Sashe 2
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
______________________________
A daren jiya juma'a misalin ƙarfe sha biyu da wasu mintuna mummunan labari ya iso gidansu Jawaad, cewar Uncle Usman ya samu haɗarin mota a hanyarsa ta dawowa daga tafiyar da yayi ta kwanaki biyu.
Lallai wannan gida sun fuskanci tashin hankali na bazata, dan bayan mahaifin Jawaad basu ƙara rasa ko ɗaya a cikinsuba, kaf ƴaƴan malam Yusif Abdul-aziz ne kawai ALLAH yayma rasuwa. Saiko shi malam Yusif ɗin da matarsa ɗaya sai mama maryam, idan ka cire waɗanan huɗun sauran duk sunada ransu, saima yaɗuwa da suka sake yi saboda haihuwar jikoki harma da tattaɓa kunne.
Ruɗanin da mama Atika ta shigane ya sakata yanke jiki ta faɗi, dan abune da tunaninsu bai taɓa kawo musuba anan kusa duk da sunsan mutuwa tabbacice ga duk mai rai, ba Uncle Usman ba ko ita kanta data tsufa sosai bata tuna mutuwar zata iya ɗaukarta a yanzu balle shi da ayanzune ake ƙara shiryama duniyar filin zama.
Lokacin da gidansu Jawaad ke cikin wannan ruɗanin shi yanacan suna gumurzu da wasu gungun ƴan ta'adda da suke fako tun kusan sati uku da suka shige, sai a yaune ALLAH ya basu nasarar yin fito na fito dasu, sun sami nasarar kama wasu a cikinsu, yayinda wasu suka gudu.
Kusan ƙarfe huɗu na dare suka iso station ɗinsu da waɗanda suka cafko, sunyi tiɓis da gajiya, ga yunwa dake cin hanjinsu ta bala'i ma kuwa, sai dai jarumtarsu da juriya mai haɗe da trianing ɗin da suka gogu a ciki duk ya ɓoye gazawarsu. Rose cema dai kawai ta kasa juriyar kasancewar ƙarfin zuciyar mace dana namiji ba ɗayaba, dukda itama ta cancanci a kirata jarumar kuwa, Jawaad ma baiso akai aikin da itaba, amma ta matsa akan sai taje, badan yasoba ya barta ta bisu.
A station ɗin suka ƙarasa kwanan, washe gari safiyar asabar ana idar da sallar asuba Jawaad ya kira gimba akan yazo ya ɗaukesa. Yanda yaji muryan gimban ne ya bashi mamaki, cikin yanayin gizagonsa yake jefa masa tambayar lafiya?.
Sanin halinsa baya son ɓoye-ɓoye a magana ya saka Gimba faɗa masa gaskiyar tashin hankalin da ake ciki a gidan nasu.
Dukda halin da yake ciki da matsalolin dangin mahaifin nasa hakan bai hanashi shiga ƙololuwar tashin hankaliba, a take ya birkicema su Jabeer, waɗanda suma jin rasuwar tai bala'in sakasu a ruɗani. Basu wani ɓata lokaciba suka nufi gidansu Jawaad ɗin kai tsaye, duk da halin gajiya da buƙatar hutun da suke a ciki. Sun iso gidan ƙarfe kusan bakwai da wasu ƴan mintuna, hankalin Jawaad ya sake tashi sosai ganin halin da ahalinsa ke a ciki, tuni ya manta da gajiyar dake tattare dashi.
Bai zaunaba su Uncle Nasir suka jashi zuwa asibitin da gawar Uncle Usman take domin su amso, abinda yasa ba'aje tun jiyaba saboda ba'a nan cikin gari bane, inda ya baro yafi kusa da inda yay haɗarin, shiyyasa aka maidashi asibitin can garin.
★★★★★★★
Ƙarfe goma da wasu mintuna muka iso gidansu Mom, katafaren gida na alfarma da ƙawa, dukda cikin tashin hankalin mutuwa mukazo hakan bai hanani mamaki da jinjina dukiya irinta wannan ahaliba, lallai dolene su aunty Shahudah suyi wulaƙanci yanda sukeso, kaga gida tamkar ba hannune ya ginashiba, harabar gidan kawai naganimafa kenan, sai mutanen gidan da zakaima kallo ɗaya ka fahinci ƴan bokone na haƙiƙa tun zamanin da boko keda tsada da daraja kuwa......
Ina cikin wannan tunanin ne nafara jiyo ƙarfin koke-koke na ƙaruwa, babu shiri na dawo hayyacina, a sannanne na lura ashe an iso da gawar mamacinne.
Har ciki sosai Ambulance ɗin dake ɗauke da gawar ta shigo, ta tsaya dai-dai sashen danaji wasu na ambata da sashen mama Atika mahaifiyarsu Mom. Zuciyata tai masifar harbawa saboda ganin wanda ya fito daga Ambulance ɗin.
Cikin tsagwaron mamaki na furta “Boss kuma anan?” akan laɓɓana, kamar yanda nakejin zuciyata aduk sanda ta samu kusanci dashi yanzunma bata canja zaniba, dole na shiga karanto addu'a gudun kar nayi abinda zai jawo hankalin mutane a kaina.
Nayi nisa a tunanin da har aka fidda gawar ban saniba, saida suna gab da shiga sashin ne nakai idanuna kansu tare da sauraren koke-koken mutane, su biyune kawai ke ɗauke da gawar a mankara, tana lulluɓe da farin ƙyalle da yay face-face da jini, alamar dai mamacin ya bugu sakamakon Accident ɗin da yayi, nantake sai zuciyata tai rauni saboda tunowa da mutuwar nawa mahaifin, sai kawai na durƙushe a wajen na fashe da kuka mai cin rai da zuciya.