamar gamsuwa, Aamilah tace, “ki kwanta ki huta zamu tattauna zuwa da safe, tunda weekend ne tana gida babu inda take zuwa”. Nanma da kai Shahudah ta amsa mata..

★★★★★

       Washe gari da safe na tashi nai ƴan ayyukan dazan iya harda kayana da sukai datti, na gyara ɗakina tsaf nai wanka sannan na fito, babu kowa falon dan har lokacin ma bana tunanin wani ya tashi a jama'ar gidan, kicin na nufa na samawa cikina abinci naci, kafin na sake komawa ɗaki na shiga neman Number dad da ya kirani kwanaki uku da suka shige, kusan duk Numbers nashi na ƙetare inada ita, dan yakan kirani lokaci-lokaci idan yay tafiya tamkar yanda yakema sauran ƴaƴansa, bata shigaba, na sake gwadawa har sau uku saina haƙura, bazan iya zuwa ko inaba bayan wajen aiki saida umarninsa, dan banida wani jagora sama da shi a halin yanzu a duniya, sai ko yaya Qaseem da nake fatan ya zama na biyu a matsayin miji. Na aje maganar zuwa gidan Inna zainabu akan sai idan ALLAH ya kaimu gobe, idan naje inda boss yace na gama abinda nakeyi sai na shiga wajen wanke kai daga nan na wuce can koda ban jimaba sai na gaishesu na taho gida, da wannan tunanin na miƙe da nufin zuwa gidansu Amina.
              Harna fice babu motsin kowa, muka gaisa da baba mai-gadi na fice abina. Da sallama na shiga gidan, Amina dake a tsakar gida tana wanke-wanke ta amsa tana kumbura fuska, dariya nayi ganin yanda tayi, dan nasan dalili, ta ɗauke kanta da faɗin, “Munyi fushi, ki koma a binki”. Kafin nace wani abu mama tace, “Kwarai kuwa Amina ina bayanki”. Kunnuwana na kama duka biyu na kneeling  alamar dai na tuba, dariya suka sanya daga mama har Amina da yayan Amina daya fito da ga bayi, shine yace, “A ni dai na yafe ma ƴar ƙanuwata, nasan aikine ke mata yawa”. Nace, “Yauwa Yayanmu, shiyyasa nake yayinka a koda yaushe”. yay dariya da haɗe yatsun sa babba da manuniya alamar dai-dai👌🏼 kenan.
      “Oh, mu baƙya yayinmu kenan? To kin ƙarama kanki laifi har tsallon ƙwaɗo sai kinyi” Amina ta faɗa tana miƙewa ɗauke da kwandon data saka kwanikan. Mama tace, “A'a auta nimafa na huce, ama mai-gadon lu'u-lu'u haƙuri”. Dariya muka saka gaba ɗayanmu saboda furicin mama, Amina tace, “Shikenan na haƙura tunda mama ta saka baki, amma da yau ɗinan saina tsamar da ƙafafunki”.  Harararta nai kafin na zauna a inda ta tashi na gaida Mama da Yaya Sule, daga nan muka hau hirarmu.

        Wajen sha biyu Amina na tayani tsifar kai muna hira, mama kuma nata ƙoƙarin ɗaura awara da muka tace da Amina bayan munje munkai markaɗe, nace, “Amina!”.
       “Na'am” ta amsamin tana leƙo fuskata. Ɗalli namata a fuska da ɗan yatsa, ta matsar da fuskarta tana ɓata fiska saboda zafi, niko na kwashe da dariya, “Ke ɗince kin wani kawomin fuska saikace maison leƙa ramin gwal”. Dariya itama tayi tana ranƙwashina a kai, “Ai bazakici bulusba kuwa”. “ALLAH da zafi” na faɗa ina harararta” tace, “Nima ai naji zafin shiyyasa na rama”. “Ba komai zaki gane shayi ruwane. Maganarnance dai zamu sake”. Shiru tayi kamar bazatace komaiba, tsifar da takemin ma ta koma min ita a hankali, na zungureta da hannu dan nasan ta faɗa kogin tunanin nata. Numfashi ta kawo a hankali, tace, ”Ina saurarenki”.
          “Amina, a zaman da kikai gidanmu na tsahon wasu shekaru, nasan zakisan halayyar kowa dake cikin gidan nan”. Tace, “Hakane” “Alhmdllh, mizan iya sani akan Qaseem da Salman?”. Shiru tai na wasu sakanni kafin ta sauke numfashi, “Duk abinda kikeson sani zan iya faɗa miki Bilkisu inhar na sanshi, wanda kuma ban sanshiba zance miki ban saniba, kimin tambaya zanfi fahimtar mikike son sani game dasu?”.
      Cike da gamsuwar maganarta nace, “Hakane, Qaseem da Salman suna neman mata?”................✍

Asha weekend lafiya🤫🤭😉😍👌🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

Yau ƴan wattpad sai haƙuri yaƙiyi wlhy, da ƙyarma nai copy ɗin wannan a can ɗin,
amma zan cigaba da gwada muga in za'a dace😔
[12/31/2020, 9:31 PM] Abubakar Saleh Kurami: Bilyn Abdull 📚:
Page 13

.................Shiru tai na wasu mintuna kafin tace, “Ban taɓa ganinsu da idanunaba a gado ɗaya da mace, amma tabbas Salman yakansha zuwa da ƴammata gidan idan kamar basa nan, ko kuma suna barcinsu na ƙaddara, dan akwai lokacin farkon dawowarsu da yataɓa zuwa da wata yarinyar ƙabila suka kwana a gidan, da safe ta fito zata tafi ALLAH ya haɗasu da Alhaji a bazata, koda ya tambayeta daga ina? Saita faɗa masa Salman ne ya kawota, wlhy a lokacin nazata Alhaji zaiyi kiran Salman yaymasa tatas a gaban yarinyar, ya kuma gargaɗesa sake kawo wata sai kawai naga ya sallami yarinyar ta tafi, shikuma ya shiga mota abinsa ya fita rai a ɓace, dan ko driver hanawa yay ya tuƙasa da kansa yaja mota ranar. Bilkisu bansan miyasa Alhaji keda sakaci wajen tsawatarma yaransa akan abinda ba daidaiba, ya gwammaci ya shanye ɓacin ran a ransa komin zafin da abun yay masa da kuma illarsa garesu da yazauna ya nuna musu kuskurensu, gaskiya ban taɓa ganin wanda yayma boko da rayuwar yahudu ƙazamin ruƙo irin Uncle ɗinkiba, sai dai ina tausaya masa, dan banyi tunanin waɗannan ƴaƴan nasa zasu masa addu'a ba a lokacin da ƙasa ta rufe idanunsa, sai dai dayake UBANGIJI gafurunne kuma rahimun ba'a shigar masa al'amari, ikonsane ya canjasu kosu ƙare rayuwarsu a haguggunce kamar yanda suka tashi. Qaseem kam dai bazance na taɓa ganin ya kawo mace gidan nanba, sai dai nakanji yana waya, dan kusan sau uku ko biyu inajin yana waya da ambatar sunan hotel, ba sunan hotel daya shigo ciki bane kawai yasa nai tunanin hakan, sunan mata dakan shigo a zancen nasa da salon yanda yake wayarne kawai dai ya ɗarsa mani haka. Sai kuma faɗa da naji wataran Hajiya na masa akan batun aure, take cewa ya zauna yanata shashanci a waje sai ya gama tsufa baiyi aureba, idan soyake wata ta haifa mata jika a waje sai ya bada himma. Kinga a zancenta yana nuna kenan yana yin abinda bai daceba ta kamashi ko aka kawo mata labari. Sai dai shima babu tabbas, tunda ba ido da ido nidai na gansaba. Abu na biyu kuma Qaseem baya shaye-shaye, baida wulaƙanci tamkar Hajiya, dan baya shiga huruminka sai idan kaine ka saka kanka a ciki ko wani dalili ya haɗaku, da wahala kiga yana hantarar masu aiki sai idan sun ƙuresa gaskiya, shiyyasa lokacin da kikazo gidan naga yanata biyema su Hajiya akan abinda suke miki nata mamaki, dan nasan ba halinsa bane, sai daga baya na fahimci soyayyace yake miki batare da shima ya saniba, shiyyasa baya iya yin shiru akan al'amarinki. Salman yana shaye-shaye, dan ɗakinsa ma zaki gansu zube baya shakka balle shayin kowa, sannan ɗan wulaƙancine dason yanƙwana mutum, sai dai shi kuma akwai ƙyauta, dan bashi da rowa, akwai kuma tausayi idan ƴan mutuncin na kansa bai cake ba, dan wani rashin mutuncin nasa abinda yake sha ne ke azashi bisa hanyar aikatawa. Haka rayuwa take, duk inda kika samu mutum da mugun hali zaki samesa da ƙyaƙyƙyawa kuma”.
      “Hakane kam Amina” na faɗa ina sake juya maganganunta a cikin raina.

         Tunda na dawo gida maganganun Amina ne kawai keta kai kawo a raina, na idar da sallar la'asar ina cikin naɗe abin sallar Aunty Shahudah ta shigo, sosai nayi mamakin ganinta harma fuskata ta kasa ɓoyewa, dan tunda aka bani ɗakinta bata sake shigowaba, hasalima a wancan lokacin catai ƙyanƙyami kayan ciki take tunda na taɓasu.
      Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo sannan ta zauna a bakin gado, fuskarta wasai babu alamin turɓune wa kamar yanda takeyi da, sannan babu kallon banza balle hantara.
        “Oh, sai kallona kike tamkar kin samu tv Bilkisu”. Murmushin da ban shiryaba nayi, dan inaga yaune karan farko dana fara jin sunana a bakinta, nace, “Aunty Shahudah ai mamakin shigowarki nan nake, nasan dai.....” sai kuma nai shiru ban ƙarisa ba. Batace komaiba sai gefenta data nunamin da hannu alamar na zauna. Nima ban musaba na zauna ɗin inata ƙara mamakinta dai. Cikin katsemin tunani tace,
      “Bilkisu aiki nazo kimin, konawa kike buƙata zan biyaki”. Kallonta nai da mamaki, sai kuma na girgiza kaina, “Aunty Shahudah ni yanzu dan zaki sakani abu har sai kin biyani? Bana buƙatar ki dinga kallon haka tsakanina dake, ki sakani kominene kike da buƙ
Chapter 28 · 0% Book details