← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 168

Sashe 94

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Koda Jawaad ya fito sai ya iske baƙonsa cikin rumfar bunun dake harabar gidan maigadi ya kawosa, ƙarasawa yay yana faɗin, “Ai bammayi tunanin kai bane Munkaila”. Baƙo mai suna Munkaila daya miƙe domin girmamawa ga Jay yay murmushi, “Nine wlhy Oga barka da fitowa”. “Yauwa sannunka da zuwa” Jay ya faɗa yana zama tare da masa nuni daya zauna shima. Cikin girmamawa Munkaila ya gaishe da Jay kasancewarsa ogansa, file ɗin gabansa ya miƙa masa yana faɗin, “Oga dukkan abinda kake buƙata gashi, harma da abinda bakaceba dukna haɗo maka”. Kai Jay ya jinjina masa da faɗi, “Sannu da ƙoƙari” yana buɗe file ɗin. Da hotuna ya fara cin karo waɗanda sukai masifar ɗaure kansa dan harda Alhaji baba tare da mata biyu wadda ɗaya a ciki takasance kakarsace mahaifiyar su Ummah da shima a hoto ya santa, kallon Munkaila yay kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida file ɗin ya rufe.
Munkaila yace, “Oga akwai matsala ne?”. Kai Jay ya girgiza masa, “Babu matsalan komai, yaya maganar wancan aikin?”. “Shima ina gab da kammalawa oga, saboda naga ka matsu da wannan ma shiyyasa na dakata da wancan”. “Shikenan kayi ƙoƙari shima ka haɗamin shi a satin nan, ga wannan ka saka mai nima nayi aljihun nawa yay ƙasa”. Godiya Munkaila yayi sosai sannan suka fito a rumfar. Jay ya shiga mota shikuma ya fice dan mashin ɗinsa na daga waje bai shigo da shiba.
★★★★★
Fitar jawad babu jimawa su Ummie suka isa gidan amarya Bilkisu, Ummie, Zuhrah, Rebecca, Nazifa. Duk da jiya suka rabu da juna tuni suka haukace da ihun murnar ganin juna, suka saka bily tsakkiya da tsokana kala-kala, tun tana musu shiru dai harta koma ramawa itama dan taga shirun nata bazai sa su barta ba.
_________________________
Asibiti yay niyyar fara zuwa saboda Uncle Sulaiman daya tilasta masa yaje, to amma wannan bayanan da Munkaila ya kawo masa yanzun sun ruguza komai, burinsa kawai ya dangane da gidan Alhaji Babba. A waje yay fakin motarsa ya shiga shi kaɗai, Alhaji babba na zaune a falo hannunsa riƙe da Jarida Jay ya shiga da sallama. Ɗagowa yay yana kallonsa fuska ɗauke da murmushi, cikin tsokana yace, “A lallai wannan angon da gaske bahausa ya aura, ashe ba gidan jiya ya komaba”. Jay dake murmushi ya girgiza kai kawai yana zama, “Wannan itace tarbar da zakamin ma na baro matata na taho ganinka da farar safiyar nan”. Alhaji babba yay dariya irin tasu ta manya yana faɗin, “Ja'iri kenan bakifa ya buɗe”. Gaidashi Jay yayi yana murmushin tsokanar da kakan nasa ke masa. Sai da suka kammala gaisuwar da tambayar lafiyar juna da amarya Bilkisu kafin jay ya buɗe file ɗin da Munkaila ya kawo masa, hotunan ciki ya fiddo gaba ɗaya ya miƙama Alhaji Babba shi kuma ya maida hankali ga duba bayanan cikin file ɗin.
“Sa'adatu! kuma?”. Alhaji babba ya faɗa da alamun bazata. Kallonsa Jay yayi amma baice komaiba. Alhaji babba yace, “Jawaad kana nufin matarka nada alaƙa da wannan ta hoton?”. Zama Jawaad ya gyara sosai yana maida dukkan hankalinsa ga kakan nasa, “Baba abinda bincike ya nuna min kenan, sai dai nima kaina a kulle yake musamman da ganin hotonka a tsakkiyar mata biyu bayan mata ɗaya nasan kanada ita kafin Mama Maryam”. Shiru Alhaji babba yay na wasu mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya, yace, “minene sunan mahaifin nata?”. “Adam makaho” Jay ya bashi amsa a taƙaice. Nanma shiru Alhaji babba yay na wani ɗan lokaci yanata faman jinjina kai da murmushi a fuskarsa kafin yace, “Abin akwai ɗaure kai da ban al'ajabi”. Jawaad yace, “Miyasa zai ɗaure maka kai bayan na fahimci kasan wani abu”. Murmushi Alhaji babba yayi mai ciwo da sake maida hankalinsa ga hotunan guda biyar, ɗaya shine da mata biyu a jiki sai jaririn yaro da alamu suka nuna ranar sunansa aka ɗauki hoton ma ƙila, ɗaya kuma matane da miji matar gurguwa sai mijin da alamu suka nuna makaho ne, sai hoto na uku jaririyace nannaɗe cikin farin showal da gani kaga sabuwar haihuwa, hoto na huɗu, mata da minjin nan ne da jaririyar, na ƙarshema dai mata da mijinne sai bilkisu a tsakkiyarsu da bazata wuce shekaru goma sha biyarba. Ya ajiye hotunan yana kallon Jawaad da ƙyau. “Akwai abinda ku baku saniba Jawaad, mahaifiyarka cema kawai zata iya sanin wani abu itama ba duka ba dan a labari ta sani. Ba Amina da Maryam kawai na taɓa aureba, na taɓa auren wata matar mai suna Sa'adatu. Kafin aurena da Amina Sa'adatu itace yarinyar da naso aura dan itace muke soyayya amma iyayena suka ƙi, bakomai ne ya sakasu ƙinba sai kasancewar Sa'adatu batajin magana, duk da yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyarba a lokacin mutane kan jefeta da kalmar ƙarancin tarbiyya, Sa'adatu ta tashi a gidansu bata da uwa a hannun kakarta ta tashi, hakan yasa ta tashi sangartacciya da batajin ƙwaɓa, a dalilin ɗan karatun da aka sakata na boko wanda a wancan lokacin iyakamu maza kawai keyinsa yasa idanunta buɗewa dan ita kaɗaice mace a cikinmu, Sa'adatu ji take tafi kowa a ƴammatan yankinmu dama gata ƴar gata kuma babanta shine maigari, ALLAH ya jarabceni da sonta fiye da yanda kake tunani har takai naima iyayena maganar aurenta. Amma sai mahaiyata tace sam batasan wannan zanceba tama rigada tamin mata Amina, na ɗaga hankalina matuƙa a lokacin amma dole na haƙura muka rabu da Sa'a ina kuka tanayi. Hakan ya zafi kakarta har tayi alwashin sai nayi nadamar yaudarar jikarta da nayi. Babu wanda ya ɗauki alwashinta wani abu aka ɗauramin aure da Amina ta tare. Banason Amina amma ita tana sona kuma mace ce mai haƙuri da kawaici, a zamanmu tasha wahala kafin na ɗan fara fuskantarta, aurenmu da Amina yakai shekara shida amma bata taɓa ko ɓariba, a wancan lokacin dan mace takai shekara goma ma bata haihuba babu mai damuwa da hakan balle ya zama abin magana shiyyasa nima ban taɓa damuwaba. Zuwa lokacin Sa'a itama tayi aure amma ba a wannan garin namu ba, wani ɗan uwanta mai kuɗi aka aura mata, sai dai kuma hankalinta na kaina dan haka shekararta uku ta kashe auren ta fito da yarinyarta guda safara'u, a lokacinfa na tsaya kai da fata saina auri Sa'a dan sonta na nan daram a raina. Zakasha mamaki idan nace maka Amina itace taita kai kawo ga iyayena har mahaifiyata ta amince na auri Sa'a. A farkon shigowar Sa'a gidana ta kwantar da kanta tanama Amina biyayya kamar gaske, amma tunda muka wayi gari ta samu ciki sai abubuwa suka fara canja salo, raini da wulaƙanci babu wanda take ragewa bataima Amina shi ba a bayan idona, amma a gabana babu abinda ya sauya na ladabin da take mata da. Sam ban fahimci zaman kisan mummuƙen da akeyi a gidana ba dan Amina ko a fuska bata taɓa nunaminba har ALLAH ya sauki Sa'a lafiya ta haifi ɗa namiji wanda yaci sunan kakana Adamu. Bayan haihuwar Adamu ne na fara fuskantar akwai matsala a zaman nasu, dan wataran na shigo a bazata na iske Sa'a nama Amina gorin haihuwa. Ranar nayi tamkar bansan Sa'a ba saboda biji-biji nai mata tare da dogon gargaɗi na saki ɗaya. Kamar Sa'a ta nutsu bayan wani lokaci saita dawo da halinta na rashin arziƙi har ƙawaye take kawowa suna haɗuwa cin zarafin Amina. Cikin amincin ALLAH Sa'a bata yaye Adamu ba saiga Amina da ciki. Munyi murna sosai fiye da zato, ganin Amina itama ta samu cikin da ake mata gori sai Sa'a ta sake sabon salon iskanci, Amina dai bata kulata dan ta bama banza ajiyartane. Cikin ikon ALLAH itama cikinta yakai haihuwa ta haifi mace wadda taci suna Bilkisu (mamanka kenan) dariya Sa'a taitayi alokacin da faɗin ai dai itace a sama tunda namiji gareta, Amina dai bata kulatan, bata yaye Bilkisu ba sai ga wani ciki, Sa'a kuma shiru, hankalin Sa'a ya kuma tashi ainun da wannan ciki na Amina harta sake haihuwa bata barta ta hutaba, a wannan haihuwarma dai mace ta samu itace Wasila (Ummah babba). dukda Sa'a ta nuna bata damuba tunda Amina mace ta sake haihuwa saita kasa daurewa, tashiga ƙananun magana Amina tai mata asiri haihuwarta ta tsaya, tun ina tsawatarwa har al'amari yafi ƙarfina na saki Sa'a saki biyu ya zama uku dan al'amarinta ya isheni. Wannan saki yama dangina daɗi yama nata zafi dan dangina dama babu mai sonta sai ƙalilan a cikinsu. Nayi ƙoƙarin na amshi Adamu amma kakar Sa'a tace ban isaba, duk hanyar data dace nabi suka hanani ɗana, acewarsu kishiya bazata riƙe musu yaroba wataran ta kashesa. Rabuwarmu da Sa'a da shekara guda Amina ta sake haihuwar mace dai again, wadda taci sunan Rahamah (ɗiyar Alhaji babba wadda ta rasu) haihuwar Rahama babu jimawa kakar Sa'a ta rasu, alokacinne na shirya amshe yarona dan banaso ya tashi da kalar tarbiyyar gidansu, sai dai a randa naje nai magana da mahaifinta washe gari aka nema Sa'a aka rasa ta gudu da Adamu. Neman duniya anyi babu wanda yaga Sa'a, munɗauki tsahon lokaci muna nemanta amma babu Sa'a babu labarinta. Har kuma ALLAH yayma Amina rasuwa ta barni da ƴaƴa huɗu duk mata ban sakejin ko labarin Sa'a ba balle yarona, kullum yana a raina, dan harda Maryam mun taɓa yin labarinsa”.
Ajiyar zuciya Jawaad ya sauke yana mai jinjina al'amarin a ransa, yace, “to Amma baba miya nisantaka da danginta harmu bamu taɓa saninsu ba ballema shi labarin Uncle ɗin? Tunda gashi dai alamu sun nuna shi Uncle ɗin ya dawo gida har yay aurema kenan ya haifi Miemaa”.
“Kasan na faɗa maka dama akwai damuwa tun hanani aurenta da akai a farko, sannan koda mukai aure danginta sunajin zafin mahaifiyata dani kaina, badanma sunso Sa'a ta dawo ta aureni ba, bayan guduwarta kuma sai abubuwa suka sake ƙwaɓewa suka ɗaura laifin akan Amina ce tai mata kurciya tabar gari saboda ita ƴaƴanta matane Adamu kuma namijine, dalilin wannan sheɗancin nasu nema yasa nayo nesa dasu na dawo nan dan lokacin garin bai haɗe ya zama babba ba gaba ɗaya kamar yanzun, ahankali abubuwa sukaita canjawa dangi makusanta sunata ƙarewa, shiyyasa kusancin namu ya sake taɓarɓarewa ma baki ɗaya tunda wanda za'aiyi dominsa babu shi tare dasu”.
Kai kawai Jawaad ke iya jinjinawa amma ya kasa magana, Alhaji babba ya katse shirun nasu da faɗin, “Duk da na daɗe banga Adamu ba tun yana yaro amma ƴarsa sai ta ɗakko kamanin Rahamah sosai musamman tana yarinya fiye da nasa kamannin, dan ni randa na farama ganinta a asibiti kamannin Rahamah na gani tattare da ita bana Adamu kawai ba, hikimar UBANGIJI kenan mai tsara yanda yaso a lokacin da yaso, Jawaad yanzu kenan Adamu baya raye?”. Cikin damuwa Jay ya jinjinama Alhaji babba kai, “Ta faɗamin mahaifinta ya rasu bayan rasuwar mamanta kusan shekara bakwai kenan ana cikin na takwas, kuma a yanda bayanai suka nunama kenan anan ɗin ya rasu, to amma abinda yama ɗauremin kai sufa danginsa ma suna nuna tamkar bashi da wata alaƙa da ɗiyar tasane fa, wannanne dalilin daya raunana zumincinsu ya dawo gefe yana rayuwarsa shi da matarsa kawai da yarinyar, kuma ko bayan rasuwarsa abinda yasa sukai watsi da ita kenan sai dai batasaniba ita”.
“Jawaad ban gane basu da alaƙa ba, duk wanda ya kalli matarka aiko yaga jinin Adamu ai”. “Gaskiya ne Baba, a hoton dai kam daka gani kasan jinsa ce, nima inason zuwa da kaina garesu naji miyasa suke nisantashi da abinda alamomi suka nuna nasa ne?”. “Bakai kaɗai zakajeba Jawaad, tare zamuje ai, dan nima ina buƙatar amsoshi da yawa a garesun”. Sun daɗe suna tattaunawa akan batun kafin jay yayma Alhaji babb sallama ya tafi asibiti.
★★★★★★
Tunda ya shiga asibitin sukai masa caa da idanu, shiko ya fuske abinsa fuska a ɗaure ya gaidasu da tambayar jikin Shahudah, kafin ya shiga ya dubata tana barci har yanzun, dan data farka suke sake mata wata allurar barcin tunda taƙi kwantar da hankalinta ta saurari kowa, ta dage sai an kira mata Jay.
fitowa yay daga ɗakin ya dawo wajensu da nufin yimusu sallama ya kama gabansa, amma sai mama Atika ta dubesa cikin gadara fuska babu wasa tace, “Mun gama magana da ƙannen ubanka yau bayan sallar azhar za'a maida aurenka da Sabira, kuma gobe idan ALLAH ya kaimu zata tare koda ba'a sallameta daga asibitin ba”.
Wani lallausan murmushi Jay ya saki da ya bama kowa al'ajab da mamaki, dan ba murmushin sukai tunanin gani daga garesa ba. Ya kalli mama Atika da ƙyau yana tura hannayensa cikin aljihun wandon shaddarsa da gyara tsaiwa yace, “Shi kuma mijinta yaya zakuyi dashi”. Yay maganar da maida kallonsa ga ƙofar shigowa.
Gaba ɗaya suka maida kallonsu ga ƙofar inda ɗan-fir'auna ke tsaye akan ƙafafunsa ya warke sarai sai tabbunan raunikan da yaji waɗanda basu gama bajewa da ƙyauba.............✍
(Kana basu pepe da ginger ɗan bilkisu da Abdul-Aziz mijin bilkisu🤣😂🚴🏼)
Chapter 94 · 0% Book details