← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 168

Sashe 159

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

...............Cike da mamaki matuƙa Aamilah ke kallon Shahudah dake zaune gaban mirror'n ɗakin Mama Atika tana tsara kwalliya, taci jan wando da farar top ƙal mai ƙyau da akaima hoton zuciya a gaba, gefe kuma madaidaiciyar jikka ce mai azabar ƙyau da aka ƙawata da zanen furrani na zuciya.....
       “Sister! Wai mi kikeyi hakane?”.
Ɗago manyan idanunta tai da sukasha kwalli ta kalli Aamilah, sake maida fuskarta tai ga mirror tana dai-daita janbakinta da yay mata ɗas a baki. “Harma tambayata kike Aamilah? Kin manta yau Valentine day?. A duk irin wannan ranar kema shaidace ai ina shiryama BB wani abu, sannan muɗan fita yawo koda dakene idan shi yace bai zuwa. Tunda matsalolin nan suka fara kema kinsan hakan bata kasanceba, to amma yanda aka maida auren nan namu ai wannan ranar ni tazomin a dai-dai, koba komai zan sake tabbatar masa yana nan daram a raina, a shirye nake kuma nai waje da waccan jakar baƙauya daga garesa da baƙin asirinta”. Cike da takaici ƙarara a saman fuskar Aamilah ta girgiza kai ƙwalla na cika mata idanu, “Sister yanzu nan duk tashin hankalin da muke a ciki keta soyayya ma kikeyi? Wlhy bantaɓa sanin akwai kunyaba a duniya irin jiya, hatta da ƴan gidannan kunyar haɗa ido nake da wasu dalilin halin da su Dad suka jefa kansu da mu, amma ke tun a daren jiya nagama kin ware kamar komai bai faru ba, ga Mom can kwance yanzu haka zazzaɓi ne ma a jikinta, wlhy badan su Uncle Sulaiman sun matsa fitar nanba nasan babu inda zataje. Duk shirmen Salman jikinsa a sanyaye yake tun jiya ya kasa fita ko ina yana tare da Mom, amma ke........”
         Shahudah da kema Aamilah wani banzan kallo tunda ta fara maganar taja gajeren tsaki tana ɗaukar sosan hoda da ƙara gyara fuskarta. “Aamilah kenan, harma kece kike da bakin faɗamin ban damu ba? A kaf ɗinku nafi kowa shan kunya a al'amarinnan, dannice kullum mai posting pictures ɗin Dad a kowanne shafina, kinsan kuma yanda nake da ɗunbin fans. sannan a dukanin shafukansa hotunana yafi na kowa yawa a cikinku, wlhy tsabar baƙinciki gaba ɗaya shafukana na rufesu, ke a jiya saida na karya duka layikan na fasa wayar sannan na samu nutsuwa. Bayan wannan mikikeso nayi? Na rasa Dad, nakuma rasa BB a karo na biyu? Impossible dear, dolene na tsira da ɗaya, domin ina ƙaunar mijina. Nasan duk bayanin dazan miki ba fahinta zakiyiba tunda ba auren kikayi ba, dan haka karki bari a jimu a gidan mutane”.
     Baki a matuƙar hangame Aamilah da Mama Atika dake a kwance tana duk saurarensu suke kallon Shahudah data jefa Cingam a baki tana ƙara gyara zaman gashin dokin dake a kanta da siririn mayafin data yafa. Juyawa tai tana kallonsu kanta tsaye, “Kumuje. dan nifa namafi son mu fara isa dan naga Maman BB sosai naga kuma kalar tarbar da zatamin. Sannan naɗan faracin uban yarinyarcan kafin zuwa dare na tare”.
    Uffan babu wanda yace mata a cikinsu, Aamilah ta taimakama mama Atika ta tashi zaune dan dama tuni ta shirya, badan tasoba zata bisu, sai dai kawai waɗanda suka bada shawarar zuwa gidan Alhaji babba a yau sunfi su da basa son zuwa rinjaye, batason kuma tace bazataje ba a fassara al'amarin da wani abu daban, ko aga kamar tana baƙin ciki da dawowar Bilkisu ne.
      Sun iske mafi yawan jama'ar gidan suma duk sun fito harabar gidan, fitowarsu ta saka kowa ya zubama Shahudah idanu, dan taci wani uban dogon takalmine bayan ɗamewa datai cikin wando da riga. Uncle Sulaiman ya kalleta cikin ɓacin rai zaiyi magana Uncle Sadiq yay saurin riƙe masa hannu yana girgiza masa kai alamar karya ce mata komai, dan yasan yin maganar kan iya janyo wata fitina daban musamman ga mama Atika da tun jiya taketa datsama mutane magana a gidan tamkar ba uwace a garesu ba.
     Haɗiye maganarsa Uncle Sulaiman yayi, badan yaso hakanba. A sauranma babu wanda yay yunƙurin cewa komai, sai dai sunata kallon Shahudah data toshe da baƙin eyeglasess ga cingam a baki tanata tauna hankalinta a kwance.

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

______________________
  Gidan Alhaji Babba
_________________________

               Kasancewar mai martaba ya sanar da wuri zasuzo saboda yanada zaman meeting da su manyan jihar zasuyi game da abinda ya faru akan su Dad, tun daga sallar asuba bamu koma barci ba, aunty Batool da Boss suka fita suka haɗo kayayyakin da za'a buƙata na haɗa abinci, kasancewar munada yawa dandanan muka shiga hada-hadar haɗa breakfast. Koma nace dai sunayi, dan nikam bama wani aikin kirki nakeba dan sam banajin daɗin jikina. Wasu na gyaran gida wasu na haɗa abinci haka akai aikin, zuwa takwas na safe komai yayi tsaf kowa nata ƙoƙarin yin wanka. Da yake boss ya ɗakko mana kaya ni da shi tun fitar da sukai da aunty Batool sai banji damuwa da tunanin mizan sakaba, nai shirina tsaf cikin doguwar rigar lass ɗin daya ɗakko mini, sai dai bayan fauda babu abinda na ƙara, turarema kaɗan na saka na yafa mayafi na fito falo inda nake ɗanjin maganganun su Anum.
       Zamana baifi da mintuna uku ba mukaji ƙarar buɗe gate, miƙewa duk mukayi, Boss da Anuwar ma suka fito tare da Alhaji babba da suka sakko a tsakkiya, yasha gayu cikin farar shadda ƙal harda babbar riga, fuskarsa fayau alamar gyaran fuska yasha a ciki, sai baza ƙamshi suke su duka ukun. Ido muka haɗa da boss mukaima juna murmushi.
      Sune suka fara fita, mu kuma muna biye da su. Lokacin har motocin  guda uku zuƙa-zuƙa sun gama shigowa, sauran kuma duk sun tsaya a waje alamar bazasu samu waje ba dan habar gidan batacin mota fiye da bakwai. Akwai kuma ta Batool, boss sai na Alhaji babba guda biyu.
      Abu-Siddiq ne ya fara fitowa, sai Abbu. Da gudu Anum ta nufi Abbu ta maƙalƙalesa, shima ya tarba ɗiyarsa cike da ɗoki da kewa duk da shekaranjiya suka rabu. Mota ta biyu, Gombiya munaya sai mai martaba Sarki Sameer Saifudden cike da izzarnan tasa da kwarjinin girma da mulki, a take dogarai suka fara jera masa kirari tare da lulluɓe gaban motar har saida ya fito. (ALLAH ya taimaki ɗan autan jimina gagara ɗaukar shaho. Ɗawisu sarkin ado, hadari sa gabanka inda kakeso, kaga dutsen cikin ruwa bakasan ana rana ba, kainuwa dashen ALLAH. Ɗan sarki, jikan sarki, baban sarki kuma insha ALLAHU). Duk da sarauta da mulki na wannan sarki yana girmama duk abinda ya kasance a gabansa, ma'ana wanda yasan ya girmesa a shekaru, dan haka koda Alhaji babba da su jay suka ƙarasa gabansa ƙasa ya rissinar da kai alamar girmama ga Alhaji babba. Dan ya tabbata a haife zai haifesa.
     Sosai Alhaji babba yaji daɗin wannan girmamawa har fuskarsa ta bayyana.
       Ba'a ɓata lokaci ba akai musu jagora zuwa babban falon baƙi na Alhaji babba da yasha gyara da ƙamshi,  an kuma shirya musu abincin karin kumallo.
      Gambiya na riƙe dani sai faman taɓa jikina take da tambayata mike damuna. Nidai kaina a ƙasa nake faɗa mata babu komai, kawai gajiyace, da yake ita bata bi su takawaba muna tare da itane sai Ummah ƙarama ke faɗa mata ai ta samu jikane. A take Ummu ta rikice da murna ta rungumeni a jikinta kai kace niɗin jininta ce da gaske. Hakan ya ƙara saka kimarta da mutuncinta gasu Umm-Anum dama duk wanda yake a wajen.

       Daga haka mukai zaman yin breakfast, inda Ummu ta saki jikinta sosai kodan dama can ta riga ta saba da Umm-Anum ne oho. Sai dai kowa yaci ya ƙoshi Alhmdllh sannan su Nabeelah suka gyara wajen, bandani da Umm-Anum ta hanani tashi, a cewarta na zauna na huta haka nan.

   ★★★★

          Acan falon baƙi kam Abbu kasa sakewa yay yaci abinci saboda nauyin Alhaji babba da yakeji, hakama takawa da ƙyar yasha haɗaɗɗen shayin da Umm-Anum taima dahu na musamman saboda tasan shi da Abbu suna matuƙar son shayin, dan idan takawa yaje can sosai yake shansa, sai farfesun kan rago da shima yana matuƙar sonsa.
     Alhaji babba babu ruwansa, mutum ne mai sakewa da jama'a dajan na ƙasa da shi a jiki, dan haka yayta jansu da hira hardai suka saki jiki da shi, musamman Abbu daya fahimci shine surukin nashi kodan nannoƙewar da yaketa famanyi.

   ______________
Chapter 159 · 0% Book details