Sashe 78
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Page 34
...................Katafaren falone daya amsa sunansa falo, komai yaji iyakar ji fiye da tunanin mai hasashe, ga wani sassanyan ƙamshi mai kashe lakkar jiki da tsaida gudun jini na tashi, lallai wannan baiwa ta isa a kirata sarauniya, ta haɗu tama gaji da haɗuwar, ga kwarjini irin wanda kowa yasan masu mulki dashi. Tana kishingiɗe ne amintacciyar baiwarta na gefenta da alama hira sukeyi, dan fuskokinsu dukansu ɗauke suke da murmushi, sai bayi biyu kawai a falon, ɗaya na tausa mata ƙafafu ɗaya na yanka mata tufa a ƙaramin filet. Sallamarmu ta sakata maido fararen idanunta kanmu, da sauri Amaturrahman ta tareni tana faɗin, “Gaskiya Ummu sai kin biya”. Murmushi Gimbiya Munaya tayi mai ƙayatarwa, cikin nutsatstsiyar muryarta tace, “Amaturrahman kin maidani kakarki a gidannan, nakula kema auren kikeso”. Da sauri Amaturrahman ta matsa gefe tana tura baki gaba da faɗin, “Ni ALLAH banason aure ina tare dake da Abbu da Mommah”. Dariya hadiman sukayi, nima dai murmushi nike, dan saita tunomin da Nabeelah. Gimbiya Munaya dake murmushi ta miƙomin hannunta da yasha adon jan lalle, “Kinga ɗiyata manta da wannan zo naji ɗuminki kinji”. Jikina har rawa yake saboda yanda tamin tamkar mahaifiya, na taka a sannu cikin nutsuwa gareta, durƙusawa nai kaina a ƙasa, ina faɗin, “Barka da rana Ummu”. Ina jiyo fitar sautin murmushinta, ta ɗora yatsunta saman haɓata ta ɗago kaina, “Nagode da wannan girmama ɗiyata, ALLAH yay miki albarka kinji, kiyi haƙuri da rashin ganina tun zuwanki”. Murmushi na mata ina ƙasa-ƙasa da idanu, dan bazan iya kallonta kamar yanda take kallona ba, nace, “Babu komai Ummu”. Murmushi ta sake yi, tare da zaunar dani sosai, ta sallami bayinta guda biyu, daga ni sai Amintacciyar baiwarta da kuma Amaturrahman data koma can cikin kujera tana kumbura wai ance za'a mata aure. itafa ta rantse bazatai aure tabar Ummu da Abbu ba. (Kujimin ƴa, to itama munayar ai sunƙumota Galadima yay daga gabansu hajiya innaro😂).
Cikin nutsuwa da hikima Gimbiya Munaya kejan Bilkisu da hira, abin gwanin sha'awa, babu wani nuna ƙyara ko izzar mulkin kasancewarta ƙasan ƙasa da ita, haka gimbiya Munaya take, bata yarda ƙasƙantar da waniba a rayuwarta, tace tasan ciwon ƙasƙanci, bazataso yima waniba, ita tasan wahalar da zuciyarta tasha lokacin da suke ƙarƙashin mulkin mallakar Innaro a gidansu. (hajiya innaronmu ta mutumci kwanciyarki lafiya cikin ƙasa matar Faruku😂🤗, karkimin fatalwa da daddare kuma yasin😤).
Yanda Sarauniya ta iya hira har bansan sanda nake bata duk amsar data buƙata daga gareni ba, har takai munyi zurfi sosai a hirar fiye dazaton mai hasashe, kiran sallar zuhur ne ya tashemu, muka koma ɗakinmu domin yi, nidai banyi yunƙurin yiba tunda naga jini a jikina dukda dai kaina a ƙulle yake.
Muna cin abinci kira ya shigo wayar Amaturrahman, ɗaukata cike da zumuɗi tana faɗin “Meenal kun tahone?” bansan mi akace mata daga canba naji cike da murna ta sake cewa, “Wlhy da gaske nake tana nan har sai lokacin tarewarta”. Daga inda nake ina jiyo ihunsu, itama ta miƙe tana rawa da ihu. Nikam mamaki suke ban, Amaturrahman irin tsagwaron izza da mulkinan na ƴaƴan sarakuna sam batayi, ko kiga tana wulaƙanta bayi tana takasu yanda takeso, abinda kawai na fahimta tarbiyyace daga iyayensu hakan, An nuna musu bayin gidansu mutanene tamkarsu masu daraja da mutunci, shiyyasa sam basa tozartasu.
Ban tambayeta su wayeba muka cigaba da ƴar hirarmu, dukda nifa dauriya kawai nake hankalina ya rabune kashi-kashi. Ba'afi mintuna talatinba saiga ƴammatan ranar da muka taɓa haɗuwa a Saloon tare da su Amaturrahman ɗin, Meenal da Amatullah, ashe tafiya sukayi shiyyasa ban gansuba tunda nazo. Suka rungumeni cike da murna, ni harma mamaki suka bani, gasu suma da shegen kauɗi, aiko yinin yau dai kaina har ciwo yake saboda surutunsu, amma zamana dasu ya ɗeben kewa sosai, sai nake ganinsu kamar su Ummie. Muna tare Zuhrah ta kira waya, yanda sukaji muna waya da ita tana tsokanata Amatullah ɗiyar Buzaye mai cike da sirrin ƙyau ta fige wayar ta saka a hansfree kowa yanaji, a cewarta suma yanzu ai ƙawayen Zuhrah ne, d
uk ƙawayena sun zama nasu suma.
Abin mamaki da daddare saina nema jini na rasa, baƙaramin ɗaure kaina al'amarin ya sake yiba, ni a ƴan kwanakinnan sam bama na ganema kaina, daga wannan al'amari ya wuce sai wannan, ALLAH na gode maka da wannan jarabawa, ya rabbi ka bani ikon cinyeta, ka ƙaramin haƙuri da juriya.
(Amin Sakwara🚴🏼)
________________________________
“Nifa wannan wasan naku dariya yake bani kaida Qaseem Boss, gashi yanzu Mami ta sake tunzura komai ya ɗau zafi, shi bazai yarda da ƙaddara bane ba?”. Murmushi Jay yayi baice komaiba, sai ƙoƙarin saka waya da yake a kunne. Daga can Abbati yay sallama. Amsawa Jay yay suka gaisa. Yace, “Ina fatan yau zaka tashi aiki da wuri dan inason ganinka, banason kuma a wuce yau saboda muhimmancin zaman”. Daga can Abbati yace, “Babu damuwa, ai kama yanka akan gaɓa, dan inason na shigo namaka ta'aziyya dama, zan shigo bayan magriba da safe sai na wuce”. Jay yace, “Kai malam nifa yanzun ƙattai sun daina kwanarmin a gida inada iyali”. Ba Abbati ba hatta da Jabeer dariya ya kwashe da ita harda ƙyaƙyƙyewa, Jay ya mangarema Jabeer kai tareda ranƙwashi mai zafi, yace, “Kaima ɗan iska na wayar zan kamaka ne, masu zuwa lahira da ido ɗai-ɗai”. Bai jira amsar abbati ba ya yanke wayarsa. Jabeer dake sosa inda Jay ya ranƙwashesa yana tuƙi yace, “Oho dai, ai sa idon namu mai lasisi ne, ni nama taɓa ganin munafukin soyayya irinka?, ALLAH zan cema sarauniya karta bar Mami ta tare har sai kazo da kanka ka furta kana SO da hawaye”. Taɓe baki Jay yayi da kwantar da kansa jikin sit ya lumshe idanunsa, a hankali yace, “Idan namata ciki a waje saiku barta ta tare ɗin, koku bari saita haihu kukaita da ƴar ko ɗan”.
Jabeer dake ƙumshe dariya yace, “Ainasan kai waliyyine bazakai hakanba”.
Shiru Jay yay tamkar bazai tankaba. Sai kuma zuwa can ya zubama Jabeer ɗin harara ya ɗauke kansa.
Kasa daurewa Jabeer yay ya kwashe da dariya yana dukan sitiyari. Jawaad yay guntun tsaki da faɗin, “Kaifa wani lokacin baka da man kai, ka isheni fa”. Jabeer dake dariya yace, “Baka da amsa yanzu, sai mun isa inda zan saida wannan jaridar tukunna”. Banza Jay yay masa bai sake magana ba, saima kansa daya sake kwantarwa jikin kujerar yay luf.
Gaba ɗaya a wannan yinin Jay yayisa cikin aiyuka, Baibar Office ba sai bayan sallar isha'i, haka ya tashi a gajiye, gida ya wuce kai tsaye dan Abbati harya kirasa ya sanar masa ya iso, ada idan zasu haɗu A.Y street suke haɗuwa, yakan daɗe bai kawo aboki family house ɗinsuba sai idan ta kama dole, to a yanzu wancan gidan a hargitse yake dan amma fidda komai na cikinsa aiki akeyi tuƙuru da sauya fasalin abubuwa.
Tare suka shigo da Abbati dake ɗauke da jikkar Jay ɗin a hannu, basu zauna falon ƙasaba saboda yay datti sosai, suka haye sama, anan yabar Abbati shikuma ya shige bedroom dan yaɗan watsa ruwa. Ya sauke idanunsa akan gadonsa ya lumshesu yana maijin wani iri, jiya iyanzu suna nan tare. Wasu abubuwan data dingayi ya tuna, babu shiri murmushi ya suɓuce masa, aransa mamaki ma yake yanda take matsoraciya ya akai ta shiga aikin nan? Bashi da mai bashi amsa dan haka ya nufi bayi, bai wani jimaba saboda yanaso su tattauna da Abbati ya kwanta da wuri, yay shiri cikin kayan barcinsa farare tas masu taushi wandon har ƙasa. Dama ya sayo musu abinda zasuci a hanya, hakan yasa yana fitowa ƙasa ya sauka ya ɗakko filets ya dawo inda Abbati ke zaune yana kallo. Sake gaisawa sukai, Abbati na juye kajin a filet Jay kuwa na daga can wajen D/table yana haɗoma kansa Shayin da shansa ya zame masa jiki yanzun, takai har idan baima shaba bayajin daɗi.
“Ni ina nawa shayin?” cewar Abbati. Hararsa Jay yayi ya ɗauke kansa ya maida ga tv, “Sai kazauna tunda ni matarkane na kawo maka”. Abbati ya miƙe yana faɗin, “Kazama matata aiban moreba Yasin, ina zani da gabjejen ƙato kamarka”. Murmushi kawai Jay yayi ban sake tankawaba, saima shayinsa da yakesha hankali kwance har Abbati shima ya dawo ɗauke da nasa.
Bayan sun sake gaisawa sukai jimamin rasuwar Gimba sosai sannan Jay ya ɗora da faɗin, “Bana babu Gimba, dama shike tsaye akan rabon kayannan na azumi Abbati, narasa wazan ɗauka yay aikinan, gashi ya kamata