← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 168

Sashe 43

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

a ƙyar.
        Nuna mata Computer ɗin nayi ina zooming ɗin wani waje cikin video ɗin da faɗin, “Ummie kalla dan ALLAH mikika fahimta a wajen nan?”. Matsowa tayi sosai tana kallon wajen cike da nazari, kafin ta amshi mouse ɗin hannuna ta maida video'n slowly, “Kai bily kilura da ƙyau wani kasuwancin kurame akeyi a wajen nan fa, ki kalli zuwan yarinyarnan wajen da ƙyau, kafin ta ƙarasa wajen shi wannan mai kifin saida suka kalli juna da mai raken can sukaima juna wata inkiya da idonu, sannan bakin mai kifin ya motsa alamar magana yayi”. Kaina na shiga jinjina mata, nace, “Haka nima duk na fahimta Ummie, to amma sam na kasa fahimtar mi mai kifin ya faɗa, na maimaita wajen yafi sau goma wlhy, amma kuma abin lura anan shi wacan mai facin minene ya ɗauka cikin tayoyi ya bama gurgun yaron can almajiri?”. Baya ummie ta dawo da video dai-dai wajen, da alama mai ɗaukar video bai saka da mai facinba a ɗaukar, dan acan gefe yake yana harkokinsa shi kaɗai, hakan yasa ba komai ake iya fahimta dangane da shiba. “Bily kinsan mizakiyi?” nace, “A'a saikin faɗa”.  kije office ɗin boss kimasa bayani, inba hakaba zamu iya rikita komai anan”.
     Gabana ne ya faɗi jin ta ambaci boss, abinda ya faru jiya ya shiga mani kaikawo, gashi yau yanda na lura baije duba aunty Shahudah bama tun jiya da safe kamar yanda naji iyayenmu na tsogumi a asibitin, ALLAH dai yasa ba maganata bace ta jawo hakan, dan yakamata ace ya cika alƙawarin daya ɗaukama Dad na zuwa gidanmu a daren jiya......... “Lafiya kuwa? Ina magana kin tafi tunani”. Numfashi na kawo ina dafe kai, nace, “Babu komai, bara nakai masan”. Nasan yanda nai maganarne a sanyaye ya sakata bina da kallo, ban yarda mun haɗa idoba na cire flash  ɗin daga Computer'n na ɗauki takardun danake rubuta bayanan na tattare cikin file ɗin daya bani jiya na fita. Maimakon na nufi office ɗin nashi saina tafi office ɗin Oga Aliyu. knocking nai aka bani izinin shiga, su biyu na iske a ciki, hakan yasani gaishesu na tsaya gefe su kammala, dan naga magana suke. Basu wani ɗauki lokaciba wancan ya miƙe ya fita, oga Aliyu ya nunamin kujera alamar na zauna, sake gaidashi nayi sannan na zauna ina ɗora takardun hannuna a tebirin gabansa. “Mami ta samune?” yay maganar cikin zolaya. Murmushi nayi nima na bashi amsa da “Sosai ma”. Yay ƙaramar dariya yana amsar takardun, “To ALLAH yasa mai washa-washa ne da zamuci mu more”. Yanzunkam saida naɗan dara kaɗan, dan bansan yana magana mai tsaho hakaba, yaɗan duba takardun sannan ya kalleni, “Mami ban fahimci komaiba anan, na minene?”. Hannuna naɗan matsa kaɗan sukai ƙara, na muskuta zamana, “Oga Aliyu bayanan daga wani video suke” nai maganar ina miƙa masa flash ɗin hannuna da cigaba da faɗin, “Nice na haɗasu anan, to kuma na cije a wani waje shine nazo neman haske”. shiru yay na sakanni batare daya amshi abin hannunaba, kafin yace, “Okey, wanene ya baki aikin a cikinmu?”. Nace, “Boss ne”. Takardun ya miƙomin, “Kinga to kije wajensa, dan bansan case ɗin miye ba, nasan zai miki bayanin duk da zaki fahimta”. Shiru nayi na kasa amsar takardun.
      Aliyu dake kallonta yace, “Da matsalane?”.
     Kaina na ɗago na kallesa, sai kuma na sauke idanuna ƙasa, “ALLAH oga shi ya cika faɗan tsiya, yaytama mutane mazurai”. Dariya sosai Aliyu yayi da wannan magana tawa, saida ya gaji dan kansa yay shiru, sake miƙomin takardun yayi har yanzu fuskarsa da murmushi, “Ai sai an masa ba daidaiba yake mazurai, tunda akan aikine zai fahimceki bazaiyi faɗaba kinji”. Kaina na jinjina masa, badan nasoba na amshi takardun na fita. Jinake kamar karnaje, amma wani sashe na zuciyata na bani shawarar naje dan akan aikine, bai kamata kuma na sanya wasa akan aikinaba, nidai na kiyaye duk wata hanya da zata sake haɗani dashi harnaga fushinsa kamar na jiya kawai. Da wannan ƙwarin gwiwar na nufi office ɗin, knocking nai aka bani izinin shiga, gabana sai faman faɗuwa yake na tura ƙofar da sallama a ƙasan maƙoshi na shiga.
          Tarin aikine jibge a gaban Jawaad, ko buƙatar shigowar wanima babayi office ɗin, hakan yasa koda Bily ta shigo  sallamarta kawai ya amsa amma bai ɗagoba, ƙarasowarta gabansa ƙamshinta

ya tabbatar masa itace, sake ɗaure fuska yay sosai fiye da yanda ta shigo ta sameshi.
        Kallo ɗaya naima fuskarsa na ɗauke kaina, a ɗaure take fiye da kullum ma dana sani, gaba ɗaya ƴar jarumtar dana shigo da ita saita gudu itama, gashi yaƙi kallon ko inda nakema dukda inada tabbacin yasan nice na shigo. Da ƙyar na iya daurewa nace, “Ina kwana Sir”. Batare daya kalleniba yanzunma yace, “Lafiya”. Shiru nai nakasa cigaba da magana, dan yanda ya amsa gaisuwar tawa a daƙile ya sake sanyayamin jiki sosai, ganin tsayuwar tawa bata da amfani na daure nace, “Sir dama akan aikin daka bani ranar monday ne”. Harna fidda rai da samun amsa sai naga ya nunamin kujera batare daya ɗagoba. Ɓoyayyen nunfashi na sauke ina ƙara ƙoƙarin ƙarfafa kaina. Na ajiye takardun hannuna a gabansa kafin naje na zauna a kujerar, shiru muka sakeyi na mintuna, saida ya tattare wasu takardun gabansa waje guda ya ajiyesu gefe kafin ya kalleni. Saurin nuna masa takardun dana ajiye nayi. Janye idanunsa yay daga tsatstsarenin da yay dasu ya ɗauki takardun, shiru tsawon wasu mintuna yana dubasu kafin ya ɗago, yace, “Kin gama ne?”.
         Sau ɗaya na kallesa na ɗauke idanuna ganin ni yake kallo, na girgiza kaina, “A'a ban gamaba, akwai wani wajene a video'n to sai nakeson ka gani kafin na shigar da bayanansa” na ƙare maganar da miƙa masa flash drive ɗin, bai amsaba ya ɗauke kansa daga gareni ya maida ga Computer ɗin gabansa, “Taso kisa”. kamar nai kuka haka naji, sai dai bani da wata mafitar daya wuce bin umarninsa, inda yake naje, a mamakina sai naga ya tashi daga kujerar tasa ya nunamin alamar na zauna, batare da yace uffanba............✍

Yau shafin nakune ƴan telegram, kuma ku warwasa da wannan, alkairin ALLAH yakai gareku aduk inda kuke, ammafa babu canji mun ƴan hud-jay team ne😜😂😂😂😍😍😘😘😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.
[12/31/2020, 9:31 PM] Abubakar Saleh Kurami: Bilyn Abdull 📚:
Telegram link group ɗinmu kenan, dan wasu sunata tambaya cewa ya zasu shiga, indai kana tele to kawai ka antaya MASARAUTAR BILYN ABDULL tanan.

https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g

Page 19
Chapter 43 · 0% Book details