← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 168

Sashe 161

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

            “A daren wata juma'a dake dai-dai da cikar Abdul-aziz shekara ɗaya da wata ɗaya akan kujerar mulki sai yay baƙi bayan sallar isha'i, tunda naga har ya yarda zaiga baƙin na tabbata masu muhimmanci ne, dan a ƙa'ida shugaban ƙasa baya irin wannan zaman musamman ma da daddare, kuma a cikin gida, gidanma a falonsa. Inason tashi na bisa naga wanene Jawaad dake fama da zazzaɓi ya hanani tashi dan yanata faman kuka, haka na haƙura nai amfani da telephone nai kiran su Wasila dake ɗakinsu, dan suna a tare damune kowa ya sani. Rahma ce ta ɗaga wayan, a cewarta Wasila tayi barci. Umarni na bata akan tasaka akaima baƙin Abdul-aziz abin sha, idan kuma suna buƙatar wani abu sai a haɗa da shi. Ta amsamin da to na katse kiran. Kusan mintuna arba'in da yin haka harma na manta ina jiran shigowarsa ne kawai sai ga Rahma ta shigomin a wani iri. Faɗa na fara mata, dan basa shigowa ɗakinsa inba da wani babban daliliba. Cikin rudin da take ciki tace, Kiyi haƙuri Yayah, wlhy wani abune ya sakani a ruɗani, zomuje ɗakinki kiji dan ALLAH kada Yah Abdul ya shigo. Ban musa mataba nabi bayanta muka fita, ina goye da Jawaad da yay barci a bayana”.
       (Yayah wai dan ALLAH mi su Alhaji Sadi keson Yah Abdull yayi ne yaƙi?). Ban ganemba Rahmah miya faru?. (Ruwan da kikace na saka a kaimusu saina iske ma'aikatan sunata faman aiki, kinsan kuma Yaya bason kowa yay masa aiki yake ba wani lokacin, shinefa na ɗauka da kaina nakai ruwan, to saina iske Yaya Nasir, Alhaji Ali da Alhaji Kokino tare da shi, sai dai kafin nai sallama naji wani furuci na Yaya Nasir daya saka bayan na gaishesu na ajiye ruwan na sake laɓewa, dan tundafa na shiga falon kan Yah Abdull a ƙasa alamun ransa a ɓace yake. Kinsan minaji kuwa?) kaina na jinjina mata a lokacin. (Ta cigaba da faɗin Yaya Nasir naji yana faɗin, “Amma dai Abdul-aziz kasan baka isa sanin sirrinmu ba sannan ka bijire mana, bafa wai dan bama sonka bane muke jawoka jikinmu, duk yanda kake tunanin mulkin ƙasarnan yafi ƙarfinka saika ɗaura ɗammarar da muke nuna maka, dan mulkin ƙasarnar baya buƙatar GASKIYARKA ko ƘWAZONKA balle son TALAKAWANKA”.  Murmushi Yaya Abdull yayi yana girgiza kansa, cike da ladabi yace, “Yaya dan ALLAH mu ajiye maganarnan, indai nine kusa a ranku abinda naji na gani a can wajen na barsa wlhy, kuma har abada bazan taɓa furtashi ga waniba koda kuwa ace Bilkisu ce ko Mama ko Jawaad. Amma hakan bawai yana nufin zan barku kucigaba da zama akan wannan hakalarba, kuji tsoron ALLAH, karku.........” da sauri Yaya Nasir ya ɗaga masa hannu, “Bama buƙatar ji”. Murmushi Yaya Abdull yay kawai yaɗan girgiza kansa, “Shikenan Yaya na bari, ALLAH ya ganar daku gaskiya idan kunada rabonta. Sai dai gaskiya koda zan haɗe wannan maganar a cikina bazan iya barin Sadi ya cigaba da sarrafa mugan ƙwayoyi ana cutar talakawa naba, dolene kodai ka rufe kamfaninka na sararafa magunguna, kokuma ni nasaka kwamitin bincike a kansa ƙarƙashin hukumar lafiya.......” a fusace Alhaji Ali (Dad) yace, “Mi kake nufi Abdul!? Kenan zaka iya mana SARAN ƁOYE (littafina na zafafa 2021🤗😋) kenan bayan kasan mu duka nan munada hannun jari a wannan kamfanin hatta da kai kanka ka sakama ɗanka hannun jari zaka aikata hakan kuma?”. “Babu wani maganar Saran Ɓoye Alhaji Ali, inda Saran Ɓoye zan muku da bazan fito na faɗa muku ba ai, sannan da kake maganar na sakama Jay hanun Jari a ciki ALLAH shine shaidata bansan abinda kukeyi a ɓoyeba kenan ai, nidai ABINDA KE CIKIN ZUCIYA ta (Littafin Rano a Zafafa 2021🤗😋) na fito na faɗa muku, dan ALLAH ya kukeson nayi? Ku kune garkuwata, a wannan tafiyar, amma kundawo kuna meman sakani cikin SIRAƊIN RAYUWA (Littafin Huguma a zafafa 2021🤗😋) kuma? Dama kun dafamin bayane domin kuyi amfani dani wajen cimma burinku ko mi? To wlhy! Wlhy! Wlhy!! Kunji sau uku, bazan taɓa cutar da talakawana danna faranta mukuba, bakuma zan taɓa nisanta kaina da UBANGIJINA saboda ku ba, sirrinku kuwa zan riƙe, domin wanda ya halicceku na kallonku, nayi imani da KIBIYAR AJALI.....(Littafin Miss Xoxo na zafafa 2021🤗😋)  sulke baya tareta saita gitta wataran, duk abinda yay farko zaiyi ƙarshe. Karku sake zuwamin gida akan wanan maganar daga yau na rufeta, kuma har gaban abada bazata sake tashiba insha ALLAH”. Kallon tsoro suke masa sosai, Alhaji Kokino zaiyi magana Alhaji Ali ya hanashi, shinefa na taho ganin Yaya zai fito). Ajiyar zuciya na sauke da cigaba da kallon Rahmah tamkar a jikinta zan samu amsoshina, fassara maganganunta nake amma babu wadda na iya samawa fassarar data dace, haka na haƙura na barta ta tafi ɗakinsu saboda farkawar da Jawaad yayi baban yaji kukansa ya shigo. Ban tambayesaba a ranar sai bayan sati kusan ɗaya, sai dai ko uffan baice daniba balle na samu amsa, haka na cigaba da masa naci daga ƙarshe yace karna sake damunsa akan abinda bai shafeniba. Ranar haka muka yini ran kowa a ɓace ni da shi”.
      Ta sake share hawayenta tana shaƙar numfashi da ƙyar, saida Gambiya ta bata ruwa tasha sannan ta cigaba.
        Tun daga wannan lokacin na fahinci abubuwa sun ɗauki zafi tsakanin Abdul-aziz da su Sadi, sai dai yaƙi faɗa min komai duk yanda naso ji, kamar yanda yay alƙawari ya saka kwamitin bincike akan kamfanin magunguna na Sadi, wanda abin bai nisaba aka ƙwace kamfanin batare da am bayyanama duniya mi aka gano a cikiba, sai dai abin mamaki ko sati biyu ba'ai da amsarba aka maida masa abinsa. daga wannan lokacin kuma yanayin yanda Abdul-aziz ke gudanar da mulki ya fara canja taku, baya iyayin komai sai abinda su Sadi sukace, ikon ALLAH dai talakawan ƙasa basu fahimci hakanba sai mu dake a kusa da shi sosai. Hankalina ya tashi sosai, dan ko shawara na bashi akan abu ko Baba da Mama maryam suka bashi sai yace ba hakaba, ga abinda Sadi da Ali sukace, ma'ana dai yafi yarda da nasu. Cikin wata guda duk ya susuce komansa ya koma ƙarƙashin ikonsu, mulkinma dai tamkar sune suke yinsa bashi ba, dan komai akan ikonsu yake gudana, sai sunce yayi yakeyi, wanda kuma sukace kar yayi komai muhimmancin abun bazai yisaba. Tun yana ciwo a tsaitsaye harta kaisa ga kwanciya, da ƙyar ya amince Doctor yazo ya dubashi a wata ranar laraba, a gwajin farko aka gano ciwon hawan jini tattare da shi, sannan zuciyarsa na barazanar kamuwa da ciwo kuma. Hankalina ya tashi, na dinga masa kuka da roƙon ya sanarmin abinda ke damunsa ko shawara na bashi, amma yaƙi. Bayan kwana biyu ya cigaba da ƴan harkokinsa yana nunamin ya warke, amma ni nasan akwai wata a ƙasa tunda nasha ritsashi yana hawaye, sannan idan ya zauna shi kaɗai zaka samesa yayi jigum yana tunani. Sai kuma rama da ya ketayi a tsaye wadda Baba da Mama maryam suka kasa haƙuri suma sai da suka tambayeni ko lafiya?. gudun karsu tashi hankalinsu nace babu komai kai kawone kawai irin na shugabanci da kuma ɗan zazzaɓi da yay na kwana biyu. Sun masa addu'a daga haka muka bar maganar.
         Bayan kamar sati shida da tashinsa daga wannan ciwo sai ya ƙara kwanciya, wannan itace kwanciyar data zama ajalinsa, a ranar bai fita office ba duk da kasancewar ranar aikice, yanama da meeting da gwamnoni, amma hakan ya gagara. Wajen yamma sai ga Sadi Kokino da Ali sunzo sun dubashi, ban kawo komai a rainaba na barsu daga su sai shi, ina ɗakina inama Jawaad shirin islamiyya sai ga Rahma da gudunta, sai dai tama kasa magana, hannuna kawai taja muka fito zuwa ɗakin da Abdul-aziz yake kwance. Sai dai muna kawo ƙofar ɗakin su Sadi na fitowa. Kallon Rahmah suka dingayi cikin wani yanayi daya sakani faɗin, “Lafiya kuwa? Miya faru?”. Cikin shashantar da zancen suka shiga gaisheni da tambayar jikinsa, tare da ɗorawa da faɗin ya kamata a sanar dan a fita dashi ƙasar U.S yaga likitan daya san aikinsa. Ban musa musu hakanba, dan nima ina buƙatar lafiyar mijina, na raɓasu na shige ɗakin sai na tadda Abdul-aziz a lulluɓe har fuskarsa, nai saurin matsawa na janye bargon. Ajiyar zuciya na sauke ganin idanunsa biyu, sai dai da alama hawaye yakeyi, amma jin motsina yay saurin sharewa ya maye fuskarsa da murmushi. Zama nai kusa dashi ina jera masa sannu, na shiga karanto addu'a kuma ina tofa masa kamar yanda ya buƙata, dan ya faɗamin jikinsa na masa zafi kamar ana hura wuta.
         Indai taƙaice muku a wanan dare  bamuyi barciba sam, washe gari muka wayi gari jikinsa ya rikice, da yayi tari sai jini, tun yanayi a ɓoye harna farga da hakan, sai dai ya hanani na faɗama kowa, a cewarsa zasu tafi asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zai samu sauƙi insha ALLAH. Badan hankalina ya kwantaba na yarda.
      Zuwa bayan sallar la'asar baba yaje gida ƴaɗan watsa ruwa dan tare damu ya yini sai ga Alhaji Ali (Dad) Alhaji Sadi Kokino, Alhaji Nasir (Uncle Nasir) da wasu mutane biyu daban saniba sunzo dubashi wai. Da yake muna falon ɗakin da yake kwance sai nace su shiga yana ciki, caraf Rahma ta riƙemin hannu tan girgizamin kai hawaye cike da idanunta amma ban fahimtaba, duk zatona damuwar ciwon nasane kawai, dan ita da Wasila tunda gari ya waye suke kuka, amma da yake Rahma tafi Wasila wayo a lokacin sai nata yafi yawa. Suna shigewa ta miƙe zaram ta kama hannuna tana nunamin ɗakin, mamaki abin ya bani na hau mata faɗa akan bata da bakine?. Har sannan bata tankaminba, kanta dai taketa faman jujjuyamin da fusgar hannuna muka zagaya ta Window.
        Ban taɓa ganin tashin hankali mai muni irin na wannan ranaba, dan kuwa zagaye muka hangi su Alhaji Kokino akan Abdul-aziz, sun lulluɓa masa wani jan ƙyalle suna wani kalar yare da su kaɗai suka san mi suke faɗa, duk yanda naso ɗaga ƙafa naje cikin ɗakin dagani har Rahma mun gagara hakan, a gaban idanunmu Nasir ya shiga zubama Abdul-aziz wani ruwa yana surkulle, sannan ya hau kansa yay....ya ya...yay fasiƙanci mafi muni da shi”. Umm-Anum ta ƙare maganar da fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin rai da zuciya, numfashin ta sai sama da ƙasa yake tamkar zata shiɗe.
      Tsitt falon yayi babu maiyin koda ƙwaƙwaran motsi, da alama dukansu sunyi suman zaune ne.
     Umm-Anum dake kuka tamkar ranta zai fita ta cigaba da faɗin, “Yana kuka da roƙonsa karya aikata masa wannan aiki maimuni, ga aman jini yanayi amma sam Nasir bai sauraresaba, sai da ya biya buƙatar zuciyarsa Ali ma yayi, Kokino ma Yayi. Duk muna kallonsu ni da Rahma, sai dai ko motsin kirki mun gazayi balle wani yunƙuri har suka fito suna kuka. Fitowarsu tayi dai-dai da dawowar baba tare da Mama Maryam. Sai ji kawai mukai suna faɗin Abdul-aziz ya rasu. Iya abinda naji kenan ban sake sanin mi nake cikiba sai a Saudia, shima ban tuna komaiba makamancin hakan sai shekaran jiya dana farka tamkar mai barci naga Anuwar da Abbunsu tare dani............✍
Chapter 161 · 0% Book details