Sashe 118
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Duk wani masoyin su Momy hankalinsa a tashe yake akan ɗauke Shahudah da ɗan fir'auna yayi, abin ɗaure kai da ban mamaki shine duk yanda ƴan sanda suka bazu nemansa basu samu koda mai kama da shiba, dai-dai da wayarsa an kasa samunta ta kowanne yanayi, dama ita Shahudah tata wayar na nan bai bari ta ɗauka ba, duk kuma inda ake tunanin samun ɗan fir'auna anje babu shi babu abokansa.
Hankalin kowa ya ƙara tashi, Momy kuka take kawai tana zazzagama Dad masifa ta waya akan ya dawo ita tashin hankalin nan yamata yawa, sannan ya saka Qaseem ya taho shima. Shidai lallashinta kawai yakeyi dan shima hankalin nasa aiba a ƙwance yakeba, yana matuƙar ƙaunar Shahudah fiye da zaton mai hasashe, shi da yake nesama dasu ya fisu tashin hankalin. A ranar ya sanarma Qaseem ya shirya ya koma gida zuwa gobe saboda halin da ake ciki. Qaseem dai ya amsa da “to” dan zuwa yanzun bai iyama Dad musu akan komai, duk abinda yace yayi shi yakeyi koda bai masaba. Tun a daren ya fara shirin komawa ƙasarsa ta haihuwa, dan dama hankalinsa bama a kwance yakeba a China'r saboda wata cuta da aketa raɗe raɗin ta ɓillo a wani yanki na ƙasar chain mai suna Corona virus, mutane duk a tsorace suke, daƙyar ya iya danne ransa yaje yayo wata ƴar sayayya da yake buƙata ya dawo hotel ɗin da yake ya kimtsa kayansa, insha ALLAH jirgin farko na gobe dashi zai tashi zuwa ƙasar Dubai cikin birin Abu-dabi, daga nan zai hau jirgin da zai sadashi ƙasarsa.
Ɗan-fir'auna ka sakamu a cakwalkwali😣🙄😏😒😠🚶🏻.
__________________________________
((°•°))((•°•))((°•°))(())(())((°•°))((•°•))((°•°))
__________________________________
Iya ƙofar ɗaki Anum ta tsaya tai min saida safe, kaina kawai na iya ɗaga mata batare da nace komaiba. Ƙofar na tura na shiga da sallama a bakina, falone madaidaici da aka zuba komai cikinsa, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi a ciki. Na sauke kumburarrun idanuna akan boss dake kwance cikin doguwar kujera idanunsa rufe, nai masa kusan kallon mintuna biyu kafin na ƙarasa inda yake, durƙusawa nai gaban kujerar na ɗaura hannuna saman goshinsa, wani irin zafi naji zauu dan haka na rimtse idanu da sauri. Jin ya ɗaura hannunsa saman nawa na buɗe idonuna, hannunma akwai zafi shima, a rufe idanunsa suke har yanzu, “Yayanmu baka da lafiya ne?”. Baice min komaiba sai idanunsa dake jajur ya buɗe yana kallona. Hawaye naj
i sun cikamin idanu, yaɗan lumshe nasa idanun ya sake buɗewa a kaina da girgiza min kansa alamar kar nayi kuka. ban ankaraba naji sun silalo kawai, hannunsa ya ɗaura saman kumatuna ya shiga sharemin batare da yayi magana ba. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya buɗe baki da ƙyar yace, “Kukan ya isa mana, haɗamin ruwa maiɗan zafi nayi wanka kozanji ƙarfin jikina”. Kaina na jinjina masa sannan na yunƙura na miƙe. Ƙofar dana gani a falon ya sakani tunanin itace bedroom, can na nufa kaina tsaye, koda na tura sai naga ƙaramin kicin ne, rufewa nai na nufi ɗayar ƙofar, itakam ina buɗewa nai tozali da bedroom babba. Numfashi naɗan sauke na shiga, ban wani zauna ɓata lokacin kalle-kalleba na shiga bathroom ɗin da shima ya kasance babba, komai tsaf an gyarashi, sai ƙamshin fresheners masu daɗi. Dai-daita ɗumin ruwan nayi yanda zai masa daɗi sannan na tara masa, komawa falon nayi na taimaka masa ya tashi zaune, dan da gaske bayajin ƙarfin jikinsa, amma duk da haka yamin nauyi sosai, haka dai na daure har muka isa bedroom ɗin, taimaka masa nayi ya cire kayan, ya rage daga shi sai singlet da boxer kawai, a haka na sake taimaka masa zuwa bayin. Duk yanda naso na zame na barsa yay wankan shi kaɗai bai yarda ba, yace na taimaka masa jikinsa sam babu wani ƙarfi, gashi yanajin jiri. Dole na daure nai masa yanda yakeso sannan na sake taimaka masa muka fito, har kayan barci an kawo mana dan haka na taimaka masa ya kimtsa yasha shayi da magani ya kwanta, bargo naja masa na rufesa na zauna gefen gadon ina kallonsa, shima dai idanunsa a kaina, bamu jima a hakaba barci ya kwashesa, ajiyar zuciya na sauke a hankali ina share ƙwallar da suka cikamin ido, duk wanda ya aikata al'amarin nan yacika baƙin azzalumi mai busashshiyar zuciya. Nima shayin kawai nasha, na ɗauki abincin na maida sashensu Umm-Anum sannan na dawo na shiga wankan nima. Gasa jikina nai sosai sannan na ɗauro alwala na fito, nima nai shirin barcin na haye gadon na kwanta tare da shigewa jikinsa da har yanzu yake zafi zau. Lumshe idanuna nayi ina sauraren yanda bugun zuciyarsa ke harbawa, a haka nima barci ɓarawa ya saceni.
WASHE GARI
Bayan mun tashi daga barcin da muka koma na safe wanka mukai, muna cikin tunani da zullumin kayan da zamu saka saiga sallamar Anuwar, boss ne ya amsa masa tare da zira jallabiya ya fita falon, babu jimawa sai gashi ya shigo da akwatinmu. Kallonsa nai da alamar tambaya, sai dai baice komaiba ya ɗora akwatin saman gadon tare da buɗewa ya ɗauka kayansa nima ya fiddomin nawa. “Kitashi ki shirya suna jiranmu, su Takawa ma sunzo” yay maganar cikin dasashshiyar muryarsa da tun jiya bata dawo dai-dai ba. Kaina na ɗaga masa na miƙe.
Tsaf muka fito cikin shiga ta kamala munata zabga ƙamshi, mun iske Anum a fallon su Umm-Anum zaune ita kaɗai da alama mu take jira, da girmamawa ta gaida Boss daketa faman kallonta ko ƙyafta ido bayayi. Nima muka gaisa sannan ta sanar mana duk suna falon baƙi mu ake jira.
Duk suna zaune an baje abinci kala-kala a tsakkiyar falon, yanda muka samu Umm-Anum zaune cikin kamala ya sakamu sauke ajiyar zuciyar jin daɗi muka bisu ɗai-ɗai muka gaisar.
Gaba ɗaya hankalin Jay akan Umm--Anum yake, kamar yanda itama nata hankalin na agaresu shi da Bilkisu, sai dai batace komaiba dan an bari sai anci abinci sannan ai zama akan hakan. Lafiyayyen breakfast ne da kowa ya tsinci kansa cikin jin daɗin cinsa, sai dai boss tsakura kawai yakeyi. hakama Umm-Anum bata wani ci sai kallon Jay take.
Bayan an kammala aka gyara wajen tsaf sannan kowa ya nutsu waje guda..............✍😓
wayyo idona wayyo yatsuna😢🚶🏻
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, gu
da biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/18, 10:26 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO