← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 168

Sashe 126

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ssauta tie.. ɗinsa yay ƙasa da shi, saima ya fincikesa gaba ɗaya ya jefa saman kujera ya shiga safa da marwa a office ɗin, duk da ac dake aiki hakan bai hanashi haɗa gumi ba, tun randa yasan akwai alaƙa tsakanin Alhaji kokino da Mr Gebrail ya saka ake bibiyar masa Mr Gebrail, ta hakane ya gano kuma alaƙar Mr Gebrail da ɗaya a cikin Uncle ɗinsa, idan ya dunƙule maganar waje guda hakan na nufin, Uncle ɗinsa, Mr Gebrail, Alhaji Kokino duk sunada a laƙa ta baɗini, dan a zahirance babu wannan alaƙar kota gaisuwa a tsakaninsu sai a ɓoye. dolene a daren nan a sato masa wayoyin Alhaji kokino, sai dai waye zai masa aikin? 'Dan dole ya kasance ɗan cikin gidanne zaiyi hakan' ya ƙare maganar a fili yana dafe kansa da furzar da huci mai azabar zafi.
Tunanin kiran bilkisu ne yazo masa a rai, dan kosu Hafiz bayason sakasu a wannan case ɗin yanzu, saboda ya haɗa da family nashi, sannan yanada sarƙaƙiyar yarda da wani, kai tsaye zai iya zama ganganci, bawai dan bai yarda dasu bane, dan su Jabeer sun wuce duk hasashen mai karatu a garesa, amma ciki ba'a yisa dan abinciba kawai ai. Bilkisu na ɗagawa yace, "Ina jiranki a office". Ya yanke wayar.
Kallon wayar kawai na tsaya yi da mamaki, to amma yanda naji muryarsa tamin kama da ta mai damuwa, miƙewa nai na fice, inajin Nazifa na tambayata ina zuwa? Ban sauraretaba na ɗaga mata hannu kawai. Koda nai knocking ba'a amsamin ba, dan haka kawai na shiga kaina tsaye. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganinsa ba yanda nai zatoba, ya ɗago ido ya kalleni sannan ya maida ga abinda yakeyi. Takawa nai na ƙarasa garesa, murya a sanyaye nace, "Wlhy nazata ko baka da lafiya, ya aikin?". Baice dani komaiba ya nunamin wajen zama, shima zagayawa yay ya zauna a kujerarsa, yanda ya tsatstsareni da idanu duk sai naji na takura, na risinar da nawa ƙasa ina kallon yatsun hannuna. Numfashi naji ya sauke mai ƙarfin, kafin nace wani abu ya fara min bayani akan kiran, ya ƙare maganar da faɗin, "Dole ne musami wayar a daren nan, dan itace zata bamu haske akan komai da gaggawa, aikin nan kuma dole mu biyu kawai zamuyisa ni da ke kawai, ko su Aliyu banason na saka sai na gama fahimtar komai".
Naji daɗin karrawarsa gareni sosai, dan banyi zaton hakanba, na gyara zamana, "To ina ganin mizai hana muyi amfani da cikin ƴaƴansa ko ma'aikatan gidan?". Shiru yay yana kallona da goga ƙasan biro akan laɓɓansa, kusan sakan goma ya janye ya maida kan takardar gabansa, ɗan rubutu yayi sannan ya sake ɗagowa ya kalleni, "Wannan shawarar taki tayi, amma babu wani ƙarin bayani a kanta?". Tsai na ɗan ƙarayi na tunani kafin nace, "Akwai, ya kamata wadda zamu saka ɗin cikin ƴaƴan nasa ta kasance mace, sannan mu nuna mata za'a cutar da shine shiyyasa muke son wayoyin na wasu awanni kawai za'a maido mata ta maida masa bayan mun saka matakan tsaro. Ko baiyi ba?". "Ihum inajinki cigaba" ya faɗa cikin lumshe idanu. Naɗan sauke ajiyar zuciya da cigaba da faɗin, "Idan muka amsa maimakon mu ajiye wayoyin a hannunmu kawai muyi copy ɗin komai na ciki sai a maida mata ta maida masa zuwa safiya". Lallausan murmushi ya saki yana ɗagemin gira ɗaya, "Ashe matar tawa ƙwaruwa ce?". Yanda yay maganar cikin zolaya yasa na rufe idanuna da tafin hannu ina murmushi. Yace, "Thanks Miemaa, da duk kaina ya kulle". Nace, "Haba dai, kaine kanka ke kullewa?". "Oh ni ba mutum bane? Duk ma ba kece kika rabamin hankali biyu ba". "Nidai babu ruwana". "Humm", ya faɗa kawai yana miƙewa. "Kinga tashi muje, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe".
Koda muka fito sai da ya shiga office ɗin Aliyu, babu jimawa ya fito riƙe da key ɗin mota, da kansa ya buɗemin na shiga sannan shima ya zagaya ya shiga, nidai addu'a nake a raina karyay gudu damu, yanda naci abincin nan na ƙoshi matsala za'a samu ai. Kasa daurewa nai na roƙesa karyay gudu dan ALLAH, ƙin tankamin yayi, sai ma waya daya ɗauka yay kira, kasancewar a Hans free ya sakata sai naji duk abinda suke faɗa, na fahimci da wani ma'aikacin gidan Alhaji kokinon yay magana, dan ya faɗa masa gamu mun taho ya fito mu haɗu a bayan layin. Dai-dai saitin wani shagon saida kayan abinci dake farkon layin muka tsaya, wani dattijon tsoho ya fito daga

shahon, kallo ɗaya naga yayma motar ya ɗauke kansa, sai kuma naga ya buɗe ya shigo baya. Motar boss ya harba gaba batare da yayi magana ba. Nidai mamaki nake tayi a raina, wannan aikin namu gaskiya saida jajircewa da cire tsoro, sai kuma ka iya kowanne irin salo na mutane masu wayo. Gaba ɗaya muka fita daga layin muka shiga wani, shima muka fita muka shiga na gaba, yana tuƙin yana kallon mirror, na fahimci dubawa yake yaga ko ana binmu, ganin babu wani mai bibiyarmu sai yay fakin gefen babban titi da muka fito. Sai lokacin ne dattijon yay magana. "Na tabbata babu wani mai binmu insha ALLAH". Kashe motar yayi ba tare da yace komaiba, ya ɗan kalleni sannan ya juya yana kallon dattijon. "Wannan itace matata, sunanta Bilkisu". "Masha ALLAH, kai ALLAH ya sanya albarka ya bada zuri'a tagari". "Amin" ya faɗa, ni kuma na juya muka gaisa da shi yanata sakamin albarka.
"Baba wannan karonma aiki ya sake kawoni gidanku, kuma ina buƙatar taimakonka kamar wancan karon". "Karka damu ɗana, zan baka dukkan taimakon da kake buƙata insha ALLAHU". "Nagode baba, akwai dattijuwar mai aikin nan da naji kuna kira maman yara ko tana gidan har yanzun?". Jimmm mai gadi yayi kafin ya sauke numfashi, "Gaskiya bata nan, a ƙalla zata kai kusan wata biyu ma kenan bata gidan nan". "Aiki ta ajiye kenan?". "A'a bata ajiyeba, mudai bamusan miya faruba, rana tsaka ɗanta yazo yana nemanta wai kwana uku bai samunta a waya" kallonsa Jawaad yake cikin nazari, "Kana nufin Yazeed?". "Ƙwarai shi kuwa, to dalilin zuwan nasane muka fahimci muma bata gidan, ita dai Uwargida tace ta tambayeta zataje gida wajen rasuwar ɗan yayarta, to nidai ALLAH shine shaida ranar data cika kwana uku da tafiya naganta da idanuna ta dawo gidan lokacin ina sallar isha'i, to amma abin mamaki sai naji ana cigiyarta bayan kwana biyu wai bata gidan". "Ban gane bata gidanba? Kai kuma bakaga fitarta ba?". "Wlhy ban ganiba yarona, dan ita macece mai yawan barkwanci inhar zata fita a gidan nan kota shiga saimun tsokani juna, to a randa ta dawo da yake salla nakeyi sai ban kawo komai a rainaba, abinda ma ya ɗauremin kai da sukace su basu gantaba randa ta dawo ɗin". Shiru boss yayi alamar tunani, dan haka nikuma nace, "To amma baba a wannan daren kana tunanin zata iya fita?". "Gaskiya bazata iyaba ƴata, dan maman yara ma tana da ciwon ƙafa bata cikason yawan kai kawoba". "Hakan na nufin tana cikin gidan kenan kokuma an fita da ita a daren, ko kaine idonka bai nuna maka dai-dai ba?". "Wlhy bana ko tantama itace ta dawo da mangaribar nan, to ƴata wazai fita da ita kuma sai kace wata kaya batare da an gani ba?, shaiɗanin daya taɓa kwatanta hakama mijinki yasa an kaisa gidan maza ai". Murmushi nayi kawai, na ɗan juya na kalla boss ɗin dake saurarnmu sannan na maida ga baba, "Baba a wannan ranar mota nawa ta shiga gidan ta kuma fita bayan dawowar maman yara?". "Babu wanda yazo tunda Alhaji baya gari ma, sai wani yaro ɗan dogo baƙi mai dogon hanci da ya kanzo lokaci-lokaci idan Alhaji na nan, to ni a ranarma da yazo ɗin saida na sanar masa baya nan ai Alhaji, sai yace ai ya sani saƙo zai bama hajiya inji Alhajin. Daga haka ban sake tofa komaiba na barshi ya shiga ni kuma na shige ɗakina, to baifi mintuna goma sha biyar da shigaba ma naji yana horn nazo na buɗe masa ya fice". "Kasan sunansa baba?" "A'a gaskiya ƴata, ban saniba wlhy".
Waya boss dake saurarenmu ya ɗauka ya shiga daddanawa, kafin ya miƙama baba wayar yana faɗin, "Shine wannan?". Amsa baba yay ya kalli hoton, cikin jinjina kai da murmushi yace, "Tabbas shine kuwa ɗana". "Baba ka tabbata?". "Babu tantama a zancena". "Shikenan mun gode, bara mu maida kai, sai dai zamu iya dawowa gareka a ko wane irin lokaci". "Babu damuwa wlhy ɗana duk sanda kake buƙatar wani abu ka kirani". Godiya muka sake masa, ya tada motar yay reverse, a wani wajen muka saukesa saɓanin inda muka ɗaukesa.
Jin yayi shiru sai na ɗan kallesa, "Hoton wanene ka nuna masa dan ALLAH?". "Zaki gani yanzun" ya faɗa yana karya kan motar muka shiga wani layi. A ƙofar wani gida madaidaici yay fakin, ganin zai fita nima sai na buɗe na fita. Mun gaisa da samari uku da alama ta nuna suke
Chapter 126 · 0% Book details