Sashe 150
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bata iya cewa sauran ƴan uwanta komaiba ta nufi hanyar fita daga asibitin da hanzari, duk faman tambayarta lafiya? da sukeyi bata juyoba balle ta amsa musu harta fice. Da kanta taja motar tabar asibitin zuwa gida.
Akan hanyar momy na nufar gida ta fahimci garin babu lafiya, dan kuwa babu abinda take gamo da shi a tituna sai matsanancin holdup. Mafi yawancin inda traffic light suke an haɗa cinkoso a wajen sosai, ga jirage masu saukar angulu da keta yawo na kaikawo a sararin samaniya, wasu ma daf da mutane suke. Ratse ta ringayi ta cikin anguwanni tamkar yanda wasu motocin taga sunayi. Da ƙyar ta samu kanta a anguwarsu, tai fakin motar a ƙofar gida batare data kasheba saboda wani bahagon ruɗani da ta sake karo da shi kuma, ƙofar gate ɗinsu a buɗe take, ga jami'an tsaro sun zagaye gidan, cikin sake shiga ruɗani ta afka cikin gidan da sassarfa tamkar zaga kifa, ananma wasu jami'an tsaron ta sake cin karo dasu a cikin gidan, talatuwa na durƙushe gefe tana kuka ita da mai bayin fulawa.
“Kai lafiya?”. Mom ta faɗa hajijiya na neman ƙwasarta zuwa ƙasa. Wani cikin ƴan sandanne ya bata amsa da faɗin, “Hajjaju wannan gidan yana a hannun hukumane a yanzun, akwai bincike da za'azo ayi a cikinsa daga yanzu zuwa kowanne irin lokaci”. Cikin tsawa da hucin ɓacin rai, “Mom tace kuɗin ubanwa muka sata to? Muba ƴan siyasaba ba ma'aikatan gwamnati ba, amma za'a turo mana jami'an tsaron binciken almun dahana da dukiyar ƙasa?”.
“A'a hajiya, mu ba jami'an tsaron almun dahana bane ba, jami'an tsarone na farin kaya, da kuma amincewar Sir Qaseem Ali muke anan bisa Umarnin Sir Jawaad Abdul-aziz Yusuf”. “Qaseem! Da Jawaad kuma?”. “Hakane hajjaju” ya sake bata amsa kansa tsaye.
Wata ashariya da momy ta manta tama iyata ta kwaso ta dire bisa ƙasa tanayin wurgi da jikkar hannunta, ta shaƙo wuyan police ɗin tana huci, a take sauran suka zagayeta da bindiga. Murmushi Munkaila yayi yana ɗaga musu hannu alamar su barta, ya kalleta fuska babu wasa zaiyi magana ta tare numfashinsa. “Kai shashasha kasan mi kake faɗa kuwa? Ina Jawaad da Qaseem ɗin suke?”. Ɗan murmushi yay mata yana zame hannunta a wuyansa ya gyara rigarsa, “Sir Qaseem yanzu ya fita, Sir Jawaad kam yana filin daga”. Sake rikicewa kanta ya nemayi, batare data nutsu wajen fahimtar inda batunsa ya dosaba ta fice a gidan tamkar wata mahaukaciya.
Mota ta sake shiga tabar anguwar batare da tamasan kalar tunanin daya dace ace tayiba, kanta tsaye station ɗin su Jawaad ta nufa, sai dai ɗan karen holdup ɗin da take fuskanta a yanzun ya zarece na ɗazu data ris
ka tsakanin asibiti zuwa gida............
_______________
JAY-QAS
____________
Koda tawagar su Jawaad suka iso cikin gari cike suka iske station ɗinsu da manyansu da ƴan jaridu, abu na farko da suka farayi shine gabatar da sallolin azhar data riskesu a can da kuma la'asar da a yanzu aketa yinta.
Suna idar da sallar ƴan Jarida sukai musu caa aka, Jay dai bai saurari kowaba daga shi har Sir Ahmad da sauran manyansu.
Cikin son ƙure mutane irin na ƴan jarida ɗaya a cikinsu ya juya ga masu ɗaukar rahoton gidan tvn su yana magana a harzuƙe. “To jama'a kamar yanda kukai hasashe dai hakanne ta kasance, dan kuwa munga alamar rufa-rufar da muka saba gani ga jami'an tsaronmu idan laifi ya shafi manyan ƙasa yau gashi ta tabbata, to ta yayama zasu yarda su buɗe komai wa duniya bayan daga kawunansu sai surukansu da abokan iyayensu dama iyayen nasu. Haka za'a kifemu bayan kwana biyu muji shiru, bayan kuma tarin gawarwaki da mutanen dake a cikin mawuyacin hali da aka amso a hannun waɗan nan miyagu ƙuru-ƙuru duk mun gansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dama ba sabon abu bane irin wannan a ƙasarmu ta gado. idan kaga ana yayata mai laifi da cecekuce da tada jijiyar wuya ga jami'an tsaro to talakane ya aikatashi, amma idan su masu faɗa ajinne suka aikata sai a rufe komai ruf da sunan kare mutuncinsu ko maganar shiga kotunsu bakaji balle musan an yanke musu hukunci. To kenan mu talakawa bamu da suturar mutunci ne? shiyyasa ake ƙwance mana zannuwa a kasuwa?”.
A take wajen ya ɗauki ƙananun maganganun sauran ƴan jaridar, kowa na ƙoƙarin ɗaukar zancen ɗan jaridar nan ya zama sinadarin zazzage tasa maganar dake cin ransa.
Ganin abun na neman kawo hatsaniya har wasu cikin ƴan jaridar na fassara abun da rufa-rufa Jay ya dawo garesu rai a ɓace. Ɗan jaridar da yay maganar Jawaad ya kafe da kallo idanunsa na sake rinewa zuwa jajur, duk da azabar ciwo da kansa ke masa haka bai hana maida masa murtaniba cikin tsananin ɗacin murya, “Kar kai azarɓaɓi akan garin daka shigo cikinsa baƙo. Karka yankema littafi hukunci abisa bangonsa, duk sharhin da zakayi batare daka buɗe rubutun cikinsaba kuskurene kawai da son zuciya zai biyo baya. Alokacin da jami'in tsaro yake filin daga shi kaɗai yasan wane irin kwazazzabo da ƙalubalene rayuwarsa ke fuskanta, da ace yanda ku ƴan media kuka iya yayata al'amari haka kuke bama jami'an tsaro gudunmawa wajen kare fituntunun da ƙasa ke a ciki da kowama ya zauna lafiya a duniya. Idan ƙoƙarinmu na aiki da jajircewa wajen tsayawa mu tantance ke hantarar ra'ayinka akanmu, to kasani sauyi ba namu bane, kai da irinkane zaku sauya. Duk lokacin da mukejin matsayinmu ya girmama a duniya wajen jama'ar cikinta, tomu samu gazawa akan ƙoƙarinmu ta ɓangaren aikinmu ko kasantuwar ɗaukakar tamu. Daga hakanne zamuga muɗin ba komai bane wajen waɗan nan al'ummar dake ɗaga darajojinmu da girmanmu a bakunansu da muryoyinsu. Daka zama mai ƙoƙarin ruruta wutar da bakasan tushentaba, mizai hana ka ajiye aikinka ka koma gidanka ka ɗaura zani kawai, koba komai ƴaƴanka zasu samu magirkan abinci biyu, shashasha kawai”.
Tsitt wajen. yayi tamkar ruwa yaci kowa, sai su Sir Ahmad kawai dake murmushi da bin Jay ɗin da kallo tamkar yanda suma ƴan jaridar da sauran jami'an suka rakashi da idanu harya shige.
Jabeer ne ya matsa garesu cikin ɓacin rai shima, ya sake kallon ɗan jaridar nan da maganar Jawaad ta sakashi duƙar dakai dan yaji kunya sosai da ganin kuskurensa akan kalamansa. “Aikin jarida ba neman kuɗi bane ko shiga rigar siyasa, aikine mai daraja abin girmamawa ga maiyinsa, ita daraja da gaskiya ake samota bada son a sani ba, kai da kayi waɗan nan kalaman kayisune bisa raɗin kanka kawai ko an sakaka badan aikin jarida ya baka damar yin hakanba, kai tsaye kake anan domin neman abinci wa iyalanka dake gida cikin kwanciyar hankali, shiko wannan da kakema gugar zanar cewar akwai kawunsa da surukinsa shiyasa ake rufa-rufa, tare da nasa iyalan ya shiga cikin jejin da baida tabbacin fitowa a raye. Atunaninka akwai sadaukarwar data kai wannan girma kuwa? Ku daina zubarma aikin jarida mutunci
dan aikine na masu mutunci a kowanne lungu da saƙo na duniya, sai dai kaicon irinku masu girmama fitina da riritata tai faɗin da zata buwayi wanda kuke tunanin kun tozartar harta dawo ga iyalanku kuma cikin aikin jarida, baka dace da wannan aikinba sam, ya kamata ka ajiyesa ka koma ka saka rigar siyasa, inaga kalamanka da nuna iyawarka zatafi dacewa dacan ɗin”. Yay maganar da watsa musu harara shima yabar wajen.
Sosai jikin duk ƴan jaridar ya sake yin sanyi, masu ƙara gishiri da magi akan batun sai suka koma gyara harsunansu suna miƙa rahoto mai inganci dan an tunatar dasu abinda suka manta domin kawai neman ɗaukaka da birgewa.
Duk jarumtar da Qaseem ke arowa yana ƙara ƙarfafa kansa da ita sai hakan ya nema gagara, kalaman Jawaad dana ɗan jaridar nan sun bala'in taɓa ruhinsa da zuciya, yabi bayan Jay hawaye na zurara saman fuskarsa batare da yayi tunanin gogewaba. A jikin ƙarfen lifter Qaseem ya iske Jawaad ya kife kansa dake tsananin sara masa, bai iya cewa dashi komaiba ya wuce zuwa office.
Ƙamshin turaren Qaseem ɗinne ya fargar da Jay zuwansa, ya ɗago a hankali yabi bayan Qaseem dake kan lifter ɗin da kallo harya gama hayewa, harya maida kansa zai sake duƙarwa sai kuma ya zabura cikin faɗuwar gaba, haka kawai zuciyarsa ta ɗarsa masa wani abu dangane da Qaseem, yariga yasan yanda yake da zafin zuciya. Cikin zafin nama ya haye lift... ɗin shima, ganima yake bata sauri gaba ɗaya, sai faman kallon agogo yake dukda kuwa a mintuna biyu kacal take kaisu.
Da gudu ya ƙarasa office ɗin Qaseem ɗin, yana taɓa ƙofar ya jita a rufe, hasashensa ya zama gaskiya kenan?, Qaseem ya shiga office domin aikata duk abinda ransa ya raya masa, baya yay ya daki ƙofar office ɗin da masifar ƙarfi, sai dai bata buɗeba amma ta girgiza. “Innalillahi...” ya faɗa yana bubbuga ƙofar da ƙwala kiran sunan Qaseem, sai dai ko sau ɗaya Qaseem ɗin bai amsa masaba, rikicewa Jawaad ya sakeyi, yabar wajen da gudu zuwa office ɗinsa dan ya tuna akwai key ɗin office ɗin Qaseem ɗin a wajensa wanda Sir Ahmad ya bashi ranar domin ɗaukar wasu files a ciki, da ƙyar ya iya gano keys ɗin saboda a rikice yake, yana ɗauka ya dawo da gudu.