Sashe 77
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin lokacin sallar zuhur yayi sai ya tsaya yay sallah kafin ya ƙarisa station, tunkan ya shiga office ɗinsa ya samu kira daga sir Ahmad, fasa shiga nasa office ɗin yay ya nufi na Sir Ahmad ɗin. Ba'a masa iso dan zai shiga office ɗin sir Ahmad, knocking kawai yakeyi a bashi iznin shiga. Yanzunma kansa tsaye ya isa yay knocking ɗin, daga ciki sir Ahmad ya bashi izinin shiga dan yana kallonsa.
Cikin girmama ya gaishesa, Sir Ahmad ya rufe file ɗin gabansa yana kallon Jay ɗin dake zaune, “Ina ka shige hakane tun ɗazun nake aike a kiramin kai?”. “Am sorry sir na fitane”. “Okey to ya ƙarin haƙuri?”. “Alhmdllh sir”. “To ALLAH ya gafarta masa, ya raya abinda ya bari. Na kiraka ne dama akan Qaseem, wai yau kwana biyu yana hannun police”. Cike da mamaki Jay yace, “Police kuma? Basusan shiɗin wanene ba?”. Murmushi Sir Ahmad yayi yana kwantar da bayansa jikin kujera, “Sun sani sarai, gabace da gabanta, ya mari wani Doctor ne a General hospital shekaranjiya lahadi harya fidda masa jini, to Doctor ɗin ɗan Alhaji ɗan-iya warzu ne, shinefa yakai maganar hukumar lafiya ta ƙasa baki ɗaya, sukuma suka saka aka kama Qaseem ɗin”. Huci Jawaad ya furzar , shi shaf yama manta yabar Qaseem ranar a asibiti, yaso ya koma amma sai aka samu akasi, ya tabbata dalilin abinda ya faru ranarne Qaseem ya mazge Doctor, shi baisan yaushe Qaseem zai daina halin ƴan danbe ba ya rage baƙar zuciya. Yace, “Yanzu miya faru to Sir?”. Sir Ahmad yace, “I.G ne ya kirani da safen nan yake sanar min cewar shi Warzu yace sai anje kotu, shikuma yaga ɗaya daga cikin yaranane shiyyasa ya kira ya sanarmin dan anrma lauya, kuma ko babansa ma bai saniba”. Murmushi ne ya kufcema Jay, dan kuwa dai yasan lallai da Dad yaji da ba'a zauna lafiyaba, dan inma ɓakin son ƴaƴane Dad yatake Warzun ya shanye. “Miya baka dariya?” Sir Ahmad ya faɗa yana tsatstsare Jay da idanu. Kai Jawaad ya shafa yana ƙara sakin wani murmushin, “Sir abinne nasu ne ai, ni nasan Dad da yasan Qaseem na cell da yanzu garinan ya fara yawo a gajimare dan rikicinsa, kafaɗamin wane station ne? zanje na fiddosa yanzun insha ALLAH”. “To aini banƙi in baka damar cirosanba, kaima rikicin naka nake tsoro ai, dan baka da maraba da Dadyn naku, ta wani wajenma ka fisa zama ɗan ƙunar baƙin wake, nikuma banason ka haɗa harƙalla da Warzu dan shaiɗanin mutumne da kake ganinsa kullum cikin manyan kaya”. “Karka damu Sir salin alin zamu dawo”. “To shikenan gashi, saika nema lauyan Qaseem ɗin kuje tare”.
Sallama Jay yaymasa ya fita.
Bai koma office ba ya sake ficewa, harga ALLAH bazai iya jurar tuƙiba, haka yake shi baison tuƙi saita kama dole, dolene yasan mafita, to amma shikam ‘Wane driver ne zai iya maye masa gurbin Ginbansa?’ yay maganar cikin rai zuciyarsa na masa zafi. Office ɗin Jabeer ya shiga, babu jimawa suka fito tare. Jabeer ɗinne ya jasu, sai da suka fara tafiya yaɗan dubi Jay ɗin daketa faman danne-danne a tab ya ɗauke kansa ya maida ga titi “Na zatafa wajen rasuwarnan ka koma?”. Jay da bai ɗagoba bai kuma fasa abinda yakeba yace, “A'a, dama sonake sai gobe idan ALLAH ya kaimu mu koma mu duka”. “Okey ALLAH ya kaimu” cewar Jabeer yana maida hankalinsa ga tuƙin.
Asibiti suka fara zuwa wajen Doctor Ballo Warzu, cikin girmama ya tarisu yana tambayar jikin Bilkisu?, mafi yawan amsarsa Jabeer ne ya bashi ita, sai da suka gama gaishe-gaishensu sannan Jay yay masa magana akan abinda ya kawosu, da tambayar miya faru bayan tafiyarsa?. Labarin komai Dr Bello ya basu, Jay ya dafe kai cikin takaici.
Shi dai Dr Bello haka kawai komai Jay yayi ƙyau yake masa da burgesa, haka ALLAH ke sakama bawa ƙaunar wani batare da wata manufa ba, yay murmushi yana kallonsa, “Karka damu abokina na haƙura indai nine, bansan ɗan uwanka bane dana barsa tun a ranarma baza'a kai hakaba saboda kai, naga rashin hankalin nasa ne yayi yawa shiyyasa naga gara aɗau mataki, amma yanzu kam ya
ci darajar mai daraja”.
Fuskar Jay ɗauke da guntun murmushi yace, “Nagode Doctor ALLAH yabar zuminci”. Shima Doctor godiya yaymusu, ya kuma rakosu har inda motarsu take, sai da yaga fitarsu sannan ya koma office yana kiran babansa a waya.
★★★★★
Tunda suka shigo police station ɗin aketa basu girma, kai tsaye office ɗin d.p.o suka nufa, inda acan ɗinma dai suka tarbi juna da girmamawa kafin a ɗaura da gaisuwar mutunci. Jay da kansa yayma d.p.o bayanin abinda ya kawosa, ya kuma nuna masa lawyer'n Qaseem ɗin da ya shigo a bayansu dan shi isowarsa kenan. A take anan aka kashe magana babu zancen zuwa kotu sannan aka kawo musu Qaseem. Babu abinda akai masa, dan ko hararsa babu wanda yayi tunda aka kawosa gurin saima girmamawa, ko kayansa ba'a cire masaba, sannan ba'a haɗashi da kowaba a cell.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Jay, kowa ya ɗauke nasa fuska a tamke, Jay ya fara miƙewa ya fice abinsa, hakan yasa Qaseem jan tsaki, rai a ɓace ya kalli d.p.o yace su maidashi cikin cell ɗin. Duk kallon mamaki suke masa, Jabeer da yasan wasan ya dafa Qaseem ɗin yana magana a hankali, kamar Qaseem ɗin bazai yardaba sai kuma miya tuna oho masa ya nufi hanyar fita Jabeer da lawyer ɗinsa suka take masa baya.
A jikin mota suka iske Jay tsaye yana magana da Engineer ɗin da zai masa gyaran gidansa da Bilkisu zata zauna. Suna isowa yana ajiye wayar dan sungama. Sake ma juna kallon ido cikin ido sukai shi da Qaseem, cikin ɗacin rai Qaseem yace, “Miyasa ka cironi? Minene haɗina da kai?”. Murmushin rainin wayeo Jay yay masa yana lasar lip ɗinsa na ƙasa, yaɗan ɗage gira cike da salo dukda idanunsa na cikin glass ne, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa suke, Yace, “Inada business da kaine shiyyasa”. Wani kallon banza Qaseem yayma Jay shima, yace, “A kasuwa ka ganni?”. Jay ya sake murmusawa tare da ciro hannunsa yaɗan sosa gefen girarsa da ɗan yatsa yana karyar da wuya, “Karkai taurin kai, akwai tagomashi mai yawa da riba”. Qaseem yaja tsaki ya motsa zaibar wajen yana faɗin, “Zanyi maganin tsagerancinka ne yaro kwanan nan”. Cike da rainin hankali Jay yace, “Ai zuru batacin zuru, sai dai a haɗu ai zuru-zuru. Nabaka nanda kwanaki bakwai kacal zaka nemeni da kuɗinka ma”. Qaseem yay wata dariyar kai banzane ya wuce motar lawyer ɗinsa batare da yabama Jay amsaba....
Jawaad yay wani lalataccen murmushi yana zare gilashin idonsa, sai da Qaseem ya shiga motar sannan ya maida glasess ɗinsa yay salute ɗin motar da faɗin, “YANZUN MUKA FARA”. (Bari na ƙarasa maka jikan Yusufa🤣. WASAN😉).
________________________________
Ƙarfe sha biyu da wasu mintuna na farka, ni kaɗaice a ɗakin, na sauka daga gadon ina addu'a da miƙa, naji daɗin jikina sosai gaskiya, rashin barci ai masifane. Wanka na shigayi, amma abin mamaki sai nai karo da Jini, cikin mamaki nace, “Jini kuma? To duka yaushe ma nai wankan tsarki? Kofa sati biyu banyiba”. Mamaki tamkar zai kasheni nai wanka na fito. Ina shiri ina juya al'amarin cikin raina. Shigowar Amaturrahman ne ya sakani juyawa na kalleta. Tai murmushi da faɗin, “Amarya saifa wani Shining kikeyi miye sirrin ne?”. Murmushin yaƙe na mata kawai bance komaiba, itama tai dariya kaɗan, “Kefa tuni na lura irin Marwah ce, muskilanci ya muku yawa, idanma an zauna hira daku daga eh sai uhm sai a'a kuka ƙware yi, badai haka za'aje anama Yayan namu dunɗun dunkum ba kamar hadarin maraice?”. Bansan sanda na ƙyalƙyale da dariya ba babu shiri, dan harga ALLAH taban dariya musamman yanda tayi da fuska sanda zatai maganar. Ta ɗagamin gira da cewar, “Ko kefa, gashi na sakaki kin dara, ki shirya muje Ummu na jiranki, yau dai tace sai taga ƴarta”. Naji daɗi a raina, sai dai ina ɗanjin tsoro-tsoro, nice yau zan gamu da Sarauniyar gagara badau gaba ɗaya, ni Bilkisu ɗiyar baba makaho da Asiya gurguwa, ALLAH sarki duniya, duk abinda kaga ba'a gani saboda ƙanƙantarsa wataran zai fito kowa ya gansa saboda girmansa, wataran kuma sai tsufa ya sakayashi, a ƙarshe mutuwa ta ɓoyesa. Tsaf na shirya da taimakon Amaturrahman cikin siket da riga na atanfa da sukaimin ɗas a jiki, dukda dai basu kama jikina ba,
duk yanda tasi hanani na saka gyale kasawa nai saida na saka sannan muka fito.................✍
Barkanmu da dawowa, ina fatan kunyi weekend cikin ƙoshin lafiya😉😘😘😍😍😍😍.
Masu kira akan zasu sayi ƘWAI CIKIN ƘAYA!! bafa shi ake tallaba, muna tallar buks ɗinmune guda goma na zafafa gasunan, duk wanda bai sayaba ya motso ya saya karya bari romon daɗi ya wucesa🤗🤗🚴🏼
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO