← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 168

Sashe 112

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

         Da asuba shine ya tadani, kafinma na sakko a gadon yayi ficewarsa, na rakasa da harara sannan na sakko da ƙyar, wani irin zafi naji ya ratsani a wajen, sai ga hawaye shar, nasa hannuna na share ina jinjina muguntar maza a raina, idan dai haka za'a dingaji to miye abin daɗi anan da har mata suke zuwa suyi iskanci dan ALLAH?. Sai da na shiga ruwan zafi yanzunma sannan nai alwala na fito, naji daɗi sosai yanzun kam harda nutsuwa, ficewa nai daga ɗakin na koma nawa, sai fitilar waya na kunna dan sun ɗauke wutarsu. Ina idar da salla gado na haye nai kwanciyata ko azkar banyiba, banason yazo ya iskeni zaune, barci yaɗan fara fisgata naji ya buɗe ƙofar, ban motsaba balle yasan idanuna biyu, sai da ya maida ya rufe sannan naɗan buɗe kaɗan naga bayanan, ajiyar zuciya na sauke na gyara kwanciya abina.

         Taƙwas saura na farka, na sakko daga saman gadon ina matse fuska saboda ciwon da jikina kemin ta ko ina, bama dole nai ciwon jikiba kodan muguntar da akaimin, wanka nayi na fito nai shiri cikin wando da riga na parkistan da sukaimin ƙyau, nai ƴar kwalliya dai-dai misali sannan nasa turare da yafa ɗan gyalen kamar yanda sukeyi. Fitowa nai dan nema mana breakfast tunda ya roƙi Ummah akan a daina kawo abinci, a bazata na iskesa a babban falo zaune yana aiki. ‘Agogo sarkin aiki’ na faɗa a zuciyata cike da gulma. Ɗagowa yay ya tsatstsareni da mayun idanunsa, hakan yasa nai ƙasa da nawa, saida na rissina ina gaishesa sannan ya ɗauke kansa daga kallona, amsamin yay da tambayata wai ya jiki. “Ni lafiyata lau”. Na faɗa ina ɓata fuska “Haka akeso ai”. ya bani amsa a taƙaice. Miƙewa nai ina satar kallon kofin dake a centre table ɗin alamar coffee ya haɗa da kansa yasha kenan? Bance komaiba na nufi kicin, inaji a jikina kallona yake harna shige.
       Idanunsa ya lumshe da sakin murmushi yana ɗauke kansa daga binta da kallo da yayi, a fili ya furta, “Masu dangi, yauma ki ƙaramin maganarsu kiga yanda zamu kwashe anan gidan sarkin son ƴan uwa”.
             Gyaɗar dana jiƙa da farar shinkafa tun da daddare na wanke, na ɗakko farar kwakwa da dama na fasa na yayyankata itama na haɗesu waje guda da citta ɗanya da kayan ƙamshi dai-dai buƙatata na markaɗesu kasancewar akwai wutar da naita addu'a da fatan su kawo tunda nai sallar asuba, sai da sukai laushi sosai sannan na tace tsaf na ɗauraye tukunya na zuba, ban kunna gas ɗinba tukunna na ɗib

a wake gwangwani biyu da rabi shima nai zaman dakawa aɗan turmina, sai da yaymin yanda nakeso sannan na cire na wanke shima nai markaɗan ƙosai, saida na tabbatar na haɗa komai sannan na kunna gas, ban rufeba tukunyar kunun ba gudun karya taso ya zube saboda gafin gyaɗa, na saka ludayi ina motsawa a hankali har yay zafi ya fara kauri, cikin amincin ALLAH baiyi ƙurnu ba yay ƙyau abinsa sai ƙamshin gyaɗa da kwakwa ke tashi, na sauke tukunyar a ƙasa danya ɗan huce kafin na saka madarar dana dama. Suyar ƙosan na fara wanda dandanan na gama kasancewar bawani yawane da shiba, na zuba madarar a kunun sannan na zuba ma maigadi muma na juye mana namu, saida na gyara komai tsaf sannan na fito da namu a Dining na maigadi ma na fito dashi na ajiye gefe. Baya a falon, dan haka naɗan gyara tunda babu wani datti na azo a gani na saka turaren wuta. Ina kammalawa yana fitowa, yay tsaf cikin ƙananun kaya sai baza ƙamshi yakeyi.
            Baice dani komaiba ya ɗauki abincin maigadi ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin ina a Dining ɗin ina ƙoƙarin haɗa masa nasa, kujera yaja ya zauna idonsa akan hannuna da har yanzu yake raɗam da ƙunshi.
      “Duk a yaushe kikai wannan?” na tsinkayi muryarsa a bazata. Kallonsa nai na janye idanuna, nace, “Yanzun”. “Kinyi ƙoƙari, ALLAH yay miki albarka”. Murmushin daban niyyaba na saki sai naji duk fushin nawa yay ƙasa, a hankali nace, “Nagode”. Shima murmusawa yayi kaɗan da ɗaukar ƙosan yakai bakinsa, ya lumshe idanu da faɗin, “Uhhhmm”. Kallonsa nai dariya na cina, na ɗauki cokali nasa gefensa alamar waiji. “Yarinya ai ba santi nakeba” ya faɗa yana jan kofin kunun dana ajiye masa a gabansa sosai. “Nima ai bance santi kake ba”. “Kin taimaki kanki to”.
         Murmushin na sakeyi ina ƙoƙarin haɗa nawa nima.
     Nayi mamakin yanda yaci sosai, ya ɗauki tissue yana goge bakinsa damin almar komai zamm da hannu👌🏼. “Nagode to” nafaɗa ina murmushi. Zagayowa yay ta bayan kujerar da nake ya ranƙwafo ya sumbaci kumatuna duka biyu sannan yace, “Kin gama mallake Jay da komansa Miemaa”.
          Hannu nakai na shafi fuskarsa ina faɗaɗa murmushina, dan naji yanda ya nuna jin daɗinsa da abincin.
      ya zagayo ta gabana ya nunamin kuncinsa alamar na sumbata. Dukda inajin kunya haka na daure na sumbacesan kamar yanda yake buƙata. Sassanyan numfashi ya sauke da juyamin ɗayan, nanma dai yi nayi ina mamakin rashin kunyarsa. “Jazakhillah bi jannah” ya faɗa yana kamo fuskata cikin tafukan hannayensa, kafin nace wani abu ya manne bakinsa da nawa.
       Yana saki na saka hannu na rufe fuska. yace, “Daga baya kenan. Bara naje Alhaji Babba na jirana zamuje wani waje”.
     Miƙewa nai tsaye nima, “To dan ALLAH ka kira Nabeelah tazo ta tayani zama, ALLAH babu daɗi kaɗaicin”. “Baga wuta ba, kuma nima aiba daɗewa zanyiba”. Cikin marairaicewa nace, “Idan suka ɗauke fa, kumafa ni tsoro nakeji”. “Jami'ar tsaro da tsoro”. Ya faɗa yana jan hancina. Bai jira amsataba ya fice yana faɗin “Aimana addu'a”.
     Da “ALLAH ya tsare” na rakasa inajin duk babu daɗi...................✍

Jiya kam Wattpad yay muku buƙulu, nayi typing tun dare zan baku na nemesa na rasa, wlhy sai sake wannan page ɗin nai cike da haushi, gashi dai sai dai kuyi maneji da shi😥.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/12, 6:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Fatima Mustapha:
Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 47
Chapter 112 · 0% Book details