← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 168

Sashe 71

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a harma dana nesa, alkairinsa dake jiƙe dani ALLAH kaɗai yasan iyakarsa, sai dai ba'a iya ganinsa da idon gani saina zuciya”. Wata irin mahaukaciyar dariya ɓaleru ya kece da ita wadda harta bama gimba mamaki, kafin yabi ba'asinta ɓaleru ya jefa masa handkherchief a fuska, daga haka bai sake banbance fari ko baƙiba sai a washe garin safiyar yau daya jisa a ɗaure, idanu a rufe, bakima a ɓame. A zuciyarsa ya ayyana, ‘GADAR ZARE akaimin da wanda na sani kenan?’. Murmushi yay na takaici wanda a zuciya ya kasance dan babu bakin yinsa. Da ƙarfin masifa aka fincike abinda aka sa masa a baki, azaba ta sakashi sakin wani irin gurnani sai dai jarumta ta hanashi nuna gazawa. Yace, “Suwanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku?”. Banza akai masa babu amsa, yasan akwai mutum tare dashi, dan yana jin hucin numfashi kasancewarsa mutum mai basira da wata ɓoyayyir baiwa. Yay ɗan yi murmushin ƙarfin hali yana mai motsa jikinsa kaɗan, ɗauri akai masa bana wasaba, hakan yasa daƙyar yake iya motsawa. Kusan minti biyir yana jiran tsammani kafin a saka masa abu akan kunne.
         Wata mahaukaciyar dariya aka sanya mai dogon zango daga cikin abinda basirarsa ta ankarar dashi wayace, daƙyar mai dariyar ya tsagaita daga can, kafin ya fara magana a kausashe. “Yaro ashe kaima tsagerane ban saniba, kai wanene daka isa tono abinda ke ɓoye? Ƙaramin naman daji abincin karnuka dakai har kakejin kakai zarra wajen yimana kutse a al'amuranmu? Banida lokacin doguwar magana dakai, yanzu za'a sakeka kai gudun mutuwarka kafin jininka ya zama halattacce ga bakandamiyarmu, wanda kakema aikinma bai isaba balle kai direbansa hhhhhhhhhhhhhh!!!!!”.
           Wata dariya gimba ya kwashe da ita shima, a kausashe yace, “Faɗan sunƙuru alamace tamai tsoro, idan kuncika maza kufito filin yaƙi mai nasara saiya ɗauki kambu, boss kainuwane dashen ALLAH, zakine mai yagalgala mazan da suke kiran kansu mazanma balle ku mata maza masu ɓuya a rumfar..........
         Kafin Gimba yakai ƙarshen zancensa an cire wayar daga kunnensa, taune leɓensa yay da ƙarfi. Kafin a maida masa baki a rufe, Bai sake jin motsin kowaba har yammaci, yana nan ɗaure babuci babu sha tun safiyar jiya rabonsa da abinci, garama ruwa yasha bayan fitowarsu massallacin juma'a, tun yana samun garkuwa daga yawu har shima yay tifƙewar da harshe bai iya juyashi ya zama abun mai gudana, ƙishirwa abune dake saurin illata mafi yawan halitta mai rai, balle irinshi mutum mai matuƙar son ruwa. Alamun duhun magriba da hasashe ne nashi yaji ya sake ɗaure garin, a wannan lokaci yaji an fara kuncesa, har aka gama tas bai motsaba bai kumace ƙalaba. Jansa aka shigayi keeeyyyy har zuwa waje, bashi da ƙarfin kare kansa dan haka ya salama bakinsa ɗauke da addu'a, tafiyar kusan mintuna uku kafin ai wurgi dashi.
      Numfarfashi ya shiga saukewa a gwame, yakai hannunsa da ƙyar ya janye ƙyallen da aka ɗaura masa a fuska, baya ganin komai da ƙyau saboda idanunsa sun kwana sun yini a rufe, ga duhun magriba, saidai ya fahimci dajine yake. Da sauri ya shiga laluban wayarsa dake aljihu wadda suka gaza gani bisa kariyar ALLAH, ya kasance mai saka waya silent saboda baison takurama Boss ɗinsa da shigowar kira, a hankali ya saba da hakan har takai bayama buɗeta koda basa tare, tun ɗazun yakejin sautin shigowar kira dama, daƙyar ya iya ganin Number boss saboda idanunsa basa gani sosai sun masa nauyi ainun. Kai tsaye WhatsApp ya shiga, yay azamar danna recording ya fara magana a galabaice.
         “Boss banjin zankai labari, dan basu kamani dansu barniba, akwai babbar ƙura a gabanka da bazan iya buɗe maka haske a kantaba yanzu saboda ƙarancin lokacin daya ragemin a duya, itace musabbabin shigowata rayuwarka tun fil'azal ka gafarceni da ɓoyewa, dama nabari ka fita daga wannan matsalar rikicin aurenne idan nadawo muyi magana, saidai ALLAH bai ƙaddara hakanba, amma nagodema ALLAH da wadda zata baka abinda yafi nawa tana raye, kai ƙoƙarin zuwa gidan Alh al..alhaji............ Ya kasa ƙarasawa saboda rawar da jikinsa ya fara na tunkarowar wata muguwar halitta  garesa maiban tsoro. Jifa yay da wayar bayan ya ɗaga ɗanyatsan

sa saƙon ya tafi

kasancewar baya rufe data shi dama can. Baya ya fara jan jikinsa yana karanto duk addu'ar data zo masa, yayinda shikuma wannan halitta ke biyosa danƙyas-danƙyas tana buɗe baki da lashewa alamar dai taga abinci. Babu zato gimba yaji yay baya, ashe wajen gaccine mai zurfin gaske dan akan tsauni suke. Wata irin wahalalliyar ƙara ya saki data bada amsa kuwwa a dajin yay ƙasa.......
       Wata irin mahaukaciyar dariya dahar saukarta ke kamar ƙasar dajin na girgiza ce ta fara ratsa tsaunika, anyita da tsayi kusan na mintuna biyar kafin ta lafa wani irin yare ya biyo baya da muryoyin mutane masu yawa. Duk wanda zai iya nutsuwar saurarar yaren zai fahimci kalaman cikinsa shirkace kawai ake ambato. (Wa'iyazubillah 😭ya ALLAH kasa mufi ƙarfin zukatanmu, ya rabbi ka saka duniya a tafukan hannayenmu karka sata a zukatanmu, kaiconmu, kaicon burikanmu kaicon son duniyarmu).

_____________________________

            Ana sallar magriba su Momy suka koma gida akan su Uncle Nasir zasu zauna da Jawaad domin yasa ɗan-fir'auna ya saki hudah.
          Momy da Shahudah ciki suka shige sukabar Aamilah na waya a barandar shiga falonsu.
             Da mamaki Aamilah ke kallon akwatinan da aka jibge a harabar gidan gaban motar Qaseem, ƙiyyy!! Sautin jawo abu ya karate kunnuwanta, kallon wajen da ƙarar ke zuwa tayi, Qaseem ne jaye da jikkan gana must go irin ƙatuwarnan sabuwa dal, amma tsabar yanda yasa ƙarfi wajen janta har hannu ɗaya ya fincike yana lililo, duk dai ya ganta yiyai tamkar basan da zamantaba, baba maigadi dai tun ɗazun yana hangen Qaseem ɗin daga ɗakinsa, tsabar baison yafito ya gansa ya sakashi aikin tayashine ya sakashi maƙalewa cikin ɗakin yana leƙensa ta Window. Jikkar ya dangwarar ya sake juyawa zuwa sashensu, daga shi sai gajeren wamdo da baƙar singlet datai mugun fidda masa siffarsa ta ƙaƙƙarfan namijin dake cin ƙarfe. Saida taga ya shige kafin ta juya da gudu gulma na cinta har saura kaɗan ta faɗi, ALLAH dai ya ara mata damar dafe ƙarfen da aka ƙawata barandar ƙofar falon nasu dashi, ƙara kwasa tai a gujen ta shiga tana ƙwala kiran Momy dake sama abin duniya ya isheta ga Shahudah tsaye kanta tana ribzar kuka da mata fitsara. Sosai kiran da Aamilah ke mata ya firgitata, ta miƙe zumbur ta fito tanabi matakalar benan da gudu-gudu. “Haba auta wannan wane irin kirane haka kamar wata baƙauya, miya farune shin kikemin kiran mafarauta?”. Baki Aamilah ta cuno bayan ta murguɗama Momy kamar wata sa'arta, kafin cikin taɓara tace, “Kajimin Momyn nan, dama kika samu na taimakeki na kawo miki labarin da ɗuminsa, toga ɗankican yana haɗa kaya da alama barin gidan zaiyi”. Sosai gaban mom ya faɗi, batama tsaya saurararta wanne a cikiba ta fice daga falon da sauri, dafa mata baya Aamila tayi tare da Shahudah data fito idanu a kumbure.
        Qaseem dake ta faman lodama ƙatuwar motarsa kayan yayma momy dake masa magana kallo ɗaya ya ɗauke kai batare da yace da ita ko ci kanki ba. Muryarta har zuga take na alamun ɓacin rai tace, “Qaseem wai badakai nake maganaba? Shin mikukeson maidanine a gidannan kai da Shahudah? shin bazaka nutsu kai ka fahimci uzirinmuba, Na shiga uku ni Aysha, wane irin mugun asiri wannan yarinyar ta haɗaku da shine kaida yaronan Jawaad da kuke ɗaukar kowa ɗan iska akan lamarinta?”. Cikin zafin murya Qaseem yace, “Nifa kin bala'in cikani da surutu hajiya, Please ki barni nai aikin gabana Mtsooww!!”. Ya ƙare maganar dajan wani wawan tsaki yana ɗauke kansa ya cigaba da loda kayansa a motar. Mutuwar tsaye kawai Momy tai tana kallonsa, Aamilah ta kwashe da dariya tana kallonsu, “Faɗan Uwa da ɗa abin birgewa, kucigaba da gashi guys”. Baki Shahudah ta taɓe tana mai juya manyan idanunta alamar zubama Qaseem harara, tace, “Ɗan jaraba duk bakai kaja manaba, wani iyayi da ƙwala kai a farantinne ya kaika nacema banzar yarinyarnan ƙazamiya mara gata, idan da baka maƙale matanba ta gidan uwarwa aurena da naka zasu haɗu ballema har bb ya aikata haka, asararre kawai mai baƙar zuciyar tsiy.....”
     Jikake tasss!! Qaseem da babu wanda ya lura da isowarsa gaban Shahudah ya sauke mata wani wawan mari, ƙasa ta zub

e tana garsheƙ

ar kuka daja masa ALLAH ya isa, to daman zuciyar ƴan mazan a kusa take, neman wanda zai amayarwa yakeyi, gashi ya samu cikin sauƙi, dan haka ya shigar tamkar an aikosa. Duk ihun da Aamilah keyi da Momy bai sauraresuba, sai ma tsarabar mari Aamilah ta samu itama, Momy kuwa ya hankaɗeta. Qaseem yanada Masifaffiyar zuciya irin wadda idan ta yunƙuro ɗinan sam bayajin bari, dan tamjar zugasama yake, sannan shifa cinnakane baisan na gidaba. Wanna. mugun zuciyan da ALLAH ya basu shida Jawaad itace ta hanasu zama ƙarƙashin inuwa ɗaya, dan kowa yanaji da kalar tasa, kawai shi Qaseem yafi Jawaad saurin fushine, dan Jawaad na dannewa yay kawaici har saika kaisa ƙarshe, amma ga Qaseem sam ba haka bane, sha yanzu magani yanzu, ga kuma ɗanbanzan riƙo saikace dangin kutare🤦🏻.
      Iya gwargwadon iko babu algus Shahudah ta daku harma da Aamilah daya koma haɗawa daga ƙarshe, dama yanajin haushinsu akan abu biyu, dukan Bilkisu da jimata ciwo, saikuma gudunmawar da suka bada akan ai masa aure da Azeema. Daƙyar da suɗin goshi baba mai gadi da kuku suka amshi Shahudah da Aamilah a hannunsa, dan yay musu kaca-kaca abinka da farar fata, Shahudah harda fasa mata baki akai jini sai ɗiga yake. Yace, “ƙananun marasa kunya, daga yau idan harku kun cika tsagerune dan ALLAH kusake shiga cikin al'amurana”. Kuka kawai suke daga su har Momy, babu wanda ya iya tanka masa har kuku da baba mai gadi suka gama loda masa kayansa a motar, sashensu ya koma ya ɗakko sauran tarkacensa ya shige mota ya fice batare da ya sakebi takantaba.

             Kai tsaye gidansa ya zarce, dama harya ajiye mai gadi tun jiya, kodaga waje kasan gidan ya haɗu, ya mugun ƙawatuwa da shukoki masu ƙamshi da daɗi, ga ƙamshin sabon fentima na tashi. Dakansa yayta shiga da kayan, da yake ALLAH yayisa mutum mai hanzari da zafin nama sai gashi ya gama sakasu ciki tas.

★★★★★
Chapter 71 · 0% Book details