Sashe 79
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ace tun jiyama aka fara rabonsu kamar yanda marigayi yakeyi”. Abbati yace, “ALLAH sarki rayuwa kenan, ALLAH ya gafarta masa, lamarine na mutane sai addu'a, sam bama tsoron ALLAH, wanda ya bada baiji ƙyashiba sai kaga masu rabawa sun zama azzalumai, amma kuma wai da an tashi zagin shugabbani suma sunada bakin jefa nasu”. Jay yace, “Humm, ai Abbati ɗan adam barshi yanda ka ganshi kaji, lokacin daka bashi zuma ya lasa zai sanar maka da daɗi yama gode maka, amma da saɓanin hakan ya gitta kafi kowa muni a idonsa. Manta da wannan maganar muyi wadda ta fita muhimmanci. Yanzu dai kafinma akai ga mahanar fidda kayan, kayan abincinmu da zamu saida sunada yawane?”.
“ALLAH na tuba boss ai suma ɗin dai kamar ƙyautarne, tunda ana saida musu ne bisa farashi mai matuƙar sauƙi, duka stores ɗinmu cike suke da kayan abinci kamar kowacce shekara, idanma munada ƙarancin wani abu to manja ne gaskiya”.
“Karka damu, batun manja nayi magana da Jessica ɗazun, insha ALLAH zuwa jibi zai iso, inason linka kayan da ake rabawarne, to da nayi tunanin sayen waɗanda muke dasu a ƙasa, sai dai ɗazun kuma wani tunani yazo mani, gara mu saya hannun ƴan kasuwa, shikuma namun mu saida musu akan farashin da aka saba ɗin bisa ƙaramar riba”.
“Banƙi ta takaba Jay, amma kaima idan ka sayi namun ai zaka samu sauƙi, dan naga wannan karon abubuwan sun taso da yawa, ga maganar gyaran gida naga ka saka, hidimar aure ta wuce wasa ai”. Ɗan lumshe idanu Jay yay yace, “ALLAH zai rufa asiri Abbati, muyi hakan kawai, inason zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu a kammala siyayyar, dukda guri ya ƙure zuwa jibi sai a fidda kayan, kayanmu kuma da za'a saida yakamata kuma ku fiddasu ai”.
“Eh dama munyi dasu Labaran gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai baja koli, shiyyasama nace zanzo na sameka yau ɗin, zan ɗauki hutun sati guda wajen aiki insha ALLAH muga an raba kayan yanda ya kamata mabuƙata sun samu”.
“Nagode sosai Abbati, nayi magana da Alhaji Garba yadi, amma Jabeer ne zai tsaya nan ɓangaren shi da su Aliyu dan aikin yamaku yawa kuma, inason wannan shekarar insha ALLAH muhaɗa da tufafi wa ƙananun yara suma, ni kuma inason hankalina ya tsaya wajen gyaran gidannan ne”.
Cikin jin daɗi Abbati yace, “ALLAH ya saka maka da alkairi ya ƙara buɗi, ALLAH yasa baɗi iwar haka muna nan muna shagalin sunan babys ɗinmu. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba. Sun cigaba da tattaunawa har kusan 12 sannan suka kwanta, Abbati a ɗakin baƙi da Jay ya shiga ya taimaka masa suka gyara, shikuma ya koma ɗakinsa ya kwanta.
WASHE GARI.
Washe gari Jay suka koma garin su Gimba, ta'azziya suka sakeyi, shima kuma aka sake masa dukda wasu harda munafunci dan sun dasa ƙananun magana akan Jay ɗan ƙungiyar asirine, shine yakai Gimba ma aka shanye nasa. Kasancewar shi mutumne mai saurin fahimtar abu kafin su baro garin ya karanci abubuwa masu yawa daga mutane, ya kuma saka an bincika masa inda ɓaleru yake ta hanyar iyayensa da basusan dawan garinba. Zuwa Azhar suka baro garin.
Tunda suka dawo daga garin su gimba aiki yake babu hutu, kiran sallar la'asar ne kawai ya tadashi, bayan an idar office ya dawo ya ɗora daga inda ya tsaya. Zamansa baifi da mintuna goma ba Hafiz dake ɗauke da takardu a hannu ya shigo office ɗin da sallama..
Batare da Jay ya ɗagoba ya amsa masa. Hafiz ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana faɗin, “Yauwa boss ga file ɗinan na gama tattare komai, abinda ya rage mana kawai yanzun shine bin sawunsa kawai, kaga dai dukkan abinda muke buƙata mun riga mun gama samunshi”.
Jawaad ya ɗago yana ɗan bubbuga pen ɗin hannunsa akan laɓɓa, takardun da Hafiz ya ajiye ya ɗauka, sai da ya gama dubawa sannan ya sake ɗagowa ga Hafiz ɗin, “Kamar ba komai ne anan ba ai Hafiz, Rose ta baka dukkan bayanan dake hannunta ne? akwai kuma bayanan Restaurant ɗinan shima ban gansaba anan?”. Hafiz yace, “Oh sorry, wlhy nama shafa'a sosai, na gidan cin abincin nan kamar suna hannun Mami ne fa, jiya naso amsa, sai kuma na iske batazoba, bara na amsosu, saina haɗo dana hannun Rose ɗin”. Dakatar dashi Jay yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. “Rose ta fita ita da Aliyu, Miemaa Kirata ta kawo, nima akwai aikin dana sakata ma ita da Daw
ood shi ya kawo nasa ita shiru kakeji”. Miƙewa Hafiz yay zuwa gaban landline ɗin office ɗin yana faɗin, “Bara muji to kota kammala duka”. Jay baice komaiba ya cigaba da aikinsa, yayinda Hafiz yay waya department ɗin su Bilkisun. Baifi mintuna goma da ajiye wayarba akai knocking ƙofar.
★★★
Tunda nazo office ban gansaba, ban kuma je inda yakeba, ina namu office ɗin na duƙufa dukkan ayyukan dake gabana, sai hirarmu da bata ƙarewa ni da Ummie.
Kasancewar jinin dana gani jiya tun a daren na nemesa na rasa yasa dukkan sallolina yau nayisu batare dana sake ganinsa ba kuma. Mun fito sallar la'asar kowa ya koma kan aikinsa. Nayi nisa sosai akan aikin da nakeyi saƙon kira daga office ɗin Boss ya sameni. Dukda nasan dalilin kiran sai da gabana ya faɗi, dama tun ɗazun Dawood ya sanarmin ya kai masa aikin daya sakamu tare saura ni yake jira. Miƙewa nai na tattare files ɗin guda biyu na fita.
Da sallama na shiga office ɗin bayan nayi knocking an bani izinin shiga, naɗanji sanyi ganin akwai Oga Hafiz a office ɗin, shinema ya amsan sallamata, dodon nawa kam bai ko ɗagoba, gaba ɗaya hankalinsa nakan Computer, inama shigowa ƙarar danna keyboard ɗinsa ce ta fara tarata, yanda yake dannawar da sauri-sauri yasa akejin ƙararsu sosai. Da fara'a oga Hafiz ya tarbeni, na gaishesa ina miƙa masa file ɗaya a cikin biyun dana shigo dashi tunda nasan dama shine wanda zan baiwa. Ɗayan kuma na matsa tebirin boss na ajiye, murya a sanyaya nace, “Barka da yamma”. Batare daya ɗagoba yace, “Barka” ya cigaba da aikinsa. Duk da yanda yaymin ɗin haka na sake dannewa nace, “Gashi na kammala, sai dai result ɗin sayin hannun nasa ɗin bai fitaba”. Dakatawa yay daga abinda yakeyi ya ɗago min manyan idanunsa da a yau suke farare tas, sai dai sunɗan kumburo alamar cike suke da gajiya, sauri janye nawa nai lokacin da sautin muryarsa ta fara isowa cikin kunnena. “Wakika kaimawa?”. Yay maganar har yanzu idanunsa a kaina dan inajin yanda suke shiga ɓargona. Cikin nutsuwa ta nace, “Sir danaje office ɗin Umar bayanan saina gamu da Hashim”. Cikin kaushin murya yace, “Hashim! Kina nufin shi kika bamawa!?”. Yanda yay maganar ya sani ɗagowa na dubesa da sauri. Dan masifa har fararen idanun nan dana gani yanzu sun sirka da ɗan ja, na kula da yashiga ɓacinrai zakaga idanunsa sun sauya kala. A ɗarare na ɗaga masa kai kawai. Uffan bai sake cewaba ya ɗauki wayar landline yay kira.
Hafiz da duk yana zaune yana kallonsu ya kalli Bilkisu, “Mami garin yaya kika bama Hashim bayan bashi akace ki bamawa ba?”. Kaina a ƙasa nace, “Wlhy ni bansan akwai matsalaba ne, na fito shikuma zai shiga office ɗin shine yake tambayata ko lafiya? Nikuma nace masa wajen Umar nazo, shine yace bara ya ajiye masa anjima saina dawo na amsa, to kafin na koma ɗinne kuma mukai fitar ranar, jiya kuma banzo office ba, ɗazun nakoma amsowa danna tattare komai shine Umar ɗin ya sanarmin bai bashiba, amma ya fita idan ya dawo zai tambayesa koya mantane”
Hafiz ya ɗan girgiza kansa da faɗin, “Ki ringa kula kinji, duk wanda ba'ace kibama abububa kidaina bashi, wannan aikin namu da kike gani kowa takansa yakeyi, shiyyasa zakiga a komai ana taka tsantsan, bara ni naje wajen Hashim ɗin da kaina Boss”.
Jawaad ya dangwarar da kan wayar a ƙasa saboda yakasa samun Umar ɗinma, bai cema Hafiz komaiba harya fice.
Kansa ya dafe cike da takaici, ya miƙe tare da tura kujerarsa baya da ɗan ƙarfi ni harma na tsorata, yay taku ɗaya biyu kafin ya juyo yana kallona, yanda ya matso daf dani yasani maida kaina ƙasa, yaɗan buga tebirin da faɗin, “Wai sai yaushene zaki daina bani ciwon kai ne yarinyarnan? Wataran saina sauya miki kamannin fuskarnan taki maikama data mage idan baki dawo hankalinki ba” yay maganar da yunƙurowa kamar zai makeni. Baya nai da sauri, cikin zafin nama na tura kujerar na miƙe tsaye, dan yanda ya fusato ɗinan nasan iya makeni zaiyi ɗin.
Jay da takaici yake neman shaƙema numfashi yace, “Zonan, idan kuma kika bari ni nazo saina karya ƙasusuwanki”. Idanuna cike da ƙwalla na kallesa ina tura baki, kafin na samu damar bashi haƙuri yace.
“Ni kike murguɗama baki?!”.
Saurin ɗagowa nai ina ƙwalalo idanu waje, kujimin sabon sh
arri, ni yaushe na murguɗa baki dan ALLAH jama'a?. ganinfa da gaske ni yake nufowa fuska a ɗaure sai na fara ja baya, bai fasa biyoni ba kamar yanda ban fasa tafiya da bayaba ina yarfe hannu, jinai tamkar na saki fitsari, yayi bala'in ɗaure fuska yanda na tabbatar yau idan ya kamani sai ya karyanin da yake faɗa. cikin sarƙewar harshe nace, “Ni wlhy ban murguɗa maka baki ba fa Sir, kuma ALLAH bani da lafiya ma”. Nai maganar dai-dai na dangane da bango, shikuma ya iso daf dani.
Ina rufe baki ana turo ƙofar, ido huɗu mukai da Rose, kafin bakina ya iya sake furta wani abu naji an fisgoni na faɗo saman ƙirjin mutum.............✍