← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 168

Sashe 156

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

weekend ba, amma kuma sai gashi a bazata da yamma liƙis. “Abbamu buguna zatai fa”. “Laifi kamata ai ko?”. Girgiza kai yaron yayi, kafin yayi magana ta matso inda suke ta ɗauka leda viva daya ajiye ƙasa lokacin da zai ɗauki Fharhan. “Sannu da zuwa”. Tafaɗa har yau da mamaki tattare da ita. Murmushi yay mata, yasa ɗayan hannunsa ya shafa kan yarinyar dake goye a bayanta. “Mai gadon zinarina barci akeyi?”. “Ai tunda naimata wanka ta ɓingire, irin wannan zuwan bazata haka”. Murmushi yayi batare da ya bata amsaba ya ida shiga gidan yana faɗin, “Banga na hannun damar Inna ba?”. “Gashi can yana barci”. Ta bashi amsa da nuna masa inda ɗayan yaron ke barci. Sauke Fharhan yay ya kama hannunsa suka nufesa, saida ya shafa kan yaronsa sannan ya zauna gefen tabarmar da aka ɗaura katifar. Itama ledar ta ajiye taje ta kawo masa ruwan sha. Sai da ta ajiye sannan ta sake kallon Fharhan, “Kazo ka kaima su Inna abinci karka bari na sake maimaita maka wlhy Fharhan ”. Baki ya tura zaiyi magana Abbansa ya hararesa, “Kanason na ɓata maka rai ko?” da sauri yaron ya girgiza masa kai, “Ɗauka abincin ka wuce, ka faɗama Inna muma muna nan zuwa gidan”. Da mamaki ta kallesa, sai dai bata iya cewa komaiba har Fharhan ya ɗauka kular abincin su inna ya fice daga gidan.
        “Amma daga dawowarka kake.....” katseta yay da faɗin, “Firdausi babban al'amarine ya kawoni gida, zo kiga abinda na gano”. Babu musu ta nufesa, ya ɗago daga danna wayar da ya keyi ya miƙa mata wayar yana faɗin, “Ko zaki iya gane wannan?”. Da saurinta ta amshi wayar, hoton da taci karo da shi ta tsatstsare da idanu, kusan mintuna uku tana kallonsa cike da nazari ko ƙyaftawa batayi, da sauri ta zabura tana zaro idanu waje da ɗora hannunta saman baki, “Abban Fharhan wlhy kamar Bilkisu fa”. “Kama ko itace?” “Wlhy bana ko tantama Bilkisu ce wannan, ko wane irin canjawa zatayi a rayuwa bazan gaza ganeta ba, dan ALLAH ina ka samo mana Bilkisu? Bayan shekarun da muka ɗauka cikin nemanta babu ko labarinta”. Tai maganar tana zama kusa da shi cike da zumuɗi. “Nima yau na ganta Firdausi, a media naci karo da hoton yana yawo a dalilin abinda ya faru, tana cikin tawagar jami'an tsaron da suka nuna bajinta wajen kamo miyagun mutanen nan yan cultism, kinganta anan tare da mijinta ranar aurensu, shima jami'in tsarone”. “A...ab... Abban Fharhan wai kana nufin Bilkisun ce ta zama jami'ar tsaro kuma tai aure?”. “Wlhy kuwa haka na gani, auren nasu bai wuce wata huɗu ba akace, amma watanta kusan biyu kenan da tarewa, shiyyasa nake faɗa miki ki ringa ɗan shiga yanar gizon nan amma kinƙi, koba komai zaki san abubuwa da yawa da duniya ke ciki, yanzu hakama bakisan abinda ke faruwa a ƙasarba yau ɗin?”. “A'a na sani, dan ɗazun su Luba sunzomin barka kasan sanda na haihu tana Niger, to shine suke labarin, hakan yasa na buɗe redio anan naji komai”. Murmushi yayi ya sake miƙa mata wayarsa dake ɗauke da hoton Bilkisu da Jawaad a ranar dinner ɗinsu lokacin da suke wasan bindiga. Sosai Firdausi ta saku wani ihun farin ciki, ta rungume mijinta tana mai fashewa da kuka, “Wlhy itace Abban Fharhan, ashe zan sake ganin bily a duniyarnan. Abban Fharhan dan ALLAH muje gidan baba, wlhy nasan zaifi kowa farin ciki a yau, bashi da wani buri daya wuce gamo da Bilkisu, wannan shine burinsa, da fatansa a kullum”.
       Babu musu ya amince, ta ɗakko mayafi da kayan da za'a sakama Abbas dake barci, shibe ya amsa ya saka masa, ita kuma ta shiga da kayansa ɗaki ta kulle ƙofar, ta kullo kicin da ɗakin da suke saka kayan abinci da tarkace, ɗaukar Abbas daketa barcinsa yay a kafaɗa suka fice a gidan, saida ta kulle sannan suka ɗauki hanyar gidan Baba a ƙafa da yake babu nisa sosai.

                Sun iske Fharhan nata bama inna labarin abinda akai masa a gidan su musbahu abokinsa kuma maƙwaftansu, tanata lallashinsa ita kuma. Sai dai shigowar su firdausi yasata maida hankali a kansu, Abban Fharhan ya kwantar da Abbas a gefen tabarmar da suke sannan suka zauna suna gaisheta.
       “Wai dama kazo garin Muktar?”. “A'a inna, zuwana kenan”. “To, shine kuma kuka taho nan? Lafiya dai ko?”. “Alhmdllh inna sai alkairi”. “To masha ALLAH,

ai haka akeson ji”.
       Kamar yanda ya nunama firdausi hoto haka ya nunama Inna itama, kwatankwacin ruɗanin da Firdausi ta shiga innama haka ta tsinci kanta a ciki, da sauri ta shiga ƙwalama Baba dake ɗakinsa kira. Fitowa yay da ɗan hanzari dan dama bai jima da shigaba wanka ya fito yake kimtsawa dan dawowarsa kenan daga kasuwar ƙauye da yake zuwa yanzun yana sana'ar kayan miyarsa.
        Shikam ai ganin Bilkisu sai ya rikice fiye da zatoma, musamman dayaga hotunan waɗanda su Bilkisun suka kama, ya share ƙwallar data taru masa a cikin ido yana faɗin, “ALLAH mai iko, ALLAH mai hikima buwayi gagara misali. Muktar kayi haƙuri, dolene zuwa gobe mu koma birni tare da kai kuwa”.
       “Baba har dani dan ALLAH”. Firdausi ta faɗa tana share ƙwalla. Inna tace, “Wlhy nima kam ba'a barina baya, dolene naje ganin ɗiyata”. Itama muryarta da rauni a ciki tai maganar.
     A take babu wani ɓata lokaci suka yanke hukuncin tafiya birni gobe idan ALLAH ya kaimu koda kuwa idan sunje Alhaji lado da Jazuga zasu salwantar da rayuwar tasu kamar yanda suka faɗa musu a baya.

________________________

               Tunda muka baro asibitin saina samu ƴar nutsuwa, dan yanzu banajin aman sam, sai dai kawai rashin ƙwarin jiki da damuwar dake cike taf da ƙirjina harma da ruɗani, ganin duk abinda ya faru nake tamkar a mafarki zan farka zuwa anjima naji ba hakaba.
         Mun yada zango a gidan Alhaji babba, inda muka iskesa zagaye da jami'an tsaro har yanzun, dan ba'a basu izinin barin gidanba. Aliyu na ajiyemu ya juya da cewar zaije ya nemo mana abincin da zamuci.
          Kasancewar magriba tayi ba zama mukayiba, da yake bayan ɗakin Alhaji babba akwai isasun ɗakuna a gidan sai kowa ya samu wajen shiga a wadace, ni dai sakani Ummah ƙarama tayi nai wanka da ruwa mai ɗumi, kamar yanda Anuwar ya taimakama Alhaji babba shima yay wanka dan ya ƙara samun ƙwarin jikinsa.
        Bani da wasu kaya a gidan dan haka na rasa yaya zanyi, saina maida na jikina na fito, salloli ake bina tun daga zuhur har mgriba da akeyi yanzun, gashi kayan jikina bana tunaninma zasuyi salla.
    Ina cikin wannan hasashen Anum ta shigo ɗauke da leda, ajiyewa tai a saman gadon tana murmushi, “Ga kaya yayanmu ya kawo miki”. Kallonta nai da sauri, mamaki sosai a fuskata, “Yazo gidan ne?”. Kanta ta jinjina min, “Yazo yanzun nan shi da abokan nan nasa na wajen bikinku, amma sun fita massallaci, Ummah tace ki saka kiyi salla kizo kici abinci”. Kai kawai na iya jinjina mata, na miƙe nayi duk yanda tace, ina saka kaya ina kallon cikina dake a shafe tamkar babu kayan ciki ma, amma a haka ake maganar akwai ɗan mutum a ciki. Bansan murmushi ya suɓuce minba, na ɗaura hannuna akan cikin naɗan shafa.

              Lokacin dana kammala rama sallolin dake kaina anata kiran sallar isha'i, dan haka na gabatar itama. ban fitaba, na kwanta a saman gadon ƙafafuna a ƙasa fuskata na kallon silin ɗin ɗakin, idanuna a lumshe suke, yayinda hannayena duka buyu ke cikin rigata ina shafa cikina, ni kaɗai nasan mi nakeji a lokacin, ina farin cikin samun ƙaruwar da ALLAH kaɗai ke wadata bayinsa da ita, gefe kuma inajin ɗacin tsintar wanda zuciyata take girmama da daratawa bayan iyayen firdausi fiye da kowa a duniya cikin mummunan hali. Tabbas da ace wanine yazomin da wannan labarin akan Dad bazan taɓa gaskatashiba koda kuwa ace Mijina ne, sai dai kash, nice da idanuna na gansa, da kunnuwana na jisa, ba'a cikin mafarkiba ko magagin barci, ba'a labari daga bakin wani ba. Haɗiye ɗacin daya tokare maƙoshina nayi daƙyar ina buɗe lumsassun idanuna jin ƙamshin turaren dana fi ƙauna fiye da kowanne a duniya a yanzun.
        Jay daya jima da shigowa yana ƙare mata kallo harya gaji ya ƙaraso inda take ya durƙusa a bakin gadon. A hankali ya kwantar da kansa saman cikinta bayan ya janye hanayenta, ya lumshe idanunsa dake cike da nauyin damuwa dana gajiya.
           “Kin bayyana a ranar da tarihi bazai taɓa mantawa da itaba Little Beejay, rana mai cike da ruɗani kala-kala da ban al'ajab, ina roƙon ALLAH ya raya mana ke cikin aminci, ALLAH yasa ki zama hasken idaniyarmu da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W) baki
Chapter 156 · 0% Book details