Sashe 124
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tana fita Jawaad ya daki kujerarsa daya tashi akai yana faɗin, “Wlhy yarinyar can saita bar aiki a cikinmu, kai ama station ɗin nan gaba ɗayansa”. Da sauri Aliyu ya taso yana faɗin, “Please Boss! calm down, don't waste your time for her, ba yanzu ya kamata ai wannan ba”. Hafiz yace, “Gaskiyane maganar Aliyu boss, micece rose da har haukarta zai dameka, nifa dama can bataimin ba, duk da tana da ƙwazo tana da siffofin mutane masu bala'in son kansu, ka barta saita gama shagala bazaka ɗauki matakin komai a kanta ba sannan ka ɗauka. Amma idan aka maida mata murtani a yanzu anma damu da ita kenan, abinda kawai za'ai mata shine winning, ayi bala'i bala'in winning ɗinta akan Mami, idan tace zata shigar mata hanci kacimin ubanta iyakar iyawa”.
Ƴar dariya Jabeer da ya shigo yayi jin furucin Hafiz ɗin, ya zauna yana faɗin, “ALLAH kai mugune Hafeez”. Zama duk sukayi suma, Hafiz yace, “ALLAH kuwa jabeer haukar yarinyar baimin ba, haka ake so ne banda hauka?, ni dama ni tace tana so ALLAH kuwa ko, hummm”. ya ƙare maganar da cije leɓe irin na tsantsar mugunta. Basu Jabeer ba hatta Jay sai da ya murmusa yana mai girgiza kansa, dan yasan Hafiz shegen kansane a iya mugunta.
Ya sauke ajiyar zuya da jan guntun tsaki. Aliyu yace, “Kayi haƙuri boss, mu munzo musha labarin Honeymoon shashashar ta wargaza komai”. Harara ya balla musu, dan haka suka kwashe da dariya suna tafawa. Jabeer yace, “Wlhy Jay kayi wani ɓul-ɓul da kai fa, ka kuma ƙara haske”. “Kana baƙin ciki ne ɗan sa ido?”. Jay ya faɗa yana jefa masa biron hannunsa. Dariya suka sake kwashewa da ita.
“Mtsoww, kufa wataran shashashancinku yawane da shi wlhy, ku ajiye wannan shiriritan muyi abu mai muhimmanci, kosu sir Ahmad banje na gaida ba, so nake mu gama sannan, dan na dawo da ayyuka masu yawan gaske, amma inason na fara jin mike tafiya daga wajenku?”.
“Akwai nasarori masu yawa da zasu sakaka farin ciki kuwa, dama mun barsu ne harka dawo muyi maka surprise”. Murmushi Jay yayi mai sanyi da jin duk ɓacin ran daya toshe masa ƙofar zuciya yana faɗawa. Aliyu ya ajiye masa files ɗin hannunsa. Ɗauka Jay yayi ya fara dubawa, a take fuskarsa ta bayyanar da annuri, sai da ya gama dubasu duka sannan ya ɗago yana kallonsu, “Woow! Ina alfahari daku sosai da sosai wlhy, gaskiya kunmin babban albishir mai darajar gaske, yanzu kuna nufin waɗanan duk sunzo hannu? Kun gama mana da waɗan nan ayyukan?”. Jabeer yace, “Ƙwarai ma kuwa, dan wanda yasa aka kashe jami'inmun ma yanzu haka gobe za'a miƙasa kotu”.
“Masha ALLAH, gaskiya naji daɗi wlhy, kuma nayi farin ciki sosai, maganar yaran canfa?”. Jawaad ya faɗa yana miƙewa ya ɗakko wani file a drawer ɗin bayansa.
Yanzunkam hafiz ne ya bashi amsa, “Ai boss maganar ƙungiya ta wuce duk yanda mukai zatonta, lokaci kawai zamu samu ko zuwa anjima sai muje office ɗin nasu kaga komai da idanunka zaifi, ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.
“Hakan yayi Hafiz, mu barsa kawa
i zuwa gobe sai muje, kuma sannunku da ƙoƙari, Jabeer maganar matar nan fa, har yau baka kammala ba ne?”. Na kammala komai, sai dai abinda ba'a rasaba, shima akan binciken mitaje yi inda take ne, inason binciko ƴan uwanta ne kokuwa? Gashi yanzu ma na daina samun wayarta gaba ɗaya kuma”.
Saurin kallonsa Jay yayi “Bata aiki wayar kokuwa?”. “An kasheta dai kusan kwana uku kenan, nafi kawoma raina matsalar caji ne”. Numfashi Jawaad ya ɗan sauke da faɗin, “Okay to ALLAH ya dafa mana, yanzu dai bara na leƙa na gaida su sir Ahmad, idan na fito zan ɗan fita wani waje, dana dawo saimu zauna akan wasu cases ɗin da muke dasu a ƙasa tunda kun kammala waɗannan”.
Duk kai suka ɗaga masa, kafin duk su miƙe su fito, shi ya hau lifter yay sama su kuma kowa ya nufi office.
Sai da ya shiga suka gaggaisa da oganninsa, office ɗin sir Ahmad ne ya zama ƙarshe, bayan sun gaisa shima da tattauna abinda ya shafi aiki Sir Ahmad ke cewa, “Nasan kasan Qaseem ya dawo ai?”. Da mamaki Jay yace, “Qaseem kuma sir!? Wlhy ban sani ba. Yaushe ya dawo?”. “Ya dawo kwana uku kenan, sai dai kuma yanzu haka sun killacesa, duk da shi ya dage akan shifa lafiyarsa ƙalau, shima Alhaji Ali ya kirani akan maganar wai ya kamata muyi wani abu a sakar masa ɗa dan baida wata corona”. Jawaad ya gyara zama yana ɗan murmushi da mamaki, yace, “To ALLAH ya kiyaye, amma kunje ɗin ku?”. “To Jay mu zamu biye musu ne, wannan hurumine na hukumar lafiya ai, kuma sunce nan da sati biyu idan bata basuga komai ba zasu sakesa ai”. “To ALLAH ya kaimu lokacin”. “Amin” sir Ahmad ya faɗa sannan sukai sallama ya fito.
Bai koma office ba ya nufi inda Sadiq ke jiransa, buɗe masa mota yay ya shiga sannan suka fice.
★★★★
Cikin Barrack sukaje wajen baba ƙaura, baba ƙaura na zaune yanata fiƙar tsinkayen iccen ƙwari Jawaad ya shiga da sallama shi da sojan da yay masa rakkiya. Ɗagowa baba ƙaura yay yana amsa musu da musu sannu da zuwa, ya nunama Jawaad wajen zama shi kuma wancan sojan ya fice. Sai da suka gaisa da tambayar ya kwana biyu sannan baba ƙaura ya kalli Jay yay murmushi da ɗauke kai. “Malam Jawaad kenan, mi kuma ya faru?”. Jawaad yaɗan murmusa yana kallon ƙwarin da baba ƙauran ya feƙe ya zube gefe kusan ashirin, “Baba na zone akan wata magana daka faɗa ranar a dajin nan”. “Tofa wace magana ce?”. Hannu Jay ya saka aljihun wandonsa ya ciro wuri da gurun nan na hannu sai zobe ya ajiye gaban baba ƙaura”. Kallon kayan baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana murmushi, “Kun sami huɗu kenan?”. Kai Jay ya jinjina masa. Cigaba baba ƙaura yay da aikin gabansa kamar ba zaice komai ba, kusan mintuna biyu sannan ya sake duban Jawaad ɗin da maida dukkan hankalinsa ga resa, “Yanzu ina ɗayan yake?”. “Bamu ɗakkosa ba, yana acan gidan data zauna ɗin”. Baba ƙaura ya ɗauki zoben ya jujjuyashi sosai a hannunsa sannan ya ajiye, “Lallai kun samu damar amsar babban makaminsu, amma yaya akai kuka iya samun zoben nan? dan abune mai daraja ga mai shi”. Muryar Jay cike da ɗaci ya zayyane ma baba ƙaura komai da ya faru, harma da maganar fyaɗen da aketa bibiyar Bilkisu da shi da sai a randa ta cire zoben ta iya tunawa. Nannauyan numfashi baba ƙaura ya sauke, yace, “Ai dama na faɗa maka yarinyar akwai duhu dake biye da ita, wannan yana ɗaya daga ciki, amma akwai wanda ya fisa girma ma sai dai bansan minene ba, ku cigaba da gayama ALLAH shi mai komai da kowa ne, ba ita kaɗai ba abubuwa da yawa zasu fito dalilin wannan zoben, dan duk inda maishi yake hankalinsa baya a kwance yanzu, har dama duk wanda ke zagaye a ƙungiyar shaiɗancin, ka turata gidan ta ɗakko wancan ɗayan wurin, idan har ta tarar an hargitsa ɗakin data ajiye to lallai mai bibiyarta da wannan sheɗancin na fyaɗe yana cikin wannan gidan, kuma shaiɗaninsu sun tabbatar masa wurin data cira a farko yana a gidan, an basa damar ya nemosa gudun karku haɗasu kamar yanda muke buƙata, dan inda tace maka ta ajiyesa babu wani shaiɗani da ya isa ɗaukarsa saboda darajar Al-Qur'ani, shiyyasa shi akace ya ɗakko, inaji a raina kuma bazai gansaba insha ALLAHU, dan daya gansa komaima zasu iya aikatawa a kanku domin halakaku baki ɗaya
musamman ma ita, suma kansu basusan taka mai mai inda ya keba bayan sanin yana cikin ɗakin kawai”. Jay dake ta tauna lip ɗinsa na ƙasa sai jinjina kai kawai ya keyi, ya furzar da huci mai zafi a bakinsa yana sake jinjina kansa. Baba ƙaura yace, “Idan ta ɗakko ku yanka wannan gurun, ku zira zoben da wurin guda biyu cikin gurin, zoben ya zama shine a tsakkiyar wurin, sai ku ƙulle gurun ku ajiye. wannan ba tsafi bane, ba kuma wani shaiɗanci bane, zakuga abinda zai biyo baya insha ALLAHU, dan cikin sauƙi zakuyita gano abubuwa masu ban mamaki da al'ajabi insha ALLAH..............✍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/18, 10:26 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Mmariya:
Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO